Labarai

AEDC, Kaduna DisCo sun zabtare farashin wutar lantarki

AEDC, Kaduna DisCo sun zabtare farashin wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH Kamfanin raba lantarki na Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) ya ba da sanarwar rage farashin wutar lantarkin da yake raba wa kostomominsa na runukunin Band A daga N225/kWh zuwa N206.80/kWh. A ranar Litinin AEDC ya bayyana haka saƙon dabya wallafa a shafinsa na X. Sanarwar ta ce, “Muna farin cikin danar da rage farashin wuta ga kostomominmu na Band A, an yi ragin ne daga N225/kWh zuwa N206.80/kWh wanda ya fara aiki daga yau, 6 ga Mayu, 2024." Kamfanin ya kuma bai wa abokan mu'amalarsa na Band A ɗin tabbacin samun wutar lantarki na sa'o'i 20 zuwa…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Kaduna

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga a Jihar Kaduna sun kashe mutum shida a wani hari da suka kai ƙauyen Ambe da ke yankin Ƙaramar Hukumar Sanga a jihar a ranar Lahadi da daddare. Mai magana da yawun Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, Mansir Hassan, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan, tare da cewa an kama mutum guda da ake zargi da hannu a harin. A cewar Hassan, bayan da 'yan sandan yankin da rudunan Operation Safe Haven, daga suka tinkari mahara inda aka suka yi musayar wuta wanda a ƙarshe aka samu nasarar damƙe guda daga 'yan bindigar sannan…
Read More
Fashin daji ya zama ‘harkar kasuwanci’ ga wasu jami’an tsaro da na gwamnati — Gwamnan Katsina

Fashin daji ya zama ‘harkar kasuwanci’ ga wasu jami’an tsaro da na gwamnati — Gwamnan Katsina

Daga BASHIR ISAH Gwamman Jihar Katsina, Dikko Radda, ya yi zargin akwai jami'an tsaro da na gwamnati da ke taimaka wa 'yan fashin daji wanda a yanzu hakan ya za zama tamkar ''harkar kasuwanci'' a gare su. Dikko ya bayana haka ne a hirar da tashar Channels Television ta yi da shi a ranar Juma'a. Ya ce, "Yanzu lamarin ya zama sana'a. Harkar kasuwanci ta masu aikata manyan laifuka, wanda ake samun hannun wasu ma'aikatan gwamnati da jami'an tsaro a ciki. "Wannan na daga cikin tarin dalilin dalilan suka sa har yanzu aka kasa ganin bayan ayyukan 'yan fashin daji."…
Read More
IKEDC ya rage farashin wutar lantarki

IKEDC ya rage farashin wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH Kamfanin Ikeja Electricity Distribution Company ya rage wa kostomominsa na rukunin Band A kuɗin wuta da za su biya zuwa N206.80 kan kowane kilowat a sa'a guda maimakon N225 da hukumar kula da lantarki, NERC a taƙaice ta amince da shi. Mai magana da yawun IKEDC, Olufadeke Omo-Omorodion, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin. Sanarwar ta ƙara da cewa, ragin kuɗin wutar zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 6 ga Mayu, 2024. Haka nan, ta ce a maimakon N225/Kwh da kostomominsu na Band A su biya bisa la'akari da…
Read More
Ƙarancin ruwa na jikkata majinyata a asibitin Dutse

Ƙarancin ruwa na jikkata majinyata a asibitin Dutse

*Gwamnatin Jigawa ta samar da inji – Shugaban asibitin Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Ƙarancin ruwan sha ya addabi babban asibitin kwanciya na Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa, wato Dutse General Hospital, lamarin da ya sa marasa lafiya da masu zaman jiyya yin gararambar neman ruwan sha a unguwannin Maranjuwa, Fagoji Bakwato da bakin kasuwar ’yan Tifa da ke birnin na Dutse. Kamar yadda binciken Wakilin Blueprint Manhaja ya nuna, ta kai ta kawo marasa lafiya da masu zaman jiyya sun koma yin alwala da ruwan leda da ake kira da ‘pure water’ na Naira 20 ƙwaya ɗaya da…
Read More
Gwamna Zulum ya samu nasarorin bunƙasa rayuwar al’ummarsa – Hon. Ayuba

Gwamna Zulum ya samu nasarorin bunƙasa rayuwar al’ummarsa – Hon. Ayuba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar Borno, Hon. Bello Ayuba ya lissafo wasu nasarorin da mai girma gwamnan jihar Farfesa Baba Gana Umara Zulum ya samu, inda ya bayyana gwamnan a matsayin mutum mai kishin al'umma da jiharsa. Hon Bello Ayuba ya ce Gwamna Babagana Umara Zulum ya samu ɗumbin nasarori musamman  a fannin inganta rayuwar bil'adama da sauransu. Shugaban Jam'iyyar APCn ya ce Gwamna Zulum ya bunƙasa ababen more rayuwa da shirye-shiryen da suka shafi jama'a kaitsaye kamar gina gidaje, gina manyan tituna a cikin gari da ƙauyaku a ƙananan hukumomi 27 da gina…
Read More
Shin za a tsagaita wuta bayan kashe sama da Gazawa 34,000?

Shin za a tsagaita wuta bayan kashe sama da Gazawa 34,000?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Tambayar sanin yiwuwar tsagaita buɗe wuta da Isra'ila ke yi a Gaza na da muhimmanci don yadda a ke ta yunƙurin yiwuwar hakan amma sai a ke ta fuskantar cikas. Ba mamaki rashin niyyar Isra'ila ta dakatar da yaqin gabanin kashe duk 'yan Hamas ke kawo kwan gaba kwan baya. Tun mayar da martanin Isra'ila a sanadiyyar kutsawar mayaƙan Hamas cikin Isra'ila ranar 7 ga Oktobar bara a ke ta samun labaru masu ban takaici na yanda hare-haren Isra'ila ke yawan kashe mata da ƙananan yara. Ko yanzu ai Isra'ila ta wuce ramuwar gaiya ga…
Read More
Masu zanga-zanga sun buƙaci a sake buɗe tuhumar N70bn da ake yi wa Matawalle

Masu zanga-zanga sun buƙaci a sake buɗe tuhumar N70bn da ake yi wa Matawalle

Daga BASHIR ISAH Wasu masu zanga-zanga da suka mamaye harabar ofishin hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC da ke Abuja, sun buƙaci a sake buɗe ƙarar zargin da ake yi wa tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, na karkatar da kuɗaɗen jihar zuwa aljihunsa. A ranar Juma'ar da ta gabata aka ga masu zanga-zangar ɗauke da alluna da kwalaye masu ɗauke da saƙonnin buƙatar EFCC ta sake buɗe kes din badaƙalar almundahana a kan Matawalle. Masu zanga-zangar sun nuna rashin gamsuwarsu kan yadda EFCC ke tafiyar da batun Matawalle, inda suka buƙaci hukumar ta ƙara himma sannan ta tabbatar da…
Read More
An gano kaburbura ɗauke da ɗaruruwan gawarwaki a Gaza – Ofishin Jakadancin Falastinu

An gano kaburbura ɗauke da ɗaruruwan gawarwaki a Gaza – Ofishin Jakadancin Falastinu

Daga MAHDI M. MUH’D Ofishin Jakadancin Falastinu a Nijeriya ya bayyana cewa a rana ta 209 na ƙazamin yaƙin kisan ƙare dangi da ake yi wa al'ummar Palastinu, an gano kaburbura masu yawa a zirin Gaza. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da Jakadan Falastinu a Nijeriya, Abdullah Shawesh ya fitar ga manema labarai a Alhamis. Sanarwar ta ce, "yaƙin ya bar kimanin tan miliyan 37 na tarkacen bama-bamai da suka fashe. An yi hasashen cewa za a ɗauki shekaru 14 kafin a kwashe ɓaraguzan da suak fashe ɗin. "Ya zuwa ranar 1 ga watan Mayu, adadin shahidan…
Read More
’Yan ƙwadago sun buƙaci soke ƙarin kuɗin lantarki

’Yan ƙwadago sun buƙaci soke ƙarin kuɗin lantarki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na Nijeriya, Joe Ajaero da Festus Osifo, yayin da su ke gabatar da jawabi na haɗin gwiwa a bikin ranar ma'aikata a Abuja, a ranar Laraba, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya da soke ƙarin kuɗin wutar lantarki tare da sausauta duk wani nau'i na haraji ga al'umma. A cikin buƙatu guda 18 da shugabannin ƙwadagon suka gabatar, sun ce ya kamata a sake duba aikin sayar da wutar lantarki a ƙasar don kar da a samu koma baya. Bugu da ƙari, suna son gwamnati ta gaggauta fitar da motocin bas ɗin CNG a faɗin…
Read More