Rahoto

Gwamnatin Zamfara ta ƙwato motoci 50 daga hannun Matawalle

Gwamnatin Zamfara ta ƙwato motoci 50 daga hannun Matawalle

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce, ta kwato motoci kusan 50 mallakin gwamnatin jiha da ake zargin tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya tafi da su. Da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Gusau, Sani Sambo, mai magana da yawun gwamna Dauda Lawal ya ce matakin ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Sokoto ta yanke a ranar Juma’ar da ta gabata. Ya qara da cewa, an bi tsarin da ya dace domin kwato motocin daga gidajen Gusau da Maradun na tsohon gwamnan wanda a baya ya musanta cewa ya mallaki…
Read More
Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya 9,000 daga 13,000 sun faɗi jarrabawar ƙarin girma

Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya 9,000 daga 13,000 sun faɗi jarrabawar ƙarin girma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Aƙalla ma’aikatan gwamnati 9,000 da suka zana jarrabawar ƙarin girman ma’aikatan Gwamnatin Tarayya na shekarar 2022 sun faɗi. An samu wannan adadi ne daga Hukumar Ɗa’ar Ma’aikata ta Tarayya.An ce aƙalla ma’aikatan gwamnati 13,000 ne suka zana jarrabawar ta shekarar 2022, wadda aka gudanar a kusan cibiyoyin gwajin kwamfuta 69. An zaɓo ma'aikatan ne daga manyan ma’aikatan gwamnati, ’yan sandan Nijeriya, da sauran jami’an soji da sauran hukumomin tsaro. Wasiƙar mai ɗauke da jerin sunayen ma’aikatan da suka yi nasara ta kasance a ranar 30 ga Nuwamba, 2023 kuma an aiko ta daga Hukumar Kula da…
Read More
’Yan bindiga sun sake sace ɗaliban jami’ar Nasarawa

’Yan bindiga sun sake sace ɗaliban jami’ar Nasarawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ’yan ta'adda da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun afka wa al’ummar Gandu tare da yin garkuwa da wasu ɗalibai a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Lafia. Wani ɗalibin jami’ar da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa 'yan bindigar sun zo ne da farko a yawansu da misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Laraba inda suka fara harbi a iska don tsoratar da mazauna yankin, amma daga baya sun fara harbi kan mai uwa da wabi, lura da cewa jami'an tsaro na tahowa sai suka tsere cikin daji domin…
Read More
Kasafin Naira Tirilyan 27 na 2024 ya cika tirela

Kasafin Naira Tirilyan 27 na 2024 ya cika tirela

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Haƙiƙa ko dai yawan tarin takardun kuɗin da su ka kai Naira Tirilyan 27 ba su cika babbar motar ɗaukar kaya wato tireba ba to za su dai cika waje mai faɗin gaske a motar. Ko ni mai rubutun nan ban tava ganin Naira tirilyan a kan takarda ba. Naira tirilyan na nufin Naira biliyan 1000. Naira biliyan na nufin Naira miliyan 1000. Naira miliyan na nufin Naira dubu ɗari sau 10. Kawai na kiyasta ne yadda yawan kuɗin su ke in an zuba su a ɗaki ko a cikin mota. A watannin baya kafin…
Read More
Masallacin Adogba: Sarkin Musulmi da Makinde sun kafa turbar kawar da ƙabilanci da bambancin addini

Masallacin Adogba: Sarkin Musulmi da Makinde sun kafa turbar kawar da ƙabilanci da bambancin addini

Daga AISHA ASAS A kwanaki ne aka ƙaddamar da babban masallacin Juma’a na unguwar Adogba da ke garin Ibadan wanda Mai Alfarma Sarkin Musulmi na Sakkwato, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya jagorancin buɗewa, Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya gina, bayan da a ka rusa tsohon masallacin a shekara ta 2019, don sabunta ta don samar da qarin fahimtar juna da kuma kawar da bambancin ƙabilanci da na addini. A lokacin da gwmanatin jihar Oyo ta rusa masallacin Adogba wanda ake kuma kira da ‘Organisation of Tadhamunul Muslimeen Mosque’, da ke Adogba, a kan hanyar Iwo a cikin garin…
Read More
Yadda bikin auren jaruma Rashida Maisa’a ya gudana

Yadda bikin auren jaruma Rashida Maisa’a ya gudana

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano A ranar Asabar ɗin da ta gabata, 11 ga Nuwamba, 2023 ne aka ɗaura auren jaruma a Kannywood Rashida Adamu Abdullahi Maisa'a, da angonta Alhaji Aliyu Adamu, Sardaunan Matasan Gwoza. An ɗaura dai a layin Malam Bello a Unguwar Daurawa, daura da babban Titin Maiduguri a cikin garin Kano, kuma an samu halartar jama'a masu yawa da suka shaida an ɗaura auren. Ita dai Rashida Adamu Abdullahi ba ta shirya wani taron shagulgulan biki ba, kamar yadda jaruman fim suka saba yi. An dai tara malamai a gidanta inda suka wuni suna karatun Alƙur'ani mai…
Read More
Bisa shirin saƙi da cin zarafin mata na “EU-UN Spotlight Initiative”, mun samu gagarumin cigaba – Uwargidan Gwamnan Legas

Bisa shirin saƙi da cin zarafin mata na “EU-UN Spotlight Initiative”, mun samu gagarumin cigaba – Uwargidan Gwamnan Legas

Daga WAKILINMU Uwargidan Gwamnan Jihar Legas, Dr. Ibijoke Sanwo-Olu, ta bayyana cewa, sakamakon goyon bayan da suka samu daga shirin Tarayyar Turai (EU) da Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) na yaki da cin zarafin mata, Jihar Legas ta samu gagarumin ci gaba wajen samar da al’ummar da kowace ‘ya mace za ta iya rayuwa ba tare da tashin hankali ko nuna mata wariya ba. "Ta hanyar haɗin gwiwar da muka yi, mun sami ci gaba sosai wajen samar da al'ummar da kowace mace za ta yi rayuwa ba tare da tashin hankali da wariya ba." Ta bayyana a wurin rufe shirin…
Read More
Abin takaici ne yadda wasu alaramomi ke harkokin addini, inji Sarkin Misau 

Abin takaici ne yadda wasu alaramomi ke harkokin addini, inji Sarkin Misau 

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Mai Martaba Sarkin Misau, Alhaji Ahmed Suleiman, ya bayyana takaicinsa bisa yadda ake kiran malamin tsangawa ko Islamiyya da alaramma, amma idan aka yi bibiyar iliminsa, sai a iske bai ma iya gudanar da ayyukansa na ibada da aka halatta masa, domin gudanar da su ba. Sarkin ya ce, "Abu ne na ban takaici matuƙa gaya, ka ga mutum ana ce da shi Alaramma, amma sai a iske yadda yake yin alwala ma akwai gyara ko kura-kurai a ciki, lamarin da ya kasance koma-baya wa sahihin ibadojin mutum da rayuwar sa." Sarkin na Misau sai…
Read More
‘Yan sanda sun halaka ƙasurgumin ɗan bindiga a Katsina

‘Yan sanda sun halaka ƙasurgumin ɗan bindiga a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar 'yan sanda a Jihar Katsina ta bayyana cewar ta samu nasarar hallaka wani ƙasurgumin varawon daji mai suna Nazifi Ibrahim. Rundunar ta kuma ƙwato tarin alburusai da wasu makamai a yayin fafatawa da ta wakana tsakanin su da wata tawagar masu garkuwa da mutane, a Ƙaramar Hukumar Faskari dake jihar ta Katsina. Kakakin rundunar, ASP Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar game da yaƙi da 'yan ta'addan daji a jihar. A cewar sanarwar, a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 rundunar ta samu bayanai da ke nuni…
Read More
Majalisar Wakilai ta fusata da shugabannin tsaro kan bijire wa gayyatarta

Majalisar Wakilai ta fusata da shugabannin tsaro kan bijire wa gayyatarta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Wakilai ta fusata kan rashin halartar hafsoshin tsaro da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, a wani zama na mu’amala da aka shirya gudanarwa a jiya Alhamis yayin zaman majalisar. A maimakon haka dai shugabannin tsaro sun tura wakilai. A makon da ya gabata ne dai majalisar ta shirya muhawara a sassa daban-daban da shugabannin tsaro yayin da take shirin yi da sauran sassan ƙasar. Biyo bayan wani tanadi da kundin tsarin mulki ya bayar na mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu, majalisar ta ƙi amincewa da wakilcin shugabannin tsaro, maimakon haka ta…
Read More