Boko Haram, ISWAP sun mamaye Zamfara – Dr Shinkafi

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da cewa, umarnin da gwamnatin jihar ta bayar na dakatar da duk wasu harkokin siyasa a jihar, ta yi ne sakamakon bayanan sirrin da ta samu wanda ya nuna wasu ‘yan ƙungiyar Boko Haram da ISWAP na lardin yammacin Afrika, sun mamaye wasu sassan jihar.

Shugaban kwamitin zartar da hukunci a kan ayyukan ta’addanci a jihar, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Gusau ran Talata.

Shinkafi wanda shi ne tsohon sakataren Jam’iyyar APGA na ƙasa, ya bayyana cewa matakan da gwamnan jihar ya ɗauka sun dogara ne da dokar zartarwa mai lamba 10 da nufin kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a jihar.

A cewarsa, bayanan sirri da aka tattara sun nuna kimanin ‘yan bindiga 1,200 ne ke shirin kai munanan hare-hare a sassan jihar.

“An hango ‘yan Boko Haram da ISWAP a wani ƙauye da ake kira Mutu a gundumar Mada ta Ƙaramar Hukumar Gusau a kan babura sama da sittin, ana zarginsu da shirin kai munanan hare-hare kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

“Gwamna Matawalle ya ɗauki matakan ne bisa tsarin zartaswa mai lamba 10, sashe na 5(2), 176(2), da 315(2) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima kan matsalolin rashin tsaro a kan iyaka da jihar,” inji shi.

Dangane da batun rufe wasu kafafen yad’ɗa labarai a jihar, Shinkafi ya ce kafafen da abin ya shafa sun taka dokar ƙasa a rahotanninsu ta hanyar yaɗa labari na jam’iyyar adawa a lokacin da ake cikin yanayin rashin tsaro tare da bijire wa umarnin dakatar da duk lamurran siyasa da gwamnatin jihar ta bayar.

Shinkafi ya ƙalubalanci Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labara ta Nijeriya (BON) da fitar da bayanan ƙarya kan matakin da Gwamna Bello Mohamed Matawalle ya ɗauka na rufe wasu kafafen yaɗa labarai huɗu a jihar.

Ya bayyana furucin da sakataren zartarwa na BON ya yi da cewa, siyasa ce da rashin bin tafarkin demokraɗiyya.

Dakta Sani Shinkafi ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa a jihar da kuma ƙananan hukumomi baki ɗaya da su daina siyasantar da matsalolin rashin tsaro da suka addabi jihar sakamakon ayyukan ta’addanci da ‘yan fashi da makami ke yi da kuma taimaka wa gwamnati kan yadda za ta magance wannan al’amari.