Editor

9513 Posts
Noman rani: Gwamna Sule ya ƙaddamar da shirin saida takin zamani

Noman rani: Gwamna Sule ya ƙaddamar da shirin saida takin zamani

Daga BASHIR ISAH A matsayin wani mataki na bunƙasa noman rani a 2022 a jaihar Nasarawa, Gwamnan Jihar, Engr. Abdullahi A. Sule, ya ƙaddamar da shirin sayar da takin zamani don tallafa wa manoman rani a jihar. Ƙaddamarwar ta shafi har da sauran kayayyakin aikin gona, inda gwamnan ya bayyana farashin takin kan N7000 ga kowane buhu. Sa'ilin da yake jawabi, A.A Sule ya yi kira ga manoman da za su ci gajiyar shirin da su yi amfani da wannan dama wajen ci gaba da wadata jihar da kewaye da abinci. Taron ƙaddamarwar ya gudana ne a harabar hedikwatar cibiyar…
Read More
Babban burina shine sama wa matasa aikan yi a ƙarƙashina – Zainab Ɗanƙasa

Babban burina shine sama wa matasa aikan yi a ƙarƙashina – Zainab Ɗanƙasa

“Jajircewa ce maganin kowanne irin ƙalubale a sana'a” Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano A wannan makon filin Mata A Yau na fannin Gimbiya ya samu zarafin tattaunawa da wata jajirtacciyar matashiya mai suna Zainab Sani Mikai'l wacce aka fi sani da Zainab Ɗanƙasa, wacce ita ce shugaba kuma jagorar kamfanin Ɗanƙasa Dishes da ke Jihar Kano. A zantawarmu da wannan matashiya ta bayyana ma na yadda ta tsunduma cikin harkokin kasuwanci bayan kammala digirinta na farko a kan (Library Science and Information Technology) a jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano. Zainab ta ce babban burinta a rayuwa shi ne…
Read More
Yadda mota ta yi ajalin ɗaliban firamare 17 a Legas

Yadda mota ta yi ajalin ɗaliban firamare 17 a Legas

Daga BASHIR ISAH A Talatar da ta gabata aka samu aukuwar wani mummunan haɗari wanda ya laƙume rayukan ɗaliban makarantar Omole Primary School da ke yankin Ojodu a jihar Legas, su 17 ciki har da yara uku 'yan gida ɗaya. Faruwar wannan ibtila'in ya tada hankalin mazauna yankin gaya, lamarin da ya fusata ɗaliban sakandaren da ke kusa inda suka fito suka tare hanya sannan suka fafari babbar motar da ta aikata wannan ɗanyen aikin har zuwa yankin Ogba tare da banka mata wuta sannan aka kama direban. An ga ɗaliban sakandaren cikin fushi sun mamaye duka hanyoyin da ke…
Read More
Yaƙin Duniya Na Ɗaya

Yaƙin Duniya Na Ɗaya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A tarihi, Yaƙin Duniya Na Ɗaya, wanda a turance ake kira da ‘World War I’ ko ‘First World War’, wani yaƙi ne wanda manyan ƙasashen duniya, musamman na nahiyar Turai (Europe) irin su Ingila (Britain), France, Germany, Russia, Austria-Hungary, Russia, Daular Ottoman ta Turkiya (Ottoman Empire), da kuma Amurka suka fafata, a tsakanin shekarun 1914 zuwa 1919. A bisa tarihi, ya tabbata cewa zuwa shekarar 1900 wato farkon ƙarni na 21, ƙasashen yammacin Turai irin su Ingila, France, Germany, Spain, Portugal, Netherlands, da kuma Italy sun kai ga cikakken ci gaban tattalin arziki (economic development) da…
Read More
‘Yan fashi sun babbake gomman matafiya a Sakkwato

‘Yan fashi sun babbake gomman matafiya a Sakkwato

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga jihar Sakkwato sun tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga da ake yi zargin 'yan fashin daji ne sun ƙona wasu matafiya a kan hanyarsu bayan da suka taso daga yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni. MANHAJA ta kalato cewa, mummunan al'amrin ya auku ne da misalin ƙarfe tara na safiyar jiya Talata a kusa da ƙauyen Gidan Bawa, wurin da aka ce 'yan fashin sun saba tare matafiya tare da ƙona abubuwan hawa. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa kimanin mutum 17 suka…
Read More
Babu tabbacin rigakafinmu ya yi tasiri kan nau’in Omicron – Moderna

Babu tabbacin rigakafinmu ya yi tasiri kan nau’in Omicron – Moderna

Kamfanin Moderna da ke jerin kamfanonin da ke aikin samar da rigakafin Korona ya ce, ba shi da tabbacin nau’in rigakafinsa ya iya tasiri kan sabon nau’in cutar na Omicron da ke ci gaba da zama barazana bayan yaɗuwarsa a ƙasashe da dama. Kamfanin Moderna na Amurka ya yi gargaɗin cewa sabon nau’in covid-19 na Omicron na da saurin yaɗuwa fiye da hasashe duk da cewa kawo yanzu babu rahoto kan wanda ya kashe. Stephane Bancel shugabar kamfanin na Moderna a wata zantawarta da 'Financial Times' ta ce, nan da makwanni biyu ake sa ran kammala tattara bayanai game da…
Read More
Bayan shekaru 40 da gano cutar ƙanjamau masana sun kasa samar da maganinta

Bayan shekaru 40 da gano cutar ƙanjamau masana sun kasa samar da maganinta

Daga WAKILINMU A ranar Labara da ta gabata duniya ta yi bikin ranar yaƙi da cutar ƙanjamau a wani yanayi cike da fatan lalubo maganin cutar bayan shafe shekaru 40 da gano ta amma ba tare da magani ko kuma rigakafinta ba, sai dai ɗan cigaban da aka samu na samar da ƙwayoyin rage tasirinta a jikin masu ɗauke da ita. Yunƙurin yaƙar cutar da Majalisar Ɗinkin Duniya ke yi ƙarƙashin shirin UNAIDS cike da fatar samar da maganin na ƙanjamau kafin shekarar 2030 ya ci karo da babban ƙalubale bayan bullar cutar Korona da ta kawo tangarɗa a yaƙi…
Read More
Zan koya wa sauran jam’iyyun darasi a 2023, cewar Fintiri

Zan koya wa sauran jam’iyyun darasi a 2023, cewar Fintiri

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Adama, Ahmad Fintiri ya ce zai koya wa sauran jam'iyyun siyasa darussa a zaɓen 2023 idan Allah ya kaimu. Fintiri ya bayyana haka ne a lokacin amincewarsa da ƙungiyar kansilolin jihar Adamawa a ɗakin liyafa na gidan gwamnati da ke Yola a ranar Laraba 1 ga watan Disamba.  A wajen gagarumin taron, an jiyo gwamnan jihar Adamawa yana cewa, "a tsayar da ɗan yankin shugabancin ƙasa a zauna lafiya, inda ya ce ya bayyana cewa ta kowane ɓangare jam'iyyar APC ta gaza cika wa 'yan ƙasa tarin alƙawuran da suka ɗauka musu.…
Read More
WASIƘU: Illar cusa ƙiyayya a tsakanin jama’a (II)

WASIƘU: Illar cusa ƙiyayya a tsakanin jama’a (II)

Yadda tsadar rayuwa ta jefa ’yan Nijeriya cikin ƙunci A wannan makon zan ci gaba da yin bayanin da na soma kan wannan maudu’i namu abin dubawa, kamar yadda yake a sama. Domin su kalaman cusa ƙiyayya suna da ɓangarori daban-daban, kuma kowa da yadda yake kallon nasa ɓangaren. Inda wani yana ganin shi ai ba yana yi ba ne don ya muzguna wa wani, don haka idan aka nemi a hana shi sai ya ga tamkar an tauye masa haƙƙi ne na faɗin albarkacin baki. Haka kuma wasu na ganin irin waɗannan kalamai da suke furtawa, kalamai ne da…
Read More
Ƙungiyar PHRC ta shirya wa jami’an tsoro na sa-kai bita

Ƙungiyar PHRC ta shirya wa jami’an tsoro na sa-kai bita

Daga MUHAMMADU MUJITABA Ƙungiyar wanzar da zaman lafiya, tsaro da kare haƙƙin ɗan adam (PHRC) ƙarƙashin shugabancin Idris Ɗahiru Ofisa ta shirya wa Jami’an tsaron sa kai bitar sanin makamar aiki kan yadda za a tsaftace aikin gudunmawarsu ta ba jama’a da ƙasa tsaron don zaman lafiya ƙasa kamar yadda ya kamata a yi aikin bada tsaron farin kaya na sa kai. Taron wanda aka gabatar a unguwar bamfai Kano a ranar Asabar ɗin da ta gabata ya sa mu halatar jami’an tsoro na ’yan sanda da lauyoyi da sauran masana domin ilimantar da jami’an tsaron sa kai kamar ’yan…
Read More