ukarofi

12433 Posts
Tambuwal ya maka gwamnatin Sokoto kotu bisa ƙin bayyana rahoton kwamitin bincikensa

Tambuwal ya maka gwamnatin Sokoto kotu bisa ƙin bayyana rahoton kwamitin bincikensa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya shigar da ƙara kan Gwamnatin Jihar Sakkwato kan zargin ƙin miƙa masa rahoton Kwamitin Bincike na Shari’a da aka kafa domin binciken ayyukan gwamnatinsa. Tambuwal, wanda a yanzu yake wakiltar Mazaɓar Sakkwato ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya mulki jihar daga shekarar 2015 zuwa 2023. A cikin ƙarar mai lamba SS/133/2026, wadda aka shigar a gaban Mai Shari’a Mohammed Mohammed na Babbar Kotun Jihar Sakkwato, reshen mai lamba 6, tsohon gwamnan na neman kotu ta umarci gwamnatin jihar ta ba shi kwafin rahoton kwamitin. Tambuwal ya shigar da…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta biya bashin albashin watanni takwas da SSANU ke bi

Gwamnatin Tarayya ta biya bashin albashin watanni takwas da SSANU ke bi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta saki kuɗaɗen albashin watanni takwas da mambobin ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya (SSANU), domin daƙile barazanar shiga yajin aikin da ƙungiyar ke yi. Kwanan nan SSANU ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14, inda ta buƙaci a gaggauta biyan sauran bashin albashin da ya taso sakamakon aiwatar da yarjejeniyar FGN/SSANU ta shekarar 2026. ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan Gwamnatin Tarayya ba ta cika buƙatunta cikin wa’adin da ta bayar ba, za ta tilasta mata fara “cikakken yajin aiki mara iyaka” ba tare da ƙarin sanarwa ba. Da yake magana…
Read More
Ya kamata a samar da tsarin bai-ɗaya na cigaban Arewa – Gwamna Uba Sani ga manya yankin

Ya kamata a samar da tsarin bai-ɗaya na cigaban Arewa – Gwamna Uba Sani ga manya yankin

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi kira ga jiga-jigan siyasar Arewa da su fi mayar da hankali wajen samar da wani tsari na bai-ɗaya da zai magance matsalolin da yankin ke fuskanta, maimakon mayar da hankali kan neman karɓe iko a matakin tarayya. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da shugabannin Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello suka kai masa ziyarar ban-girma a ranar Laraba, a zauren Majalisar Zartarwa na Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna. Ya nuna godiyarsa ga gidauniyar bisa yadda take jan hankalin ’yan siyasar Arewa da masu riƙe da muƙaman gwamnati kan…
Read More
An kama direban da ya kashe ɗan achaɓa ya gudu a Kebbi

An kama direban da ya kashe ɗan achaɓa ya gudu a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Jami'an 'yan sanda sun sami nasarar kama wani direba da ba a bayyana sunan sa ba wanda ya buge wani mai babur a hanyar Birnin Kebbi zuwa Argungu da ke jihar Kebbi. Ganau Malam Abdullahi Muhammed Dagwaya ya bayyanawa wakilin mu da cewa sun tsaya Sallah a ƙauyen Gidan Hamani ne wannan babbar motar ta zo ta wuce, bayan sun gama Sallah suka fara tafiya, sun kusa shigowa garin Argungu sai suka tarar da wannan motar a gaban su ta ture wannan mai babur ɗin kuma ta ja shi ƙasa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar…
Read More
2027: Kwamitin Abdulsalami ya gargaɗi Tinubu, Atiku, Obi da sauran ’yan siyasa kan rikici a yaƙin neman zaɓe

2027: Kwamitin Abdulsalami ya gargaɗi Tinubu, Atiku, Obi da sauran ’yan siyasa kan rikici a yaƙin neman zaɓe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kwamitin Samar da Zaman Lafiya na ƙasa, wanda tsohon Shugaban ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ke jagoranta, tare da Babban Limamin Cocin Katolika, Most Reɓ. Matthew Kukah, a matsayin mai gudanar da shi, ya gargadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran ’yan siyasa kan yin kamfen mai ɗauke da kalaman tayar da hankali ko tunzura jama’a gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Kwamitin ya kuma nuna damuwa kan rahoton samun wasu al’amura 60 da suka shafi zaɓe a sassa daban-daban na ƙasar cikin wata guda, ciki…
Read More
Yadda magungunan gargajiya ke jefa ’yan Nijeriya haɗari

Yadda magungunan gargajiya ke jefa ’yan Nijeriya haɗari

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Aƙalla mutane 48 ne suka rasa rayukansu a Jihar Ondo bayan shan wani maganin gargajiya da aka fi sani da ‘agbo’, lamarin da ya sake jawo hankali kan haɗarin amfani da magungunan gargajiya ba tare da kulawar ƙwararrun ma’aikatan lafiya ba. Lamarin ya faru ne a ƙaramar Hukumar Odigbo, inda sama da mutane 170 kuma suka kamu da rashin lafiya mai tsanani bayan shan gaurayen maganin, kamar yadda Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC) da jami’an lafiya na jihar suka bayyana. Mutanen da abin ya shafa sun fito daga al’ummomin Araromi-Obu, New…
Read More
Tsohuwa mai shekaru 67 da wani soja sun kammala karatu a Afrika Academy — Malam Rabiu

Tsohuwa mai shekaru 67 da wani soja sun kammala karatu a Afrika Academy — Malam Rabiu

Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano Sakamakon kyakkyawan tsarin karatun da Afrika Academy da ke Kano ke gudanarwa ta hanyar sadarwa ta zamani, wato intanet, ko kuma tsarin karatun online, wata tsohuwa mai shekaru 67 da ke Jihar Kaduna ta samu takardar shaidar kammala karatun ƙwarewa na Diploma a kan ilimin addinin Musulunci. Malam Rabiu Yusuf, Shugaban Afrika Academy, ya bayyana cewa tsohuwar ta kammala karatun ne a fannoni shida da suka haɗa da Tafsiri, Sirar Ma’aiki (SAW), Tauhidi, Hadisi, Fiƙihu da kuma ilimin Tarbiyya domin kyautata zamantakewa a tsakanin al’umma. Ya kuma bayyana cewa wani soja da ke fagen fama…
Read More
Ma’aikatan matatar mai ta Fatakwal sun yi barazanar rufe aiki saboda bashin albashin watanni bakwai

Ma’aikatan matatar mai ta Fatakwal sun yi barazanar rufe aiki saboda bashin albashin watanni bakwai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ma’aikatan da ke ƙarƙashin ƙungiyar Support Staff Union ta Kamfanin Matatar Mai na Fatakwal (PHRC), sun yi barazanar rufe ayyukan matatar idan ba a biya su albashin watanni bakwai da ake binsu ba, tare da aiwatar da sabon tsarin albashin da suka ce an amince da shi. Ma’aikatan sun gudanar da zanga-zanga tare da tare ƙofar shiga matatar, inda suka ce idan ba a biya bukatunsu cikin sa’o’i 48 ba, za su rufe matatar gaba ɗaya. Sun kuma buƙaci a aiwatar da sabon tsarin albashi da alawus-alawus da suka ce GCEO na NNPC, Bayo…
Read More
AKCOE ta yaye ɗaliban da suka kammala digiri a karo na farko — Dakta Ayuba

AKCOE ta yaye ɗaliban da suka kammala digiri a karo na farko — Dakta Ayuba

Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano A karon farko, Kwalejin Ilimi ta Aminu Kano, wadda aka fi sani da AKCOE, ƙarƙashin jagorancin Dr. Ayuba Ahmad Muhammad, mai haɗin gwiwa da Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA), ta gudanar da bikin yaye ɗalibai maza da mata da suka kammala karatunsu na digiri a fannoni daban-daban. Shugaban kwalejin ya bayyana hakan ne a wani gagarumin biki da aka gudanar a ƙarshen makon da ya gabata a birnin Kano. Haka kuma, ya ƙara da cewa wannan kwaleji na daf da zama jami’a, kamar yadda shugaban kwalejin ya bayyana a lokacin bikin yaye ɗaliban da suka…
Read More
Daukar dubban matasa aiki a 123 Homes na rage wa gwamnati nauyi — Tajuddeen UAC

Daukar dubban matasa aiki a 123 Homes na rage wa gwamnati nauyi — Tajuddeen UAC

Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano An bayyana cewa duk wata masana’anta ko kamfani da makamantansu da suka ɗauki matasa aiki, to hakan na rage wa gwamnati nauyi ne. Saboda haka, shugaban kamfanin gine-gine da samar da filaye domin amfanin al’umma, kuma Manajan Darakta na 123 Homes & Facility Managers Ltd, Alhaji Tajudden Musa UAC, ya ce kamfaninsu ya ɗauki ɗimbin matasa aiki domin bunƙasa tattalin arzikin al’umma da ƙasa baki ɗaya. Ya ce kamfanin na ƙoƙarin tabbatar da cewa ana gudanar da komai bisa tanadin doka, ta hanyar biyan dukkan haƙƙoƙin gwamnati da sauran hukumomi a kowane mataki. Ya ce…
Read More