Labarai

KNEP da AFAN za su tallafa wa manona da takin a Jigawa

KNEP da AFAN za su tallafa wa manona da takin a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Ƙungiyar manoma a Jihar Jigawa mai Suna Kenap ƙarƙashin jagorancin Alh Nura Ahmed Sale, ta ce za su haɗin gwiwa da ƙungiyar AFAN wajen samar wa anoma taki mai inganci cikin sauki a Jihar jigawa . Sale ya buƙaci haɗin kan ƙungiyar Afan ne saboda karfinta da kuma yadda take taimakon manoma a Nijeriya. Ya ce haɗinkansu ya zama dole domin saida haɗakai ne za su iya cimma burinsu na nuna wa manoma yadda ake amfani da wannan takin mai cokali. Ya ce takin na da inganci fiye da buhun takin zamani mai nauyin…
Read More
Tudun Biri: Sojoji 12 sun gurfana gaban kotunsu bayan kammala bincike

Tudun Biri: Sojoji 12 sun gurfana gaban kotunsu bayan kammala bincike

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar Sojojin Nijeriya ta bayyana cewa, ta kammala binciken da aka daɗe ana dakon sakamakonsa kan bom ɗin da aka jefa bisa kuskure kan mutanen ƙauyen Tudun Biri a Ƙaramar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna. Ta kuma ce, sojojin da aka samu da laifi a kai harin, za su gurfana a gaban kotun soji, domin fuskantar hukunci. Daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron Nijeriya, Edward Buba, ne ya bayyana haka a taron manema labaran da aka gudanar a Abuja. A Disambar bara ne wani jirgin sojoji ya jefa bom kan mutanen da ke bikin Maulidi,…
Read More
Kotu ta tsare fasto kan aikata fyaɗe

Kotu ta tsare fasto kan aikata fyaɗe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata kotun majistare ta tsare wani limamin coci a gidan yari kan laifin yi wa wata matashiya mai shekaru 22 fyaɗe. Babbar Kotun Majistare da ke Badagry a Jihar Legas ta tisa ƙeyar Fasto Sunday Adewoye zuwa gidan yarin ne a ranar Talaa bayan an gurfanar da shi. Ɗan sanda mai gabatar da ƙarar, Insfekta Ayodele Adeosun, ya shaida wa alqali cewa a ranar 17 ga Afrilu, 2024 ne Fasto Adewoye ya zakke wa matar da ƙarfin tsiya a garin na Badagry. Hakan a cewarsa laifi ne a ƙarƙashin dokar hukunta manyan laifuka ta…
Read More
Iyalai da almajiran Malam Mai Siddi sun yi addu’ar cika shekara 32 da rasuwarsa a Gombe

Iyalai da almajiran Malam Mai Siddi sun yi addu’ar cika shekara 32 da rasuwarsa a Gombe

Ya bada gudunmawa wajen haɗa kan al’umma ta vangaren karatun Ishiriniya Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe A ranar Juma’ar da ta gabata ne 26 ga watan Afrilu 2024 iyalai da almajiran Sheikh Abubakar Siddi Bolari (Mai Ishiriniya) suka gabatar da addu’o'i na musamman don cika shekara 32 da rasuwarsa. Shi dai Sheikh Malam Abubakar Siddi Mai Ishiriniya Malamin addinin Musulunci ne da ya bada gudunmawa sosai wajen ciyar da addinin Islama gaba, a tsawon rayuwarsa wanda ya bar giɓi mai wuyar cikewa. Tarihin rayuwarsaSheikh Abubakar ɗa ne ga ɗan Abdullahi ɗan Salihu wanda yake jinin sharifai ne da ke…
Read More
Kotu ta haramta wa NERC aiwatar da ƙarin kuɗin wutar lantarkin

Kotu ta haramta wa NERC aiwatar da ƙarin kuɗin wutar lantarkin

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Kano ta ba bai wa Hukumar Kula da Wutar (NERC) da kamfani Kano Electricity Distribution Company (KEDCO) kan kada su aiwatar da ƙarin kuɗin wutar lantarkin da aka yi ga masu amfani da wutar lantarki na Band A. Kwanankin bayana ne NERC ta umarci kamfanonin rarraba wutar lantarki da su ƙara kuɗin wutar da suke bai wa kostomominsu na rukunin Band A domin samun wadatar wutar lantarki. Sai da daman 'yan Nijeriya sun soki matakin na NERC musamman yadda hukumar ta ɗora da yawan kostomomin nata a tsarin Band A duk…
Read More
Hisbah ta bai wa ‘yan jarida da lauyoyi gurbi a shirin auren zawarawa

Hisbah ta bai wa ‘yan jarida da lauyoyi gurbi a shirin auren zawarawa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Hukumar Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa, ya sanar da bai wa 'yan jarida gurbi guda 50 a shirin auren zawarawan da hukumar za ta yi nan gaba. Daurawa ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da manema labarai ranar Laraba a Kano. Ya ce, sako 'yan jarida da sauransu a cikin shiri, zai taimaka wajen daɗa bunƙasa shi. Daurawa ya ƙara da cewa, shirinta na gaba zai haɗa har da lauyoyi da ma'aikatan kiwon lafiya da sauransu. Wannan na zuwa ne bayan da hukumar ta samu nasarar ƙulla aure 1,800 a…
Read More
Sarkin Kano ya buƙaci a dawo da Makarantar Sojojin Sama ta Kano

Sarkin Kano ya buƙaci a dawo da Makarantar Sojojin Sama ta Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mai Martaba Sarkin Kano, Alh Aminu Ado Bayaro, ya yi kira ga Shugaban sojojin sama na Nijeriya kan ya yi ƙoƙari wajen dawo da Makarantar Sojojin sama da ke garin Kwa a yanki Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa wadda aka rufe sakamakon rashin tsaro a watannin baya. Basaraken ya yi wannan kira ne lolacin da Shugaban Sojojin Sama na Nijeriya, Hassan Bala Abubakar, ya ziyarce shi a fadarsa a ranar Alhamis. Ta cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na Masarautar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Na'isa, ya tura wa Blueprint Manhaja ya ce, Sarkin ya ƙara…
Read More
Ranar Ma’aikata: Ƙarin albashi da kashi 35 ɓata lokaci ne — NLC

Ranar Ma’aikata: Ƙarin albashi da kashi 35 ɓata lokaci ne — NLC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi watsi da ƙarin albashin da Gwamnatin Tarayya ta yi musu a matsayin “vata lokaci.” Manhaja ta ruwaito a daren Talata cewa gwamnatin ta yi wa ma’aikatanta ƙarin kashi 25 zuwa 35 na albashinsu; ’yan fansho kuma kashi 20 zuwa kashi 28. Sanarwar da mai magana da yawun hukumar kula da albashi ta ƙasa (NSIWC), Emmanuel Njoku, ya fitar ta duk ƙarin za su fara aiki ne daga watan Janairun 2024. Njoku ya kuma shaida wa Manhaja cewa za a biya ma’aikatan cikon ƙarin albashin na watannin da…
Read More
Man United ta fi nuna ƙwarewarta a Firimiya – Ten Hag

Man United ta fi nuna ƙwarewarta a Firimiya – Ten Hag

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Erik ten Hag ya bayyama cewa Manchester United ɗaya ce daga cikin ƙungiyoyin da ta fi nuna bajinta a gasar Firimiya ta bana. Kocin ya faɗi hakan duk da ƙungiyar Old Trafford na fama da kalubalen cin wasa ko dai a gida ko a waje a kakar nan. Ranar Asabar United ta tashi 1-1 da Burnley a firimiya, wadda take ta biyun ƙarshe, inda mai tsaron raga, Andre Onana ya yi kuskuren da aka farke a bugun fenariti ta hannun Zeki Amdouni. Hakan na nufin Ten Hag ya samu nasarar wasa daya a cikin minti 90…
Read More
Tinubu ya taya Idris murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Tinubu ya taya Idris murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya taya Ministan Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa, Mohammed Idris, murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Laraba. Sanarwar ta ce, Ministan hadimin gwamnati ne wanda ya zo a daidai lokacin da ake buƙatarsa. Ta ƙara da cewa, Ministan wanda mawallafi ne kuma ɗan siyasa, yana aiki da ƙwarewa a matsayinsa na Ministan Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa. Haka nan, ta ce Idris na daga cikin 'yan sahun gaba a fagen yaɗa labarai…
Read More