Rahoto

Manyan kamfanonin duniya na buƙatar finafinan Kannywood, inji shugaban MOPPAN mai murabus

Manyan kamfanonin duniya na buƙatar finafinan Kannywood, inji shugaban MOPPAN mai murabus

DAGA MUHAMMADU MUJITTABA KANO    "Daga cikin sauye-sauye da Kannywood ta samu a zamani shugabancina shine samun canje canje kasuwancin fina-finai wanda aka dai na cinikin ga wuri ga waina aka koma ta kamfanonin sadarwa na zamani irinsu YouTube, wanda yanzu akwai sama da 500 mai makon da ake saida a CD da makamantansu yanzu an wuce wannan an samu cigaba kuma yanzu akwai manyan kamfanonin duniya irinsu Amazon da suke bukatar finafinan Kannywood, wanda wannan abin farin ciki ne da nasarori da aka samu a zamani na," cewar Dakta Ahmad M. Sarari, Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Masu Shirya Finafinai ta…
Read More
Gwamna Nasir ya amince da biyan Naira billiyan 27.5 ga ɗalibai ‘yan asalin Jihar Kebbi 

Gwamna Nasir ya amince da biyan Naira billiyan 27.5 ga ɗalibai ‘yan asalin Jihar Kebbi 

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi  Gwamnan jihar Kebbi Dr. Nasir Idris, Kauran Gwandu ya amince da fitar da N27,500,000 domin  gaggauta biyan kudaden daliban da ke karatu a makarantar shari'a a Nijeriya tare da rijistar dukkan 'yan asalin jihar Kebbi 38 dake wannan makarantar.  Wannan yana qunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan shari'a na jihar Dr. Junaidu Bello Marshal wanda ya raba wa manema labarai a Birnin Kebbi a ranar Litinin din da ta gabata.  A cewar kwamishinan, dalibai 28 Bar Part II za su karvi kudi Naira 750,000 (Naira Dubu Dari Bakwai…
Read More
Dattawan Arewa da na Ibo sun tsoma bakinsu kan tafiye-tafiyen Tinubu

Dattawan Arewa da na Ibo sun tsoma bakinsu kan tafiye-tafiyen Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kungiyar Dattawan Arewacin Nijeriya da takwararta ta Ohanaeze Ndigbo mai kare muradun al'ummar Igbo da wasu kungiyoyin farar hula sun bayyana rashin jin dadinsu game da tafiya zuwa Paris da Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi daidai lokacin da kasar ke fama da karuwar matsalar tsaro. A ranar Laraba 24 ga Janairu ne Shugaba Tinubu ya tafi zuwa Faransa domin wata ziyara ta kashin kai. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar gabanin tafiyar, ta ce Tinubu zai koma Nijeriya cikin makon farko na watan Fabarairu. Sai dai kungiyoyin…
Read More
Ɗan jari-bola ya tsunto bom da ya tashi da almajirai a Borno

Ɗan jari-bola ya tsunto bom da ya tashi da almajirai a Borno

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani abun fashewa ya kashe wasu almajiran wata makaranta hudu tare da wasu mutum biyu da ba a gano su wane ne ba a Karamar Hukumar Gubio da ke Jihar Borno. An ruwaito cewa, shugaban aaramar hukumar Alhaji Mali Gubio ne ya tabbatar mata da faruwar wannan lamari, ya ce abin ya fashe a wani kango da misali qarfe 11 na safiyar Asabar. “Duka mutanen da abin ya rutsa da su sun mutu, don haka ba za mu iya tabbatar da abin da ya faru ba, amma wani abun fashewa ne ya tashi a inda ake…
Read More
Rage adadin masu taimataka wa Shugaban Ƙasa zai shafi ayyukan gwamnati – Tinubu

Rage adadin masu taimataka wa Shugaban Ƙasa zai shafi ayyukan gwamnati – Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya bayar da hujjar cewa ministocinsa 47 ne a majalisar ministoci, inda ya ce adadin ya nuna irin ayyukan da ake bukata domin tafiyar da gwamnati mai inganci. Shugaban ya nuna shakku kan rage yawan majalisar ministocinsa, yana mai cewa babu tabbacin hakan zai inganta ayyuka. Ya kuma bukaci shugabannin kungiyar Kiristoci ta Nijeriya da su yada sakon haquri da fata a tsakanin ’yan Nijeriya, yana mai gargadin cewa akasin haka na iya cutar da kasar nan ba tare da gyarawa ba. Tinubu, wanda ya jaddada rawar da shugabannin addinai ke takawa…
Read More
Ba zan taɓa cin amanar Kwankwaso ba – Abba Gida-gida

Ba zan taɓa cin amanar Kwankwaso ba – Abba Gida-gida

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa ba zai taba cin amanar mai gidansa kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ba. Da ya ke jawabi ga magoya baya a Abuja, jim kadan bayan yanke hukuncin Kotun Koli da ta tabbatar masa da zabensa, Gwamna Yusuf ya nuna godiya ga Kwankwaso bisa kwazonsa na ganin cewa ba a zalunci al’ummar Kano ba. A cewar Gwamna Yusuf, “mu na godiya ga Allah da wannan gagarumar nasara da ya ba mu. Mu na kuma godiya ga jagoranmu, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa…
Read More
 Alhaji Ƙarami da ASUSS sun jagoranci ƙaddamar da littafin tarihin Fadar Bege da Hafiz Abdallah

 Alhaji Ƙarami da ASUSS sun jagoranci ƙaddamar da littafin tarihin Fadar Bege da Hafiz Abdallah

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Alhaji Ƙarami Isyaka Rabiu da ASUSS sun jagoranci kaddamar da littafin tarihin shahararrun sha’iri na Manzon Allah da sahabban sa da Ahalinsa wato Marigayi Abdulaziz Fadar Bege bayan rasuwar fadar bege shekaru 10 da suka wuce. Littafan biyu wanda fitaccen marubuci Malam Bilyaminu Abul-warakat Ayagi, wanda ya rubuta litattafai sama da 100 wanda kuma shi  ne ya rubuta litafin tarihin Marigayi Fadar Bege da kuma na sha’irin mawakin Manzon Allah wato Ambasada Dakta Hafizu Abdullah wanda Alhaji Karami Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu ya kaddamar da sayen litattafan hudu akan Naira miliyan biyu domin qarfafa gwiwa…
Read More
Wike ya ɗora alhakin yajin aikin malaman Abuja kan shugabannin ƙananan hukumomi

Wike ya ɗora alhakin yajin aikin malaman Abuja kan shugabannin ƙananan hukumomi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya zargi shugabannin kananan hukumomin shida da laifin yajin aikin da malaman makarantun firamare ke cigaba da yi a yankin. Wike, wanda ya yi wa ’yan jarida jawabi a ranar Talata a Abuja jim kadan kafin wani taron gaggawa da hukumomin tsaro, ya ce jami’an kananan hukumomin ba su cika aikin da aka dora musu ba. A ranar Lahadin da ta gabata ne Kungiyar Malamai ta babban birnin tarayya Abuja ta umurci malaman firamare da su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar 15 ga watan Janairu. Yajin aikin…
Read More
Ɗan APC da ɗan PDP Ɗanjuma da Ɗanjummai ne – Sule Lamiɗo

Ɗan APC da ɗan PDP Ɗanjuma da Ɗanjummai ne – Sule Lamiɗo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a Jam'iyyar PDP ya ce zargin da tsohon shugaban rikon kwarya na jam'iyyar APC Chief Bisi Akande ya yi cewa idan PDP ta dawo mulki 'yan Nijeriya za su sake shiga qunci ba gaskiya ba ne. Alhaji Sule Lamido ya ce duk dan APCn da yake ganin PDP ce ta lalata Nijeriya to da shi a ciki, kasancewar shi ma asali dan PDP ne. Sule Lamido ya ce ya yi mamakin kalaman Bisi Akande kan cewa PDP musiba ce, annobar bala'i ce azaba ce, amma duk da hakan…
Read More
Aminin Pantami ya ba da tallafin N50m don kuɓutar da ‘yan matan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Abuja

Aminin Pantami ya ba da tallafin N50m don kuɓutar da ‘yan matan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Abuja

Daga BASHIR ISAH Tsohon Minista kuma fitaccen malamin Islama, Farfesa Isa Pantami, ya sanar cewa an tara kudi Nairia miliyan 50 domin ceto da ‘yan matan zuri’ar Al-Kadriyar da ‘yan binbdiga suka yi garkuwa da su a yankin Abuja. Pantami ya ce wani amininsa ne ya ba da tallafin ragowar Naira miliyan 50 daga cikin miliyan 60 da ‘yan bindigar suka bukaci a biya, bayan da ya tattauna batun da shi. A cewar tsohon ministan, “Alhamdu lil Laah! A kashin kaina ba na goyon bayan biyan kudin fansa ga barayi. Amma tun da a bayyane yake mun rasa ‘yarmu Nabeeha…
Read More