Rahoto

Zan tabbatar da bai wa duniya labarin Nijeriya da Afirka – Shugaban Muryar Nijeriya

Zan tabbatar da bai wa duniya labarin Nijeriya da Afirka – Shugaban Muryar Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Hukumar Muryar Nijeriya, Mallam Jibrin Baba Ndace, ya ce hukumar za ta hada kai da masu ruwa da tsaki wajen bai wa duniya labaran Nijeriya da Afirka. Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da ya jagoranci ma’aikatan hukumar a ziyarar ban girma da ya kai hedikwatar Media Trust da ke Abuja. Yayin da ya bayyana Nijeriya a matsayin kasar da ba ta cika dari bisa dari, ya ce akwai labarai masu kyau da yawa da za a fada game da Nijeriya. “A Muryar Nijeriya abin da nake yi tun lokacin da…
Read More
Gwamnan Kebbi ya rantsar da Alƙalin-alƙalai da shugabannin wasu hukumomi 

Gwamnan Kebbi ya rantsar da Alƙalin-alƙalai da shugabannin wasu hukumomi 

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi  Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya rantsar da Mai shari'a Umar Abubakar a matsayin babban alqali da Khadi Sadiq Usman Mukhtar a matsayin Grand Khadi na jihar. Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu ne ya kaddamar da bikin rantsarwar a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Birnin Kebbi a ranar Litinin. Da yake gabatar da mutanen biyu ga gwamnan domin rantsar da shi, sakataren gwamnatin jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Bala Tafida ya kuma karanta sunayen shugabanni da mambobin hukumar da Parastatals da za a kaddamar. Bayan rantsuwar, Gwamna Nasir…
Read More
Hazo: NiMET ta gargaɗi masu cutar asma da ma’aikatan jirgin sama

Hazo: NiMET ta gargaɗi masu cutar asma da ma’aikatan jirgin sama

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya, NiMET,  ta ba da sanarwar taka-tsantsan ga masu fama da cutar asma da masu fama da lalurar numfashi da kuma ma'aikatan jirgin sama kan yanayin buji mara kyau da ke tafe. Rahoton da hukumar kula da yanayi ta fitar a ranar Talata ya kuma yi hasashen yanayin zafi da sanyi a jihohin Arewa ta tsakiya na kasar nan daga ranar Laraba 3 ga watan Janairun 2024. "An shawarci mutanen da ke fama da asma da sauran matsalolin numfashi da su yi taka-tsantsan game da yanayin", inji rahoton. "An shawarci ma'aikatan…
Read More
An ƙaddamar da bikin girbin amfanin noma a gonar Daɗin Kowa a Funtuwa

An ƙaddamar da bikin girbin amfanin noma a gonar Daɗin Kowa a Funtuwa

Daga WAKILINMU An kaddamar da bikin cire shinkafa da albarkatun noma na bana a gonar 'Daɗin Kowa Farm’ dake garin Dakamawa a karamar hukumar Funtuwa dake Jihar Katsina. Bikin wanda ya kasance ana aiwatar da shi a karshen damina duk shekara ya kayatar yayin da a ka samu albarkatun noma fiye da na shekarun da suka shude, inda aka samu shinkafa wacce ta fi ta ko'ina yawa da albarka har tan miliyan daya a mashahuriyar gonar ta Daɗin Kowa. Sauran albarkatun noman da aka girbe sun hada da farin wake, masara, gero da dai sauransu. Hajiya Zainab wacce aka fi…
Read More
Akwai buƙatar kowa ya sa hannu wajen farfaɗo da ilimin firamare a Zariya – Dr. Hassana

Akwai buƙatar kowa ya sa hannu wajen farfaɗo da ilimin firamare a Zariya – Dr. Hassana

Daga ISAH GIDAN ƁAKKO a Zariya Sakatariyar Ilimi ta Karamar Hukumar Zariya, Dokta Hassana Muhammad Lawal ta bayyana kudurinta na bin duk hanyoyin da su ka dace domin kawo karshen matsalolin da suke addabar makarantun firamare a karamar hukumar Zariya. Dr. Hassana Lawal ta bayyana haka ne a jawabin da ta yi a lokacin dora dambar makarantun firamare da suke qaramar hukumar Zariya, inda ta fara da makarantar firamare ta Zage-zagi a birnin Zariya. Dr. Hassana ta bankado matsalolin da su ke addabar makarantun firare a karamar hukumar Zariya da suka hada da gine-ginen gidaje da sauran gine-gine da al'umma…
Read More
Emefiele: EFCC ta kai wa Ɗangote sumame bayan rikitowarsa a matsayin attajirin Afirka

Emefiele: EFCC ta kai wa Ɗangote sumame bayan rikitowarsa a matsayin attajirin Afirka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami’an Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati, EFCC, a ranar Alhamis, sun kai samame babban ofishin Kamfanin Dangote dake Legas. Kamar yadda shafin jaridar TheCable ya rawaito, jami’an hukumar sun gudanar da bincike kan kudaden da aka ware wa kamfanin a zamanin Godwin Emefiele, tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN. Amma Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya qi cewa komai kan batun. Sai dai wani ma’aikacin Kamfanin Dangote ya tabbatar da cewa, jami’an EFCC na nan a babban ofishin kamfanin. “Sun bukaci a ba su takardu kan hada-hadar kudi da CBN,” inji ma’aikacin.…
Read More
Sauyin yanayi: Ƙalubalen da wasu garuruwa ke fuskanta a Jihar Yobe

Sauyin yanayi: Ƙalubalen da wasu garuruwa ke fuskanta a Jihar Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Rahoton da Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya ta fitar a 2019 ya bayyana cewa Nijeriya ta na asarar kimanin fili mai fadin murabba'in kadada 350,000 a duk shekara, sakamakon yadda hamada ke ci gaba da mamayewar yankuna, wanda hakan ya na faruwa ne ta musababbin sauyin yanayi, mai alaka da ayyukan yau da kullum da Dan Adam masu jawo dumamar yanayi. A nata bangaren, a wani sabon binciken da Hukumar Agora Policy ta gudanar a wannan shekara (2023), ta bayyana cewa, Nijeriya za ta iya yin hasarar Dalar Amurka kimanin biliyan 460 sakamakon sauyin…
Read More
Emefiele ya nesanta kansa daga zarge-zargen talauta Nijeriya

Emefiele ya nesanta kansa daga zarge-zargen talauta Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya karyata zargin da Mai Binciken CBN Na Musamman da Shugaba Bola Tinubu ya nada ya yi masa, wato Jim Obazee. Kwanan nan Obazee ya gabatar wa Tinubu rahoton harqallar da ya bankado Emefiele ya aikata a CBN, wadda aka yi zargin ya bindige biliyoyin nairori da biliyoyin daloli. Cikin harkallar da Obazee ya bankado har da badakalar sauya launin kudi, wadda Obazee ya ce damfara ce kawai sata Emefiele ya kantara. Da ya ke karyata zarge-zargen da Obazee ya yi masa Emefiele a ranar Lahadi…
Read More
Tarihi da siyasar rayuwar Ghali Umar Na’Abba

Tarihi da siyasar rayuwar Ghali Umar Na’Abba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An haife shi ne a gidan Umar Na’Abba, babban dan kasuwa a Tudun Wada, cikin birnin Kano, a ranar 27 ga Satumba, 1958. Mahaifinsa ya kasance mai karfin tarbiyya kuma malamin addinin Musulunci. Mahaifinsa ya koya masa kyawawan halaye na aiki tukuru, kasuwanci, sahihiyar magana, jajircewa, halin sassaucin ra'ayi, hankali, ladabi da son addini sosai. Ilimi: Ya yi makarantar firamare ta Jakara da ke Kano, inda ya samu shaidar kammala karatunsa na farko a shekarar 1969, sannan ya halarci Kwalejin Rumfa da ke Kano, inda ya samu shaidar kammala karatu ta Afirka ta Yamma. A tsakanin…
Read More
Harin Filato: Ku ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki – Sarkin Musulmi ga gwamnati

Harin Filato: Ku ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki – Sarkin Musulmi ga gwamnati

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan harin da aka kai jihar Filato, inda aka kashe sama da mutane 155 a jajibirin Kirsimeti. Ya yi kira ga gwamnati da ta wuce yin Allah wadai da hare-haren tare da inganta matakan tsaro. Ya yi wannan jawabin ne a wajen rufe taron koyar da sana’o’in addinin musulunci karo na 8 da aka gudanar a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa a ranar Larabar da ta gabata, wanda kungiyar dalibai musulmi ta Nijeriya, MSSN ta shirya. Da yake bayyana damuwarsa kan yawaitar tavarvarewar tsaro a…
Read More