13
Jun
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wata ma’aikaciyar jinya mai suna Lucy Likeh ta ɓace bayan zuwa tashar mota a babban birnin tarayya domin aika wa ƙawarta saƙo.’Yar shekaru 28 da haihuwa, an ce tana aiki da wata ƙungiya mai zaman kanta a MKK Plaza da ke Jabi, Abuja, an ce ta je wurin tashar na Zuba don aika wa ƙawarta saƙo zuwa Minna, Jihar Neja, ranar Juma’a.Bayan ta ziyarci tashar, ba a san inda ma’aikaciyar jinyar take ba, kuma wayarta a kashe.An ce tana sanye da baƙar wando da baƙar riga da hular feskaf lokacin da aka ganta na ƙarshe.Da yake…
