Ba zan jajanta maka ba don kai ka nace ka zama shugaban ƙasa – Akande ga Buhari

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Chief Bisi Akande ya ce ko kaɗan ba zai jajanta wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba dangane da suka da yake samu bisa ƙalubalolin rashin tsaron ƙasa, domin shi ya nemi ya zama shugaban Nijeriya.

Akande ya yi wannan furuci ne a bikin gabatar da wani littafi mai ɗauke da tarihinsa da aka yi wa laƙabi da “Gudunmawa Ta” wanda Shugaba Buhari ya halarta da aka gudanar a Otal ɗin Eko dake Ikko jiya Alhamis.

Waɗanda suka halarci bikin gabatar da littafin sun haɗa da Jigon jam’iyyar APC, kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu; Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola da Kakakin majalisar dokoki ta jihar Legas, Mudashiru Obasa.

Tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel; Ministan Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola wanda wakilin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje mataimakin sa Gawuna ya wakilta; Gwamnan jihar Kwara, Abdulraham Abdulrazak, da Ooni na Ife, Oba Enitan Ogunwusi.

Sauran sun haɗa da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, Sanata Tokunbo Abiru, Sanata Solomon Adeola, da Sanata mai wakiltar mazaɓar yammacin Legas, Opeyemi Bamidemi, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, Sanata Musuliu Obanikoro, Sanata Ganiyu Olarewanju Solomon, Sanata Tokunbo Afikuyomi, Kwamishinoni jihar Legas, Jiga-jigai magoya bayan Bola Ahmed Tinubu, Matan SWAGA da ke Legas, Tawaga daga jihar Osun, Basaraken jihar Legas, Oba Rilwanu Akiolu I, wanda ya samu wakilcin masu riƙe da masarautun gargajiya, da dai sauran su.

Akande ya ce “Mu ‘yan Nijeriya mun san kana qaunar ƙasar nan, amma muna buƙatar Nijeriya ta ɗaukaka, muna kuma zargin ka da duk ababen da suka saɓa wa ƙasar nan.

“Mun san mu almubazarai ne, macuta kuma ga duk wasu laifukan mu za mu zarge ka ne. Ba zan jajanta maka ba domin kai ka zaɓi riƙe wannan aiki na shugabanci.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *