Editor

9513 Posts
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero: Sarkin da aka jima ana tsumayi…

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero: Sarkin da aka jima ana tsumayi…

*Zai amshi sandar mulki gobe*Yadda aka shirya bikin ba shi sandar*Asali da tarihin bada sandar sarautar Daga BILKISU YUSUF ALI a Kano "SAI KA YI”Kalaman da suka yi fice a bakunan Kanawa kenan a lokacin da ya ke riƙe da sarautar hakimci. Fata nagari lamiri, ya tabbata ga Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, don a gobe Asabar, ranar 3 ga Yuli, 2021 ne Gwamnatin Jihar Kano ta ware da ƙawata ranar na yin mashahurin taron da aka jima ba a yi irinsa ba, don bayar da sanda, duba da tun gabanin taron Jihar Kano ta yi cikar…
Read More
Cutar korona: Shugaba Bio ya kafa dokar hana fita a Sierra Leone

Cutar korona: Shugaba Bio ya kafa dokar hana fita a Sierra Leone

Daga WAKILINMU A matsayin wani mataki na yaƙi da ɓullar cutar korona karo na uku a ƙasar Sierra Leone shugaban ƙasar, Julius Maada Bio, ya bayyana kafa dokar hana zirga-zirga daga ƙarfe 11 na dare zuwa 5 na asuba, wadda za ta soma aiki Litinin mai zuwa idan Allah Ya kai mu. Ɗaukar matakin ya haɗa har da rufe masallatai da mujami'u, sai gidajen abinci da aka buƙaci su riƙa tashi da ƙarfe 9 na dare, sannan taron bukukuwa kada a wuce mutum 50. Bio ya bayyana ɗaukar matakin ne a Alhamis da ta gabata, tare da cewa an yi…
Read More
Itace tun yana ɗanye ake tanƙwara shi

Itace tun yana ɗanye ake tanƙwara shi

Daga SADIYA GARBA YAKASAI Ya na da kyau iyaye mu san mene ne mahimmancin yara da tarbiyyarsu da Allah ya ba mu, ba don komai ba sai don sanin cewa shi ɗa amana ne a gurin iyaye. Ko a cikin fatawa ta addini, malamai sun faɗi cewa, ɗa amana ne ga mu kanmu iyaye mata, don mu san cewa, tarbiyya wata babbar amana ce a gurinmu, saboda mace ita ce ja gaban tafiyar da tarbiyyar ’ya fiye da shi kansa mahaifi. Dalili shi uba sabgoginsa kaɗan ne cikin gida, saboda fita nema ga iyali na sanya sa idonsa akan 'ya'ya…
Read More
Matsalolin aure a Arewa: Anya ba jaki aka ƙyale ake bugun taiki ba?

Matsalolin aure a Arewa: Anya ba jaki aka ƙyale ake bugun taiki ba?

Daga AMINA YUSUF ALI Assalamu alaikum. Sannunku da jimirin karatun Jaridar Manhaja. A wannan mako mun zo muku da bayani a kan yadda yawaitar samun matsalolin aure a Arewacin Najeriya wato Ƙasar Hausa. Wadda wasu suke ganin Ƙasar Hausa a matsayin shalkwatar mace-macen aurarraki a ƙasar nan. Duk da yawan wa'azi da malamai da iyaye suke yi ga mata a kan su bi mazajensu. Da kuma irin izaya da muzgunawa da mata zawarawa suke fuskanta. Wata macen ma tana biyayya ga mijinta har ma a kan abinda a saɓa wa shari'a. Mace Bahaushiya tun daga ranar da aka haife ta…
Read More
Sakamakon Jarrabawar JAMB da barazanar ilimi a Nijeriya

Sakamakon Jarrabawar JAMB da barazanar ilimi a Nijeriya

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Kwanan nan ne Hukumar Kula da Shirya Jarrabawar Shiga Manyan makarantu a Nijeriya (JAMB) ta saki sakamakon jarrabawar ɗalibai na zangon 2020/2021, sakamakon da ya ja hankali kuma ya ɗaga hankali a faɗin ƙasar, saboda yadda ɗalibai suka faɗi warwas a jarrabawar. Sakamakon jarrabawar ya nuna cewa, a cikin ɗalibai 6,944,368 da suka zauna jarrabawar, guda 973,384 ne kacal suka tsallake shingen shiga jami’a. Hakan ya na nuni da cewa, kashi 14 cikin 100 ne kacal suka haye maki 180 da hukumar ta gindaya a matsayin shingen da ɗalibi zai haye, kafin ya samu…
Read More
Ko Biyafara ta riga mu gidan gaskiya?

Ko Biyafara ta riga mu gidan gaskiya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Haƙiƙa gidan gaskiya shi ne kishiyar gida mai ƙyale-ƙyale na duniya da filo da katifa amma yayin da mai rai ya yi filo da ƙasa ya koma gidan gaskiya kenan. Kamar yadda masu rai kan shuɗe sanadiyyar mutuwa sai dai a haifi wasu, hakanan lamuran rayuwa su ke shuɗewa da ya sa ma a ke yi wa duniya kirari da “mai yayi” don nuna cewa komai ka gani a na yayinsa wata rana zai zama tsohon ya yi. Misalin fitina a nan Nijeriya, kun ga ai yaƙin basasa na Ojukwu ya zama tarihi haka nan Marwa…
Read More
Jikin ɗan’adam: Kyakkyawar siffa

Jikin ɗan’adam: Kyakkyawar siffa

Daga MUSTAFA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa masu karatu Assalamu alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke zaƙulo muku bayanai game da jikin  ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Rubutun yau zai mayar da hankali ne izuwa kyawun siffa da sura ta ɗan adam. Ka tava tambayar kanka/kanki ya akayi wannan sura mai cike da tsari da hikima ke tafiya a doron ƙasa? A cikin Al-ƙur'ani Mai Girma, Allah Maɗaukakin Sarki ana cewa: " Haƙiƙa mun halicci ɗan adam a sura mafi kyawun tsayuwa" wannan batu la…
Read More
Silar shiga ta cikin marubutan ‘Labarina’ – Saddiƙa Habib Abba

Silar shiga ta cikin marubutan ‘Labarina’ – Saddiƙa Habib Abba

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano Rubutu wani abu ne da masu yin sa su ke samun damar isar da sakon su ga Jama'a yadda za su yaɗa manufar su walau ta ɓangaren addini ko kuma ɓangaren al'ada, da ma fanoni daban daban na rayuwa. Saddiƙa Habib Abba tana cikin Marubutan wannan lokacin da su ke da burin faɗakar da jama'a ta ɓangaren zamantakewar rayuwar su ta yau da kullum, kuma tana ɗaya daga cikin marubutan da Allah ya yi wa baiwar yin rubutun ta kowanne ɓangare. Domin kuwa marubuciyar labarin Hikaya ce, kuma marubuciya ce a kan al'amuran yau da…
Read More
Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 73 a cikin makonni biyu – Hedikwatar Tsaro

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 73 a cikin makonni biyu – Hedikwatar Tsaro

Daga UMAR M. GOMBE Babban Ofishin Tsaro da ke Abuja ya ce an samu kashe mayaƙan Boko Haram guda 73 a tsakanin makonni biyu a yankin Arewa-maso-gabas. Daraktan yaɗa labarai na rundunar tsaro na ƙasa, Bernard Onyeuko, shi ne ya bayyana haka ran Alhamis, yana mai cewa rundunar shirin Operation Haɗin Kai ce ta samu wannan gagarumar nasarar. Jami'in ya ƙara da cewa sojojin sun ƙwato makamai masu tarin yawa daga sassa daban-daban a wajen 'yan ta'addan Ya ce a ranar 27 na Yunin da ya gabata, sojojin sun karɓi wasu 'yan Boko Haram su 55 da suka yi saranda…
Read More
Hukuma ta kama tabar wiwi na milyan 91 ɓoye cikin tifar yashi a Legas

Hukuma ta kama tabar wiwi na milyan 91 ɓoye cikin tifar yashi a Legas

Daga WAKILINMU Ofishin Hukumar Kwastam da ke Seme ya kama tabar wiwi har ƙullli 3,186 da aka ɓoye cikin yashi a cikin wata tifar ɗaukar ƙasa. Jami'an hukumar sun kama kayan ne a babbar hanyar Seme zuwa Badagry, wanda ƙyasce kuɗin wiwin ya kai Naira milyan 91,488,977. Jami'in hulɗa da jama'a na ofishin, Abdullahi Hussain, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Larabar da gabata, inda ya ce sun kama kayan ne da safiyar Talatar da ta gabata. Kazalika, Hussain ya bayyana cewa sun samu nasarar ganowa da kuma kama kayan ne sakamakon bayanan sirrin…
Read More