29
Dec
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An cafke wata dalibar Kwalejin Kiwon Lafiya da ke Kontagora, kan zarginta da kai wa ’yan bindiga bayanai a Jihar Neja. Kwamishinan ’yan sandan Jihar Neja, Shawulu Ebenezer Danmamman, ya ce an cafke dalibar da ke karatu a Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya da ke Kontagora ne bayan an kama wani dan bindiga mai shekara 37. A yayin binciken dan bindigan da aka kama a garin Kontagora ne aka gano lambar dalibar a cikin wayarsa. Ita kuma a wurin bincike aka gano sunan wani dan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Shaibu Haruna a…
