Labarai

Ranar Ma’aikata: Gwamnan Zamfara ya jaddada ƙudurinsa na kyautata rayuwar ma’aikatan jihar

Ranar Ma’aikata: Gwamnan Zamfara ya jaddada ƙudurinsa na kyautata rayuwar ma’aikatan jihar

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na kyautata wa rayuwar ma'aikatan jihar. Ya bayyana haka ne a wajen taron bikin Ranar Ma'aikata na bana wanda aka saba gudunarwa ran 1 ga Mayun kowace shekara. Bikin bana a jihar ya gudana ne a ranar Laraba a Sakatariyar JB Yakubu, Gusau, babban birnin jihar. Cikin sanarwar da ta fitar, Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya ce gwamnatin jihar ba za ta baro ma'aikatan jihar a baya wajen gudanar da harkokinta. Sulaiman ya rawaito Lawal na cewa, “Gwamnatina na sane da muhimmiyar rawar da ma'aikata ke…
Read More
1 ga Mayu sabon albashi mafi ƙaranci zai fara aiki – Gwamnati

1 ga Mayu sabon albashi mafi ƙaranci zai fara aiki – Gwamnati

*Ba mu amince da ƙarin albashin kashi 35 ba — NLC Daga BSHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta ba da tabbacin cewa sabon albashi mafi ƙaranci zai fara aiki daga 1 ga Mayu. Kodayake, Gwamnatin ta ce kwamitin da ke da ruwa da tsaki kan batin ƙarin albashin bai kammala aikinsa ba tukuna. Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha, ita ce ta yi wannan babayin a wajen taron bikin Ranar Ma'aikata da aka shirya ranar Laraba a Abuja. Ta ce abin takaici ne ƙarin albashin bai kammalu ba zuwa wannan lokaci, amma cewa ana ci gaba da tattaunawa domin tabbatar dukkanin bayanai…
Read More
Ranar Ma’aikata: Gwamnati ta ayyana 1 ga Mayu, ranar hutu ga ma’aikata

Ranar Ma’aikata: Gwamnati ta ayyana 1 ga Mayu, ranar hutu ga ma’aikata

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga watan Mayu, a matsayin ranar hutun gama-gari albarkacin Bikin Ranar Ma'aikata na bana. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Babban Sakataren Ma'aikatar Cikin Gida, Dr Aishetu Ndayako, ta fitar ranar Talata a Abuja. Aishetu ta ce, Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo ne ya ayyana ranar hutun a madadin Gwamnatin Tarayya. Tunji-Ojo ya jaddada buƙatar aiki da ƙwazo a ɗaukacin ɓangarorin ƙwadago, kana ya ƙara haskaka ƙudurin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin samar da walwala ha ma'aika da kuma son ganin ma'aikata sun zamo masu…
Read More
Za mu gurgunta samar da fetur muddin ba a biya mu bashin N200bn ba — IPMAN

Za mu gurgunta samar da fetur muddin ba a biya mu bashin N200bn ba — IPMAN

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Masu Dakon Fetur ta Nijeriya (IPMAN), ta yi barazanar gurgunta samar da fetur afaɗin ƙasa muddin ba a biya ta bashin Naira biliyan 200 da take bi ba. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙarancin fetur ke ci gaba da ta'azzara lamarin da ya yi sanadiyar ƙarin farashin fetur a sassan ƙasa, inda a yanzu ake sayar da fetur tsakanin N610 da N800 kan lita guda a wasu wurare, sannan N1000 zuwa N1200 a kasuwar bayan fage. Jigo a IPMAN, Mazi Oliver Okolo ne ya yi wannan barazanar, kuma cewa da goyon bayan shugabancin…
Read More
Emefiele ba ya bayar da kwangila sai da cin hanci, in ji shaida

Emefiele ba ya bayar da kwangila sai da cin hanci, in ji shaida

Daga BASHIR ISAH Mutum na biyu da ke ba da shaida a kan shari'ar da tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ke fuskanta, ya bayyana wa Kotu ƙarara cewa lallai Emefiele ba ya ba da kwangila ba tare da ya karɓi cin hanci ba. John Ayo wanda ya kasance tsohon Darakta na Sashen Labarai na CBN, ya bayyana haka ne ga Babban Kotun da ke zamanta a Ikeja, Jihar Legas. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake ba da shaida a gaban Alƙali Rahman Oshodi yayin zaman da kotun ta yi a ranar Litinin. Emefiele na fuskantar shari'a ne kan…
Read More
An gano gawar budurwar da aka sanar da ɓacewarta a Abuja

An gano gawar budurwar da aka sanar da ɓacewarta a Abuja

Daga BASHIR ISAH An gano gawar Murjanatu Zubaiaru bayan da 'yan uwanta suka ba da sanarwar ɓacewarta a Abuja. Kafin mutuwarta, Murjanatu ɗaliba ce 'yar aji huɗu a Jami'ar Abuja. A cewar kawun marigayiyar, Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti kuma tsohon Mataimakin Shugaban Hukumar Kwali, a ranar Juma'ar da ta gabata Murjanatu ta bar gida zuwa makaranta amma ba a ga dawowarta ba, kuma wayarta ba ta shiga. Ya ce, "Iyayenta sun tuntuɓe ni kan ko na ga Murjanatu alhali ba ta zo gidana ba kamar yadda aka yi zato. Duk ƙoƙarin da muka yi don ji daga gare ta waya,…
Read More
Yanzu-yanzu: JAMB ta saki sakamakon UTME na 2024

Yanzu-yanzu: JAMB ta saki sakamakon UTME na 2024

Daga BASHIR ISAH Hukumar Shirya Jarrabawar Neman Gurbin Karatu a Manyan Makarantu (JAMB), ta saki sakamakon jarrabawar da ta shirya ta 2024. Shugaban JAMB, Fargesa Ishaq Oloyede ne ya sanar da hakan ga manema labarai alran Litinin a hedikwarar hukumar da ke yankin Bwari, Abuja.
Read More
Kamfanonin waya sun nemi Tinubu ya ba su haɗin kai don tsauwala farashi

Kamfanonin waya sun nemi Tinubu ya ba su haɗin kai don tsauwala farashi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kamfanonin manyan layikan sadarwar da su ke aiki a Nijeriya, wato Glo, MTN, Airtel da 9Mobile, sun roƙi Gwamnatin Tarayya a karƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta sassauta wasu ƙa'idojin da ta saka wa kamfanonin, don ba su damar ƙara tsauwala farashin kuɗin kiran waya da na data. A cewar kamfanonin, tsarin kula da farashin na yanzu bai dace da yanayin matsin tattalin arziki ba, don haka suke neman taimakon gwamnati, don magance ƙalubalen farashin. Kamfanonin sadarwa guda huɗu sun ce, su kaɗai ne ba su yi ƙari kan farashinsu ba, wanda hakan ke…
Read More
Don kare Nijeriya daga faɗawa fatara ya sa na cire tallafin fetur — Tinubu

Don kare Nijeriya daga faɗawa fatara ya sa na cire tallafin fetur — Tinubu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya jaddada cewa matakin cire tallafin fetur da gwamnatinsa ta ɗauka abu ne da ya zama wajibi don hana ƙasar faɗawa cikin fatara. Tinubu ya bayyana haka a ne sa'ilin da yake jawabi a wajen taron tattalin arzikin duniya da ke gudana a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya a ranar Lahadi. Ya ce akwai buƙatar cire tallafin na fetur domin sake farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar. Ta bakinsa, “Ga Nijeriya, mun yi amannar haɗin gwiwar tattalin arziki da haɗa kai ya zama dole don samar da kwanciyar hankali a sauran ƙasashen duniya. "Game…
Read More