Editor

9513 Posts
Sabon kwamishinan ‘yan sandan Bauchi ya sha alwashin yin aiki bisa tsarin doka

Sabon kwamishinan ‘yan sandan Bauchi ya sha alwashin yin aiki bisa tsarin doka

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Sabon kwamishinan ‘yan sanda da aka tura jihar Bauchi, Umar Mamman Sanda, ya sha alwashin jajircewa wajen murƙushe duk watni ƙalubale da kan taso a jihar bisa manufofin Babban Sufeton ‘yan sanda na ƙasa, Alkali Baba Usman da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Sai dai, sabon kwamishinan ya bayyana cewar, za a samu biyan wannan buƙata ce kaɗai idan an ƙwamatsi haɗin kan sauran hukumomin tsaro da ke cikin jihar, don haka ya sha ɗamarar haɗin kai da su domin tabbatar da ingantuwar rayuwar ɗaukacin jama’ar jihar. Sabon kwamishinan ‘yan sandan yana yin jawabi ne…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: ’yan bindiga sun sake kai hari masallaci a Neja, sun halaka mutum 15

Da ɗumi-ɗumi: ’yan bindiga sun sake kai hari masallaci a Neja, sun halaka mutum 15

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Aƙalla masallata 15 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka samu rauni a harin da aka kai a masallaci da ke ƙauyen Ba'are a ƙaramar hukumar Mashegu na jihar Neja. Maharan sun kai harin ne yayin da mutanen ƙauyen ke sallar asubahi kamar. Wata majiya ta ce, an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kontagora domin yi musu magani. Kwamishinan ’yan sandan jihar Neja, Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da harin, ya ce, aƙalla mutane 9 aka kashe a harin. Ya jadada cewa, hukumomin tsaro za su cigaba da yin ayyukansu na…
Read More
Kamfanin Dangote ya ƙaddamar da horon ‘yan jarida 60 a Arewa maso Yamma

Kamfanin Dangote ya ƙaddamar da horon ‘yan jarida 60 a Arewa maso Yamma

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Larabar makon jiya Kamfanin Ɗangote ya ƙaddamar da wani shiri na horas da 'yan jarida 60 daga jihohin arewa maso yamma a jihar Kano. A cewar fannin hulɗar jama'a na kamfanin, horon wani ɓangare ne na tsarin ayyukan sauke nauyin al’umma da kamfanin ke yi. Horon, a cewar kamfanin, an yi shi ne da nufin ƙara ƙaimi kan fasahar kafafen yaɗa labarai, wanda aka gayyato 'yan jarida daga jihohin Sakkwato, Katsina, Kebbi, Kano, Kaduna, da kuma Jigawa. Horon na haɗin gwiwa ne da Kamfanin Folio Media and Creative Academy, inda kamfanin ya…
Read More
Yadda kwantena ta rikito kan uwa da yaranta 3 a Kwara

Yadda kwantena ta rikito kan uwa da yaranta 3 a Kwara

Daga BASHIR ISAH A ranar Talatar da ta gabata aka samu aukuwar wani mummunan haɗari a Ilorin, jihar Kwara inda sunduƙin ɗaukar kaya da aka fi sani da kwantena, ya rikito daga saman tirelar da ke ɗauke da shi ya faɗa kan wata mata da 'ya'yanta su uku sa'ilin da suke cikin mota. An yi zargin cewa haɗarin ya auku ne sakamakon ƙoƙarin tserewa da direban motar da ke ɗauke da sunduƙin ya yi bayan da jami'an yaƙi da fasa-ƙwauri suka tasa shi gaba. Binciken MANHAJA ya gano cewa wannan na zuwa ne kimanin wata guda da faruwar wata arangama…
Read More
Jami’an Kwastam sun kama tsabar kuɗi Naira miliyan 71.350 da wasu haramtattun kayayyaki a Katsina

Jami’an Kwastam sun kama tsabar kuɗi Naira miliyan 71.350 da wasu haramtattun kayayyaki a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar Kwastam reshen jihar Katsina ta kama maƙudan kuɗaɗe har Naira miliyan 71.350 da aka ɓoye cikin jakar 'Ghana Must Go'. Muƙaddashin shugaban hukumar a Katsina Ɗalha Wada Chedi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da hukumar ta kira a birnin Katsina. Wada Chedi ya ƙara da cewa an kama waɗannan tsabar kuɗaɗe ne a kan iyakar Jibiya da ke jihar Katsina. "Mun kama tsabar kuɗi har Naira miliyan 71.350 waɗanda aka ɓoye cikin jakar 'Ghana Must Go' a iyakar Jibiya cikin wata mota ƙirar Toyota, wadda wasu mutane uku ke tuƙawa,…
Read More
Sojoji sun ceto ‘yan sanda 20 daga hannun ISWAP

Sojoji sun ceto ‘yan sanda 20 daga hannun ISWAP

Daga BASHIR ISAH Biyo bayan martanin da sojojin Nijeriya suka mayar kan harin da mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka kai ofishin 'yan sanda na Buni Yadi a jihar Yobe a Juma'ar da ta gabata, hakan ya sanya jami'an tsaron suka samu nasarar ƙwato duka 'yan sanda su 20 da 'yan ta'addar suka yi garkuwa da su yayin harin nasu. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaro suka yi nasarar halaka mutum 91 tsakanin 'yan fashin daji da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankunan Kala Balge, Rann, Dikwa da kuma Biu a jihar Borno, da Gombi…
Read More
Aikin jarida da rubutun adabi na tafiya hannu da hannu – Hajaru Baba

Aikin jarida da rubutun adabi na tafiya hannu da hannu – Hajaru Baba

“Gudunmawar marubuta ga gyaran al'umma na da yawa” Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Marubuciya Malama Hajaru Abdullahi Baba fitacciyar ’yar jarida ce da ta ke aiki a tashar gidan rediyo ta Vision FM da ke garin Sakkwato Birnin Shaihu. Marubuciya ce da ta samu nasarar wallafa littafinta na farko mai suna 'Kishiyar Mafalki' kimanin shekaru 10 da suka gabata, amma halayyar wasu 'yan kasuwar littattafan Hausa da ta zarga da kasancewa ‘marasa tausayi’ ya sa ta tsorata da harkar buga littafi, inda ta koma tunanin sakin rubuce-rubucen ta na gaba a yanar gizo, wato 'online' kawai. A tattaunawar ta da Manhaja,…
Read More
Buhari ya yi alhinin harin Sakkwato

Buhari ya yi alhinin harin Sakkwato

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa game da mummunan harin baya-bayan nan da 'yan fashin faji suka kai kan wasu matafiya a Jihar Sakkwato. Cikin sanarwar da ta sami sa hannu Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a, Femi Adesina a ranar Laraba, Buhari ya ce, “Na yi matuƙar damuwa da yadda mutuwa ta cimma waɗannan 'yan ƙasa yayin da suke kan hanyarsu ta tafiya zuwa wani sashe na ƙasa. “Wannan ya nuna matsalar da wannan gwamnatin ke fuskanta wadda take buƙatar haɗin kan 'yan Nijeriya ne don magance…
Read More
Numfashin mutum (5)

Numfashin mutum (5)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa masu karatu Assalamɗalaikum. Barkanmu mu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka da ke kawo muku bayanai game da jikin ɗan Adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikin ku ke aiki. Zan ci gaba da bayani akan numfashin mutum cikin yardar Allah. A makonnin da suka shuɗe, na kawo bayanin yadda iskar oksijin ke shiga cikin jikin ɗan Adam. Sannan kuma a satin da ya wuce, na fara bada bayan yadda ake fitar da iskar kabon dai ogzayid daga jikin ɗan adam, ma'ana saga cikin huhu izuwa iskar…
Read More