01
Jul
Daga WAKILINMU Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashin daji ne sun kashe ɗan majalisar dokoki na jihar Zamfara mai wakiltar mazaɓar Shinkafi, Hon.Muhmmad Ahmad. An kashe Ahmad ne ran Talata da daddare a kan hanyarsa ta zuwa Kano bayan ya halarci gangamin karɓar Gwamna Matawalle na jihar Zamfara zuwa APC sakamakon sauya sheƙa da ya yi ya bar PDP. Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a na majalisar, Malam Mustafa Jafaru-Kaura, ya shaida wa manema labarai cewa baya ga halaka ɗan majalisar da 'yan bindigar suka yi, sun kuma sace ɗansa da direbansa. Ya ce lamarin ya faru…
