Labarai

An buƙaci Tinubu ya ja kunnen EFCC kan yi wa doka karan-tsaye

An buƙaci Tinubu ya ja kunnen EFCC kan yi wa doka karan-tsaye

Daga BASHIR ISAH An yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan ya ja kunnen Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) bisa karan-tsayen da take yi wa doka wajen gudanar da harkokinta. An buƙaci Tinubu ya taka wa EFCCn burki ne bayan da ta yi yunƙuri cafke tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, duk da cewa a baya umarnin kotu ta haramta mata hakan. Idan za a iya tunawa, a ranar 9 ga Fabrairu, 2024, Babbar Kotun da ke zamanta a Lokoja, ta yanke hukunci kan ƙara mai lamba HCL/68M/2024 tsakanin Alhaji Yahaya Bello da EFCC, inda ta…
Read More
Mun inganta tsarin shugabanci a Zamfara — Lawal

Mun inganta tsarin shugabanci a Zamfara — Lawal

Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa ta inganta tsarin shugabancin Jihar Zamfara da zummar bunƙasa jihar yadda ya kamata. Lawal ya bayyana haka ne yayin taron majalisar zartarwar jihar wanda ya jagoranta ranar Litinin a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Gusau, babban birnin jihar. Kakakin Gwmanan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar cewa, Gwamnan ya tunatar da mambobin majalisar ƙudurorin da gwamnatinsa ta sanya a gaba don cigaban jihar. Sanarwar ta ƙara da cewa, taron ya tattauna kan muhimman batutuwa bayan da Gwamnan ya gabatar jawabin maraba. Sanarwar ta rawaito…
Read More
Da Ɗumi-ɗuminsa: Kotu ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Ganduje daga APC

Da Ɗumi-ɗuminsa: Kotu ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Ganduje daga APC

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Babbar Kotun Jihar Kano mai Lamba 4 dake zaman ta a kan titin Mila, ta tabbatar da dakatarwar da wasu shugabannin Jam'iyyar APC a Mazaɓar Ganduje suka yi wa Shugaban Jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje daga jam'iyyar. Alƙalin Kotun, Justice Usman Malam Na'abba ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata takardar da masu ƙara suka nema, ba tare da sanar wa ɓangaren waɗanda suke ƙara ba wato (Motion Ex parte). Haladu Gwanjo da Laminu Sani ne suka shigar da ƙarar, inda suka yi ƙarar ɓangarori huɗu waɗanda suka haɗar da Jam'iyyar APC, Kwamitin…
Read More
Majalisar Dokokin Kaduna ta kama hanyar binciken gwamnatin El-Rufai

Majalisar Dokokin Kaduna ta kama hanyar binciken gwamnatin El-Rufai

Daga BASHIR ISAH Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta kafa kwamiti na musamman domin binciken yadda gwamnatin Nasiru El-Rufai ta gudanar da hada-hadar kuɗi a wancan lokaci. Kwamitin zai binciki yadda tsohuwar gwamnatin ta ciyo bashi da bayar da kwangila da dai sauransu. Yayin wani taron jin ra'ayiyin jama'ar gari da aka shirya a ranar Asabar da ta gabata, an jiwo Gwamna Uba Sani na ƙorafi kan tarin basussukan da ya gada daga gwamnatin El-Rufai tun daga 29 ga Mayun 2023. Gwamnan ya ce abin da ya zo ya tarar bai taka kara ya karya ba don kuwa ko albashin ma'aikata…
Read More
Almundahana: Ana zargin Ganduje da karkatar da N51bn mallakar ƙananan hukumomi

Almundahana: Ana zargin Ganduje da karkatar da N51bn mallakar ƙananan hukumomi

Daga BASHIR ISAH Hukumar Yaƙi da Rashawa da Sauraren Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Kano, ta shigar da sabuwar ƙara kan tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, inda take zarginsa da karkatar da maƙuden kuɗi Naira Biliyan 51.3 mallakar ƙananan hukumomin jihar. Shugaban Hukumar, Muhuyi Magaji ne ya bayyana haka a cikin wani shirin da tashar Channels Television ta yi da shi a ranar Talata. A cewar Magaji, bincike ya gano wasu kuɗaɗe mallakar ƙananan hukumomi har biliyan N51.3 wanda aka karkatar da su zuwa asusun ajiyar wasu ɗaiɗaikun mutane ba a bisa ƙa'ida ba a…
Read More
Soja ya faɗa komar ‘yan sanda kan daɓa wa ɗan acaɓa wuƙa a mashaya

Soja ya faɗa komar ‘yan sanda kan daɓa wa ɗan acaɓa wuƙa a mashaya

Daga BASHIR ISAH Rundunar 'Yan Sanda a Jihar Legas ta tabbatar da tsare wani sojan Nijeriya bisa zargin daɓa wa wani ɗan acaɓa a wuƙa a mashaya. Rundunar ta ce sojan na aiki ne tare da 159 Battalion da ke Yobe, kuma ya luma wa ɗan acaɓan wuƙar ce a ciki. Kakakin 'yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da tsare sojan a ranar Litinin. Inda ya ce an kama sojan ne da misalin ƙarfe 3:00 na asubahin Asabar a yankin Ikorodu da ke Legas. Hundeyin ya ce lamarin ya auku ne sakamakon saɓanin da ya shiga…
Read More
NDLEA ta damƙe masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi 51,000, ta gurfanar da 9000 a cikin shekara uku

NDLEA ta damƙe masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi 51,000, ta gurfanar da 9000 a cikin shekara uku

Daga BASHIR ISAH Hukumar Yaƙi da Sha da Safarar Miyagun ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), ta ce a tsakanin shekaru uku da suka gabata, ta samu nasarar damƙe masu ta'ammali da miyaƙun ƙwayoyi mutum 50,901 kana ta gurfanar da 9000. Shugaban Hukumar na Ƙasa, Buba Marwa ne ya bayyana hakan a wajen bikin ƙaddamarwa da kuma miƙa ginin da Gwamnatin Birtaniya ta bai wa hukumar a matsayin gudunma wanda aka gudanar a ranar Litinin. Sanarwar da mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi ya fitar, ta rawaito Marwa na cewa, daga cikin mutum 50,901 da aka kama bisa zargin ta'ammali da…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe Sakataren PDP a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe Sakataren PDP a Zamfara

Daga BASHIR ISAH Wasu 'yan bindiga da ake zargin ɓarayin daji ne a Jihar Zamfara, sun kashe Sakataren Jam'iyyar PDP na Ƙaramar Hukumar Tsafe a jihar, Musa Ille. Majiyarmu ta ce an kashe marigayin ne a ƙofar gidansa bayan da da 'yan bindigar suka yi wa gidan ƙawanya a ranar Litinin da daddare. Shugaban PDP na yankin, Garba Garewa, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai a ranar Talata. Ya ce, “Muna zargin makisan 'yan fashin daji ne, jiya (Litinin) suka shiga gidansa suka halbe shi." Wani mazaunin yankin, Abubakar Tsafe, ya shaida wa jaridar News Point…
Read More
Shugabancin APC na Jihar Kano ya dakatar da waɗanda suka dakatar da Ganduje a matakin Gunduma

Shugabancin APC na Jihar Kano ya dakatar da waɗanda suka dakatar da Ganduje a matakin Gunduma

Daga BASHIR ISAH Kwamitin Gudanarwa na Jam'iyyar APC na Jihar Kano, ya saka wa shugabannin jam'iyyar na gundumar Ganduje c'da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa takunkumi bisa dakatar da Shugaban APC na Ƙasa Umar Abdullahi Ganduje, da suka yi a ranar Litinin. Shugabancin APC na ƙaramar hukumar ya daƙile matakin dakatarwar da aka yi wa Gandujen ne tare da sauke waɗanda ke da hannu a korar daga muƙamansu. Shugaban APC na Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, Inusa Dawanau, ya shaida wa manema labarai cewa, an samu waɗanda suka dakatar da Ganduje da yi jam'iyya zagon ƙasa, tare da cewa an samu…
Read More
Raɗɗa ya raba wa jami’an tsaro motocin aiki a Katsina

Raɗɗa ya raba wa jami’an tsaro motocin aiki a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, ya miƙa wa jami’an tsaro motocin yaƙi masu sulke guda 10 domin gudanar da aiki a ƙananan hukumomi takwas dake fama da matsalar rashin tsaro a jihar Katsina don ƙarfafa tsaron al'uma. Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da motocin ne don inganta tsaron jihar wanda sojoji da 'yan sanda da kuma jami'an tsaron da gwamnatin jihar ta kafa ke jagoranta a ƙananan hukumonin da matsalar ta fi ta'azzara. Taron miƙa motocin ya gudana ne ranar Talata a gidan gwamnatin jihar. A jawabinsa, Gwamnan ya nanata cewa zai ci gaba da…
Read More