Buɗaɗɗiyar wasiƙa ga al’ummar Kano game da ƙidaya

Daga ABDULBAQI ALI AHMAD SHARIFAI

Assalamu alaikum al’ummar jihata ta Kano mai albarka, da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya.

Bayan haka, na rubuta wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa ne gare ku a kan abinda yake tunkarar mu na ƙidayar al’ummar ƙasar nan da za a fara a wata mai kamawa. Ku sani, ta wannan hanya ce ake rabon arzikin ƙasa gwargwadon yawan jama’a, ta haka ne kuma gwamnati ke aiwatar da ayyukan raya ƙasa.

Muna da ƙalubale mai tarin yawa da muke buƙatar kulawar gwamnati musamman ta la’akari da yawanmu. Sai dai kash, sakacin shugabanni da talakawanmu na janyo mana asara mai tarin yawa, saboda rashin tsayawa a yi abinda ya kamata.

Tabbas yawanmu ba ƙarya ba ne, saɓanin yadda abokan zamanmu ke ikirarin wai ana haɗawa da tumakinmu a wajen ƙirga mu, shi yasa a kullum suke ganin damarmu duk kuwa da cewa tunda ake ƙidaya a Najeriya tun daga 1954 zuwa yau ba su taɓa fin mu yawa ba.

Shekaru 17 kenan rabon da a yi ƙidaya a Najeriya, duk da cewa a ƙa’idar da majalisar dinkin duniya ta sanya duk shekara 10 ne za a riƙa yi. A don haka, mu yi wa Allah da ma’aiki Sallalahu Alaihi Wasallam mu fito da iyalanmu a ƙidaya mu.

Yo idan ba rainin wayo ba, ina za ka ha ɗa mai auren mata huɗu da mai auren mace daya jallin jal kamar fitilar babur? Na barku lafiya.

Abdulbaki Ali Ahmad Sharifai, gogaggen ɗan jarida ne, kuma mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum. Ya rubuto ne daga Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *