ukarofi

12525 Posts
Lokaci ya yi da za a tsabtace rundunar ’yan sandan Nijeriya gaba ɗaya

Lokaci ya yi da za a tsabtace rundunar ’yan sandan Nijeriya gaba ɗaya

A duk ƙasashen da suka ci gaba, babu wata hukuma da ta fi muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya, kare rayuka da dukiyoyi da kuma tabbatar da bin doka kamar rundunar 'yan sanda. Ita ce fuskar gwamnati da talaka ya fi haɗuwa da ita a rayuwarsa ta yau da kullum. Saboda haka, ingancin aikin rundunar 'yan sanda na da tasiri kai tsaye kan yadda jama'a ke kallon gwamnati da kuma tsarin adalci. A Nijeriya kuwa, duk da irin ƙoƙarin da gwamnati da shugabannin rundunar ke yi wajen sake fasalin aikin 'yan sanda, har yanzu akwai wasu ɓata-garin jami'ai da ke…
Read More
Shawara ga Alhaji Aliko Dangote

Shawara ga Alhaji Aliko Dangote

Ina amfani da wannan dama wajen isar da wata ƙaramar shawara ga mai girma shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote. Na ji cewa kamfanin ya fito da wata tsari da ke ƙarfafa jama'a su kai rahoton duk direban motar kamfanin da ya karya dokokin hanya, tare da alƙawarin ba da tukuicin har naira dubu d Dari biyar (N500,000) ga wanda ya bayar da sahihin bayani. Wannan tsari abin yabawa ne, domin zai taimaka wajen rage haɗurra da kuma tabbatar da cewa direbobin kamfanin suna bin ƙa'idojin tuƙi. Sai dai ina da wata ƙaramar shawara: ya kamata a yi taka-tsantsan…
Read More
Shehu Mujaddadi bai ƙwace ƙasar kowa ba

Shehu Mujaddadi bai ƙwace ƙasar kowa ba

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Wallahi akwai takaici da ban mamaki wani ɗan kwangilar AIFOB ko na makiya Arewa wanda ba shi ma da alaka ta kusa ko nesa da Hausawa; ya rubuta wai Shehu Mujaddadi ya ƙwace ƙasar Hausa ko ya yaƙi wani Sarki da sauran shirmen makirci da sai a soshiyal midiya dandalin bulus na Bello Badum a ke gani. In ka deɓe ƙasar Gobir inda shi ma Shehu ɗan yankin ne, ba wasu wajaje da ya taka da kafarsa. Allah cikin ikonsa da’awarsa ta kai nisan inda ƙafarsa ba ta taɓa takawa ba. Hatta Gobir ɗin ma Wallahi…
Read More
Nehemiah Danjuma: Kurman farko da ya zama lauya a Arewa

Nehemiah Danjuma: Kurman farko da ya zama lauya a Arewa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An rantsar da matashi, Nehemiah Danjuma a matsayin lauya a Nijeriya, inda ya kafa tarihi a matsayin mutum na farko mai matsalar ji, wato kurma, daga Arewacin ƙasar da aka rantsar domin fara aikin lauya. Matashi Danjuma, ɗan asalin Jihar Kaduna daga ƙaramar Hukumar Jaba, ya kammala karatun digirin farko na fannin Shari'a da sakamako na Second Class Upper a Jami'ar Ilorin. Daga bisani ya kammala shirin Bar Part II a harabar Abuja ta Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Nijeriya. Da yake sanar da wannan gagarumar nasara a shafinsa na ɗ, Danjuma ya rubuta cewa: "Kurma…
Read More
Me yake kawo rashin zuwan yara makaranta a Arewa?

Me yake kawo rashin zuwan yara makaranta a Arewa?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A cikin wannan mako mai ƙarewa na samu damar halartar wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin ilimi, domin tattauna yadda za a ƙarfafa gwiwar iyayen yara, da samar da sabbin dabaru kan yadda za a daina cire yara daga makaranta zuwa aikin gona, ko aikin haƙar ma'adinai da neman kuɗi. Hukumar Kula da Ilimin ƙananan Makarantu ta SUBEB a Jihar Filato tare da haɗin gwiwar UBEC da ke ƙarƙashin gwamnatin tarayya, da Kwamitin Kula da Harkokin Makarantu na SBMC ne suka gudanar da wannan taro, wanda ya tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi…
Read More
An tsinci jariri bayan wani otel a Kebbi

An tsinci jariri bayan wani otel a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Hukumar hisba ta jihar Kebbi ta sanar da tsintuwar wani jinjiri bayan wani otel a cikin garin Birnin Kebbi. Daraktann shari'a Malam Surajo Usman Kamba ya bayyana cewa bayan da hukumar hisbah ta sami rahoton wani jinjiri da a ke sa ran an jefar da shi ne a bayan Zinari Hotel da ke cikin garin Birnin Kebbi, ba ta yi ƙasa a gwiwa ta tura jami'an ta zuwa wajen. Bayan da suka isa wajen sun tarar da jinjirin cikin yanayi mai buƙatar kulawa, inda aka ceto shi tare da ɗaukar matakan da suka dace domin…
Read More
Bilkisu Yusuf: Matar da ta rusa katangar da ta hana mata jagorantar ɗakunan labarai

Bilkisu Yusuf: Matar da ta rusa katangar da ta hana mata jagorantar ɗakunan labarai

"Ta jagoranci ɗaruruwan matasa, musamman mata masu sha'awar aikin jarida." (Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS A tarihin Najeriya, akwai matan da ba a auna girmansu da muƙaman da suka riƙe ko lambobin yabo da suka samu. Ana ci gaba da tuna su ne saboda irin tasirin da suka bari a rayuwar jama'a da kuma sauye-sauyen da suka haifar. Bilkisu Yusuf na daga cikin irin waɗannan fitattun mutane. A wannan makon, shafin Gimbiya ya ci gaba da waiwayar rayuwa da gudunmawar wannan fitacciyar 'yar jarida wadda ta zama abin koyi ga tsararraki masu zuwa. Bilkisu Yusuf ba kawai…
Read More
NULGE da NUJ sun taya shugaban NLC a Katsina murnan samun muƙamin babban sakatare

NULGE da NUJ sun taya shugaban NLC a Katsina murnan samun muƙamin babban sakatare

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi da ta 'an jarida tare da wasu ƙungiyoyi a Katsina sun bi sahun masu taya shugaban ƙungiyar ma'aikatan jihar Kwamred Hussaini Hamisu 'Yanduna samun muƙamin babban sakatare a gwamnatin Katsina. Shugaban ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi reshen Katsina, Kwamred Nasiru Maiwada Maiadua ya bayyana cewa gwamnati ta yi la'akari da kyakkyawan shugabanci da jajircewa wajan kula da jin daɗin ya'yan ƙungiyar NLC a jihar. Ya bayyana cewa sadaukar da kai da jajircewa wajen cigaban ma'aikatan gwamnatin Katsina ya sanya gwamnatin Dikko Raɗɗa tayi la'akari da wannan gudummuwa da ya bada. Kwamred Nasiru…
Read More
NBTE ta yaba wa Gwamnatin Katsina kan fassara kayan koyon sana’o’i zuwa harshen Hausa

NBTE ta yaba wa Gwamnatin Katsina kan fassara kayan koyon sana’o’i zuwa harshen Hausa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban hukumar ilimin fasaha na ƙasa (NBTE) ya yaba wa gwamnatin Jihar Katsina bisa ƙoƙarin ta na fassara kayan koyon sana'o'i zuwa harshen Hausa. Babban sakataren hukumar ilimin fasaha ta ƙasa (NBTE), Farfesa Idris Muhammad Bugaje, ya bayyana ƙaddamar da littattafan koyar da sana'o'in fasaha da aka fassara zuwa harshen Hausa a Katsina Youth Craft Village a matsayin wani babban ci gaba da zai sa ilimin sana'o'i ya isa ga al'ummomin karkara cikin sauƙi. Haka kuma ya yaba wa gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, bisa zuba sama da Naira biliyan biyar wajen bunƙasa…
Read More
FIFA na duba yiwuwar faɗaɗa gasar Kofin Duniya zuwa ƙasashe 64 kafin gasar 2030

FIFA na duba yiwuwar faɗaɗa gasar Kofin Duniya zuwa ƙasashe 64 kafin gasar 2030

Shugaban Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya bayyana cewa hukumar za ta yi nazari kan yiwuwar ƙara yawan ƙasashen da za su halarci Gasar Kofin Duniya daga 48 zuwa 64 kafin gasar shekarar 2030. Wannan shiri ya biyo bayan nasarar da aka samu a sabon tsarin gasar ta 2026, inda aka ƙara yawan ƙasashen da ke halarta daga 32 zuwa 48, abin da ya bai wa ƙarin ƙasashe 16 damar shiga gasar. Da yake magana a wata hira, Infantino ya ce za a mika wannan shawara ga kwamitocin da abin ya shafa na FIFA domin su tattauna…
Read More