ukarofi

12525 Posts
Sojoji sun kashe babban mai yaɗa farfagandar ISWAP da tawagarsa a Borno

Sojoji sun kashe babban mai yaɗa farfagandar ISWAP da tawagarsa a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar Operation HAɗIN KAI (OPHK) ta sanar da kashe babban jami’in yaɗa farfaganda na ƙungiyar ISWAP, Abu Salim al-Barnawi, tare da wasu mambobin tawagarsa a wani samame da aka kai a Jihar Borno. A cikin wata sanarwa da Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar a Maiduguri, ya ce wannan nasara za ta raunana ƙarfin ISWAP wajen yaɗa farfaganda da kuma ɗaukar sabbin mabiya. Sanarwar ta bayyana cewa Abu Salim tsohon kwamandan ISWAP ne kafin daga bisani a mayar da shi shugaban sashen yaɗa labarai na ƙungiyar, inda yake jagorantar…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta biya kamfanonin lantarki bashin Naira biliyan 333

Gwamnatin Tarayya ta biya kamfanonin lantarki bashin Naira biliyan 333

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta biya kamfanonin samar da wutar lantarki guda takwas (GenCos) jimillar Naira biliyan 333 a matsayin kashin farko na shirin biyan tarin basussukan da ɓangaren wutar lantarki ke bi. An bayyana cewa kuɗin sun shafi tashoshin samar da wutar lantarki guda 17 da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar shiga shirin. Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Makamashi, Olu Verheijen, ce ta bayyana hakan ranar Talata yayin taron masu zuba jari da aka shirya domin ƙaddamar da kashi na biyu na takardun bashi na Shirin Gyaran Kuɗaɗen ɓangaren…
Read More
Sabbin ƙa’idojin CBN na iya tilasta bankunan Nijeriya tara ƙarin jarin tiriliyan N1.7 – Rahoto

Sabbin ƙa’idojin CBN na iya tilasta bankunan Nijeriya tara ƙarin jarin tiriliyan N1.7 – Rahoto

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD  Wani sabon rahoto da Renaissance Capital (RenCap), ɗaya daga cikin manyan kamfanonin zuba jari na duniya, ya fitar ya nuna cewa bankunan Nijeriya na iya fuskantar ƙalubalen tara ƙarin jarin sama da Naira tiriliyan 1.7 tare da sake fasalin tsarin kamfanoninsu, idan Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya aiwatar da sabbin ƙa'idojin da ya gabatar kan Kamfanonin Riƙon Hukumomin Kuɗi, wato Financial Holding Companies (HoldCos. Rahoton mai taken "Nigerian Banks: More Capital, Declining Returns", wanda aka wallafa a ranar 16 ga Yulin 2026, ya yi gargaɗin cewa sabbin ƙa'idojin na iya rage ribar masu hannun jari, taƙaita…
Read More
Amurka ta kashe Dala miliyan 1.2 wajen kare kayan tarihin Nijeriya

Amurka ta kashe Dala miliyan 1.2 wajen kare kayan tarihin Nijeriya

Daga MAHDI MUSA NUHAMMAD Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta kashe Dala miliyan 1.2 cikin shekaru biyar da suka gabata wajen tallafa wa ayyukan kare kayan tarihi da al'adun gargajiya a jihohi 21 na Nijeriya, tana mai cewa wannan ba tallafi kawai ba ne, illa wata dabarar zuba jari da ke amfanar ƙasashen biyu. Mataimakin Jakadan Amurka a Nijeriya, Keith Heffern, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin ƙaddamar da wani aikin kare kayan tarihi da Gidauniyar Wheyham ta gudanar a Abuja. A cewarsa, kuɗaɗen da aka kashe sun fito ne musamman daga Asusun Jakadun Amurka na Kare Kayan Tarihi,…
Read More
An rantsar da sabbin shugabannin ANCOPSS a Kano

An rantsar da sabbin shugabannin ANCOPSS a Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar Shugabannin Makarantun Sakandare ta Jihar Kano (ANCOPSS), tare da raba magungunan agajin gaggawa ga makarantun kwana 20 da ke faɗin jihar. Da yake jawabi a wajen taron, Sakataren Gudanarwa na Hukumar Kula da Makarantun Sakandare ta Jihar Kano, Alhaji Rabiu Saleh Gwarzo, ya buƙaci sabbin shugabannin da aka rantsar su mayar da hankali wajen inganta shugabancin makarantu tare da tabbatar da haɗin kai a tsakanin membobin ƙungiyar. Ya ce haɗin kai shi ne ginshiƙin nasara, yana mai bayyana cewa idan shugabannin makarantu suka kasance “tsintsiya maɗaurinki ɗaya”, hakan zai…
Read More
Inganta ilimi shi ne babban abin da na sanya a gaba, inji Hon. Balago

Inganta ilimi shi ne babban abin da na sanya a gaba, inji Hon. Balago

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Shugaban ƙaramar Hukumar Kiyawa da ke Jihar Jigawa, Hon. Abdulhamid Ibrahim Balago, ya ce inganta ilimi shi ne babban abin da gwamnatinsa ta bai wa fifiko, yana mai jaddada cewa ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban al'umma a kowane fanni. Balago ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a wajen bikin yaye dalibai karo na takwas da kuma rabon kyaututtuka da aka gudanar a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kiyawa a makon da ya gabata. Ya ce tun bayan hawansa mulki ya kafa kwamitin bunkasa ilimi karkashin jagorancin mataimakinsa, tare…
Read More
Trump ya jinjina wa Tinubu kan yaƙi da ta’addanci

Trump ya jinjina wa Tinubu kan yaƙi da ta’addanci

* Ya yi alƙawarin ƙarfafa haɗin gwiwa da Nijeriya Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan abin da ya bayyana a matsayin jajircewarsa wajen yaƙi da ta'addanci da magance matsalolin tsaro a Nijeriya, musamman hare-haren da ake kai wa al'ummomin Kiristoci. Yabon na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 6 ga Yulin 2026, wadda Trump ya aikewa Tinubu, kuma Fadar Shugaban ƙasa ta fitar da ita ga manema labarai ranar Laraba ta bakin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai…
Read More
Majalisar Dattawa ta yi barazanar ladabtar da NNPCL, CBN, JAMB, NECO da sauran hukumomi kan ƙin amsa gayyatarta

Majalisar Dattawa ta yi barazanar ladabtar da NNPCL, CBN, JAMB, NECO da sauran hukumomi kan ƙin amsa gayyatarta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi barazanar amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba ta wajen ɗaukar mataki a kan wasu Ma’aikatu, Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati (MDAs) da suka ƙi amsa gayyatar Kwamitinta kan Harkokin Kuɗi domin gudanar da binciken sa ido. Barazanar ta fito ne bayan shugaban kwamitin, Sanata Sani Musa (Niger ta Gabas), ya gabatar da batu a zaman majalisar na ranar Laraba. Sanata Musa ya ce kwamitin na gudanar da bincike lokaci-lokaci bisa tanadin sashe na 88 da 89 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya domin tantance yadda hukumomin gwamnati ke…
Read More
Wani magidanci ya roƙi kotu ta tilasta wa ’yarsa fitar da mijin aure

Wani magidanci ya roƙi kotu ta tilasta wa ’yarsa fitar da mijin aure

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani magidanci mai ’ya’ya 11, Lawal Hamisu, ya garzaya Kotun Shari’a ta II da ke zamanta a Magajin Gari, Jihar Kaduna, inda ya roƙi kotun da ta umarci ’yarsa mai suna Fatima Lawal ta gabatar da wanda zai aure ta, tare da taimaka wajen ɗaura musu aure. Ta bakin lauyansa, H.B. Debo, Lawal ya shaida wa kotun cewa Fatima mai shekara 27, wadda ta kammala karatun Babbar Difloma (HND), har yanzu ba ta gabatar da wani namiji da ya zo neman aurenta ba. Ya ce duk da cewa ’yarsa tana da samari, babu wanda…
Read More
Ba zan soki Tinubu a talabijin ba alhali Ina da damar ba shi shawara a sirrance – Fashola

Ba zan soki Tinubu a talabijin ba alhali Ina da damar ba shi shawara a sirrance – Fashola

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Gwamnan Jihar Legas, kuma tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje na Tarayya, Babatunde Raji Fashola, ya bayyana cewa ba ya da niyyar sukar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bainar jama'a, yana mai cewa ya fi son ci gaba da ba shugaban ƙasar shawarwari kai tsaye a sirrance. Fashola ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi da tashar yaɗa labarai ta TVC a ranar Laraba, inda ya amsa tambayoyi kan dalilin da ya sa ba kasafai yake yin tsokaci a fili game da yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da mulki ba. A cewarsa,…
Read More