13
Jun
Daga AISHA ASAS Masu karatu barkanmu da sake saduwa a shafin kwalliya na jaridar al’umma, Manhaja, da fatan ba ku ƙosa da wannan darasi na atisaye ba. A yau da yardar mai dukka za mu taɓo wani ɓangare da kusan zan iya cewa ya fi adabbar mutane, amma rashin sani kan sa ayi masa wata fassarar da ta saɓa wa sananniyar ma’anar sa. Da yawa daga cikin wasu matsaloli da suka dangance ciwo da muke cewa matsala ce ta mutanen ɓoye, ko sammu da jifa, zuwa duk wata damuwa da ta shafi rikeɗewar tunani, takan samu ne ta sanadiyyar damuwa.…
