ukarofi

12433 Posts
Sauyin Sheƙa: Dan Majalisar Tarayya na Kura ya karɓi ƙungiyoyin APC zuwa NDC

Sauyin Sheƙa: Dan Majalisar Tarayya na Kura ya karɓi ƙungiyoyin APC zuwa NDC

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kura, Madobi da Garun Malam, Hon. Yusuf Umar Datti Kura, ya karɓi ƙungiyoyi sama da goma na jam’iyyar APC da suka sauya sheƙa zuwa NDC a yankin Kura. An gudanar da taron ne a ranar Asabar da ta gabata a filin makarantar firamare da ke garin Karfi. Da yake jawabi, Datti Kura ya ce sauyin sheƙar na nuna cewa al’umma sun fahimci, a cewarsa, irin matsin rayuwar da gwamnatin APC ta jefa ƙasar a ciki. Ya kuma yaba wa waɗanda suka shigo NDC, tare da cewa za su taka…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta tura tawaga zuwa Habasha domin musayar ƙwarewar shugabanci

Gwamnatin Tarayya ta tura tawaga zuwa Habasha domin musayar ƙwarewar shugabanci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai kasance cikin tawagar manyan jami’an Nijeriya da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da aikewa birnin Addis Ababa na Habasha, domin gudanar da shirin musayar ƙwarewa da dabarun shugabanci tsakanin Nijeriya da Habasha. Tawagar Gwamnatin Tarayya za ta kasance ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, tare da haɗin kan Gwamna Dauda Lawal na Zamfara da wasu gwamnoni. Ana sa ran tawagar za ta tashi daga Nijeriya ranar Talata domin halartar taron musayar ƙwarewar shugabanci tsakanin Nijeriya da Habasha, wanda za a gudanar daga ranar 7 zuwa…
Read More
Muna shirya mauludi domin murnar tunawa da fiyayyen halitta — Abba Mai-Kayan-Doki

Muna shirya mauludi domin murnar tunawa da fiyayyen halitta — Abba Mai-Kayan-Doki

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano An bayyana lokacin Maulidi a matsayin wani lokaci da ake nuna murnar haihuwar Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (SAW). Shugaban ƙungiyar Masu Sayar da Kayan Doki ta Kasuwar Kurmi, Chiroman Kasuwar Kurmi, kuma Madawakin Alin Mashuwa na Jihar Legas, Alhaji Abba Mai Kayan Doki, ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai a wajen Maulidin da ƙungiyar ta saba shirya wa duk shekara a Kasuwar Karo na Sha Biyar. Alhaji Abba ya ce kasancewarsu a wannan hidima da suke shirya wa duk shekara na nuna irin farin ciki da annashuwar da suke ji wajen…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta horas da tubabbun ’yan bindiga dubu

Gwamnatin Katsina za ta horas da tubabbun ’yan bindiga dubu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta fara tantance tubabbun ’yan bindiga marasa aikin yi guda 1,000 domin ba su horo kan sana’o’i daban-daban tare da koyar da su ilimin addinin Musulunci. Shirin na ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Youth Mobilizers for Peace and Progress Forum, tare da haɗin gwiwar Sautus Sunnah Charity Foundation. Shirin na da nufin bai wa matasan jihar damar samun ilimi da dabarun dogaro da kai, musamman ta hanyar koyar da sana’o’in da za su taimaka wajen samar musu da hanyoyin samun abin dogaro da kai, da kuma rage matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa.…
Read More
Makarantar Kimiyya da Fasaha a Dawakin Kudu ta yi taron iyayen ɗalibai

Makarantar Kimiyya da Fasaha a Dawakin Kudu ta yi taron iyayen ɗalibai

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Makarantar Kimiyya da Fasaha da ke ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu ta gudanar da taron haɗin gwiwa da iyayen ɗalibai domin tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban karatu, tarbiyya da kyautata harkokin makarantar. Taron ya samu halartar iyaye da masu ruwa da tsaki, inda aka tattauna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin makaranta da iyaye wajen tabbatar da samun ingantaccen ilimi da tarbiyya ga ɗalibai. Tun da fari, Shugaban ƙungiyar Iyayen da Malamai ta makarantar (PTA), Alhaji Auwal Iliyasu, ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin iyaye da makaranta, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta…
Read More
2027: Masallatai da coci-coci su nisanci kamfen na siyasa

2027: Masallatai da coci-coci su nisanci kamfen na siyasa

Yayin da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027 ke ƙara ɗaukar zafi, shugabannin haɗin gwiwar Majalisar ƙasa ta Addinai (NIREC), wato Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, da Shugaban ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN), Archbishop Daniel Okoh, sun yi gargaɗi ga shugabannin addinai kan amfani da mimbari, coci-coci, masallatai da sauran dandalan addini wajen rura wutar siyasa ko tayar da rikicin addini a lokacin da ake tunkarar zaɓe. Haka kuma, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume; Babban Sakataren NIREC, Farfesa Cornelius Afebu Omonokhua; da Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, sun…
Read More
2027: Kotu da INEC sun ɗaura ɗamara

2027: Kotu da INEC sun ɗaura ɗamara

*Mun shirya tsaf don tunkarar zaɓen 2027 – INEC *Za mu sa ido kan take-takenku – Alƙalin-alƙalai ga masu shari’a Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babbar Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Kudirat Motomori Kekere-Ekun, ta gargaɗi alƙalan da za a naɗa domin zama a kotunan sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da su tabbatar da cewa sun kasance masu gaskiya da adalci, tana mai cewa za a sa ido sosai tare da bibiyar yadda suke gudanar da ayyukansu. CJN ta kuma gargaɗi lauyoyi da kada su yi amfani da ’yancinsu na sukar hukuncin kotu ko yadda ake gudanar da shari’a wajen kai wa…
Read More
Tinubu ya rage farashin fetur na wata guda

Tinubu ya rage farashin fetur na wata guda

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin rage farashin man fetur da ake sayarwa a gidajen man Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL) na tsawon kwanaki 30, a wani sabon mataki da ta ce an ɗauka ne domin rage wa ’yan Nijeriya raɗaɗin tsadar fetur da sufuri. Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana shirin a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai kan farashin man fetur da batun tallafin mai, wanda aka gudanar a Abuja. Oyedele ya bayyana cewa, za a fara aiwatar da rangwamen ne na tsawon kwanaki…
Read More
Idan ka ga ɗan PDP a Kebbi to ɗan kwangila ne – Dagwaya

Idan ka ga ɗan PDP a Kebbi to ɗan kwangila ne – Dagwaya

Mataimakin shugaban jam'iyyar ADC na jihar Kebbi Alhaji Musa Muhammed Dagwaya ya bayyana cewa yanzu idan ku ka ga wani ɗan jam'iyyar PDP a jihar Kebbi ɗan kwangila ne.Ya yi wannan bayanin ne a garin Felande yayin wata ziyarar sada zumunci da ayarin sa ya kai ranar Lahadin da ta gabata. Alhaji musa Dagwaya ya ce su ne suka zo da PDP suka yi rainon ta har ta bunƙasa kuma sun rusa ta babu labarin ta yanzu a Kebbi. Duk mai hankali ya san akwai yan kwangila da ke yi wa gwamnatin APC aiki suna yaudarar mutane da sunan yayan…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta gyara ƙarin makarantun firamare 68 a faɗin jihar

Gwamnatin Katsina za ta gyara ƙarin makarantun firamare 68 a faɗin jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya amince da gyaran wasu ƙarin makarantun firamare 68 da suka lalace a faɗin jihar. Wannan amincewa ta zama kashi na uku na shirin gaggawa na gwamnatin jihar na gyaran makarantun firamare da suka lalace, kamar yadda wata sanarwar manema labarai da Hon. Lawal Rufa’i Safana, Mai Ba Gwamnan Shawara kan binciken ƙananan hukumomi kuma shugaban kwamitin da ke kula da shirin, ya fitar. Kwamitin ya ce makarantun 68 da aka zaɓa sun ƙunshi makarantu biyu daga kowace ƙaramar hukuma 34 na jihar. Wannan kashi na baya ya…
Read More