24
Jul
Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano ƙungiyar Kano Association Council of Traders and Entrepreneurs (KASCOTE) ta gudanar da taronta na uku a Kano, inda ta haɗa 'yan kasuwa da masu zuba jari daga sassa daban-daban na Nijeriya da ƙasashen waje domin bunƙasa harkokin kasuwanci da masana'antu. Shugaban KASCOTE, Alhaji Hassan Yaro, ya bayyana a wajen buɗe taron cewa manufar taron ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin 'yan kasuwa, da samar da damar zuba jari da bunƙasa masana'antu. Ya ce taron baje kolin kayayyaki ya samu haɗin gwiwa da Jamhuriyar Indonesia, ƙarƙashin jagorancin jakadan ƙasar a Nijeriya, tare da rakiyar shugabannin jami'o'i…
