22
Jul
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mai ba gwamnan Jihar Katsina shawara kan ayyukan ƙananan hukumomi, Hon. Lawal Rufa'i Safana, ya bayar da umarnin soke kwangilar aikin gina gidajen .alaman asibitocin mataki na farko (PHCs) da ake gudanarwa a ƙananan hukumomin Funtua da Sabuwa, dalilin rashin bada himma ga aikin kwangilar da nuna ko in kula ga aiki da ɗan kwangilar ke nunawa bayan ya karɓi kuɗin somin taɓi tun ƙarshen shekarar 2025. Haka kuma ya bai wa ɗan kwangilar da ke gudanar da irin wannan aiki a ƙaramar hukumar Dandume wa'adin sati biyu kacal da ya kammala aikin tare da…
