09
Jul
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya sa hannu a kan umarnin shugaba guda huɗu, da nufin rage wasu nau'o'in haraje-haraje ga al'ummar ƙasar. Ɗaya daga cikin umarnin shugaban ƙasar shi ne dakatar da harajin kashi biyar a kan ayyukan wayoyin sadarwa da kuma dakatar da harajin da aka tsawwala a kan kayan da ake sarrafawa a cikin gida. Mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan ayyuka na musamman da al'amuran sadarwa, Dele Alake ya faɗa ranar Alhamis cewa shugaban ƙasar ya kuma sa hannu a kan Dokar Kuɗi ta 2023, wadda a yanzu ta jingine…