Buhari ya yi na’am da sabon tsarin albashin fansho mafi ƙaranci

Daga FATUHU MUSTAPHA

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yarda a biya masu karɓar fansho da sabon tsarin albashi mafi ƙaranci.

Sakatariyar Hukumar Fansho, Dr Chioma Ejikeme, ita ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai a Abuja a Juma’ar da ta gabata.

Jami’ar ta ce da wannan amincewar da aka samu daga wajen Shugaban Ƙasa, an ƙarfafa wa kwamitin PTAD kan ya soma gyare-gyare game da abin da ake biyan masu karɓar fansho domin ya daidaita da sabon tsarin biyan haƙƙoƙin nasu.

Ejikeme ta ce sabon tsarin biyan fansho ɗin zai soma aiki ne daga Mayu, 2021. Ta kara da cewa, biyan ariyas na ‘yan fansho ɗin zai gudana ne a tsawon lokacin da za a ɗauka wajen ɗabaƙa biyan sabon tsarin albashin fansho.

A cewarta, “Za a biya ariyas na Afrilu 2021 tare da albashin fansho na wata-wata da aka saba biya daga watan Mayun 2021.”

Ta ce tun ran 22 ga Afrilu aka saki bayanin sanar da al’umma ƙudurin Shugaban Kasa a kan biyan albashin fansho mafi ƙaranci.

Sakatariyar ta jaddada cewa Ƙungiyar Masu Karɓar Fansho ta Ƙasa ba ta da wani dalilin da zai sa ta gudanar da zanga-zanga saboda an rigaya an cim ma matsaya kan batun.

Ta ce a matsayin hukumar gwamnati da aka ɗora wa alhakin sanya ido game da sha’anin fansho da biyan masu haƙƙi haƙƙoƙinsu, an ƙarfafa mata gwiwa don ta zage damtse wajen ci gaba da yi wa masu karɓar fansho hidima yadda ya kamata. “Kuma za mu ci gaba da ƙoƙari don ganin mun inganta rayuwarsu”, in ji Ejikeme.

A ƙarshe, jami’ar ta roƙi ƙungiyoyin masu karɓar fansho da su zamo masu bada haɗin kansu ga hukumar a kowane lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *