ukarofi

12525 Posts
Iyalai na buƙatar adalci bayan zargin sojoji da kisan malamar makaranta a Gusau

Iyalai na buƙatar adalci bayan zargin sojoji da kisan malamar makaranta a Gusau

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wasu iyalai a Jihar Zamfara na roƙon hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta ƙasa da ƙungiyoyin lauyoyi da su shiga lamarin bayan wata malama mai shekara 28, Zainab Abdullahi, ta rasu sakamakon zargin sojoji sun kashe ta a kan hanyarta ta zuwa aiki a Gusau a ranar Talata da ta gabata. Zainab, wacce ke koyarwa a wata makarantar mata a babban birnin jihar, ta rasu ne bayan shaidu sun ce wata motar soja ta buge babur din da ta hau sannan suka tsere. An yi jana'izar ta a ranar da ta mutu bisa ga koyarwar…
Read More
An fara sayar da takin gwamnatin Gombe a Shongom kan N32,000

An fara sayar da takin gwamnatin Gombe a Shongom kan N32,000

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe An fara sayar da takin zamani na mai sauƙin farashi na gwamnatin Jihar Gombe a ƙaramar hukumar Shongom, inda ake sayar da kowanne buhu kan farashin Naira 32,000 domin tallafa wa manoma da kuma bunƙasa samar da abinci. Da yake ƙaddamar da shirin, shugaban ƙaramar hukumar Shongom, Modi D. Shelpidi, ya ce gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta samar da tallafin ne domin rage wa manoma raɗaɗin tsadar taki tare da ƙara yawan amfanin gona a wannan kakar noma. Ya buƙaci manoma su yi amfani da damar wajen sayen takin, yana mai jaddada cewa za…
Read More
Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da cibiyar sarrafa rogo da gari a Katsina

Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da cibiyar sarrafa rogo da gari a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da sabuwar cibiyar sarrafa rogo da gari a ƙaramar hukumar Batsari, tare da sanya mata sunan marigayi tsohon ministan noma da albarkatun ruwa, Dr. Abba Sayyadi Ruma, domin girmama gudummawar da ya bayar. Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa cibiyar wani muhimmin mataki ne na cika alƙawarin gwamnatinsa na bunƙasa noma, samar da ayyukan yi, rage talauci da ƙarfafa tattalin arzikin karkara. Ya ce gwamnati ta himmatu wajen mayar da noma kasuwanci mai riba ta hanyar sarrafawa, adanawa, tattarawa da samar da kasuwanni. Ya ce cibiyar za…
Read More
Daga yanzu malamai za su rinƙa koyar da darussan da suka karanta ne a Katsina – Kwamishinan Ilimi

Daga yanzu malamai za su rinƙa koyar da darussan da suka karanta ne a Katsina – Kwamishinan Ilimi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Kwamishinan ilimi a Jihar Katsina Alhaji Yusuf Suleiman Jibiya ya bayyana cewa daga yanzu darussan da malamai na makaratun firamare da sakandire za su koyar zai daidaita da irin karatun da su ka yi.Haka kuma gwamnatin Katsina za ta rinƙa tura su aikin malanta a mahaifar su. Kwamishinan wanda ke magana da manema labarai a ofishin sa ya sanar da cewa gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da biyan Naira dubu 30 a matsayin alawus ga malamin da ke koyar wa a karkara da kuma basu rancen buburan hawa mai amfani da hasken rana a matsayin…
Read More
Sharhin littafin ‘Sanin Asali Shine Farin Cikin Rayuwa Da Aminci’

Sharhin littafin ‘Sanin Asali Shine Farin Cikin Rayuwa Da Aminci’

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Sunan littafi: Sanin Asali Shine Farin Cikin Rayuwa Da Aminci Mawallafi: Sheikh Abdulƙadir Na'Annabi Mu'azu Shekarar bugawa: 2026 Yawan shafi: 80 Mai sharhi: Abba Abubakar Yakubu Wane ne Sheikh Na'Annabi Mu'azu? Sheikh Abdulƙadir Na'Annabi Mu'azu wani fitaccen malamin addinin Musulunci ne da ke zaune a Jos, Jihar Filato. Allah Ya yi wa wannan malami baiwar sanin ilimin luggar Larabci da Balagha. Sannan malamin gwani ne wajen rubuta waƙoƙin Larabci da na Hausa, masu ƙunshe da darussa iri-iri. Ya kuma rubuta wasan kwaikwayo na Larabci da suka shafi tarihin Musulunci, da wasu fitattun malaman Musulunci. Sanin Asali…
Read More
Burin kowanne marubuci ne ya rubuta labari, ya ga ya koma fim – Jibrin Kaila 

Burin kowanne marubuci ne ya rubuta labari, ya ga ya koma fim – Jibrin Kaila 

"Kiyaye ƙa'idojin rubutu shi ne ƙashin bayan kowanne rubutu" (Ci gaba daga mako mai zuwa) Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Sunan Jibrin Yusuf Kaila ba ɓoyayyen suna ba ne, musamman ga marubuta masu mu'amala da kafafen sada zumunta. Matashi ne mai tsananin shauƙin son karance-karance da rubuce-rubuce. Yana kuma yawan rubutu kan tambihi game da harkokin rubutu da ƙalubalen marubuta. Ya fito ne daga ƙaramar Hukumar Haɗejiya ta Jihar Jigawa. A wannan makon wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya tattauna da shi game da gudunmawar sa a harkar adabi da kuma shawarwarinsa ga matasan marubuta ýan'uwan sa. A yi karatu…
Read More
Matar Sarkin Kabi Muhammadu Mera ta rasu

Matar Sarkin Kabi Muhammadu Mera ta rasu

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Allah ya yi wa Hajiya Halima ɗaya daga cikin matan Marigayi Sarkin Kabi Muhammadu Mera rasuwa. Hajiya Halima ta rasu a garin Argungu safiyar Laraba ɗin nan bayan fama da rashin lafiya, an kuma gudanar da sallar jana'izar a fadar Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu inda aka sami halartar mataimakin gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafidan Kabi, kwamishinoni, shugabannin ƙananan hukumomin masarautar Argungu, waƙilin Sarkin Gwandu Sarakuna, ƴan kasuwa, ƴan siyasa da kuma jami'an gwamnati. Mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama'ila Muhammad Mera ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa wace ba za a…
Read More
‘Yan asalin Katsina uku sun sami muƙamin kwamishinan ‘yan sanda a Nijeriya

‘Yan asalin Katsina uku sun sami muƙamin kwamishinan ‘yan sanda a Nijeriya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Raɗɗa ya yaba da cancanta da ƙwarewa bayan wasu 'yan asalin Katsina sun samu muƙamin kwamishinan 'yan sanda. Ya gode wa sufeto janar na 'yan sanda, IGP Disu bisa amincewar da ya nuna ga jami'an Katsina, ya ce za su cigaba da bautawa Nijeriya cikin gaskiya da ƙwarewa. Sabbin jami'an da aka ɗaga zuwa wannan babban muƙami sun haɗa da CP Nuhu Na Aliya Darma daga ƙaramar hukumar Rimi, CP Ibrahim Usman Lukunche daga ƙaramar hukumar Katsina, da kuma CP Tijjani Murtala Mohammed daga ƙaramar hukumar Safana. CP Nuhu na Aliya Darma ya gina…
Read More
An kama wani mutum da ƙunshi 28 na tabar wiwi a Katsina

An kama wani mutum da ƙunshi 28 na tabar wiwi a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama ƙunshi 28 na tabar wiwi a hannun wani mutum da ake zargi dillalin miyagun ƙwayoyi ne. Kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce an kama wanda ake zargin ne, Ibrahim Usman mai shekara 37, a wani samame na sirri da aka gudanar a kan hanyar Mashi zuwa Birnin Kuka, da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar 20 ga Yuli. Ya ce binciken da jami’an suka yi ya gano ƙunshi 28 na busasshiyar ganyen da ake zargin tabar wiwi ce. A cewar rundunar, wanda ake zargin ya amsa…
Read More
Kwamishinan ilimin Katsina ya cigaba da ziyarar makarantun da jarrabawar NECO ke gudana

Kwamishinan ilimin Katsina ya cigaba da ziyarar makarantun da jarrabawar NECO ke gudana

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A ƙoƙarin sa na ganin ɗalibai da ke cigaba da zana jarrabawar NECO basu sami wata matsala ba, kwamishinan ilimi a Jihar Katsina Alhaji Yusuf Suleiman Jibiya ya kai ziyarar sa ido a wasu makaratun a cikin garin Katsina. Makaratun da ɗalibai ke zana jarabawar sun haɗa da Government Senior Secondary School Kofar Kaura (Tudun Matawalle) da Eldan Science and Arabic Academy, Government Day secondary School Kofar Yandaka da School for the Blind sai Sir Usman Nagogo college of Arabic and Islamic studies. Kwamishinan ya ce mahimmancin ziyarar shine ma'aikatar sa ta gano wuraren da…
Read More