19
Apr
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar EFCC ta bayyana cewa har yau ba ta wanke ko da mutum ɗaya da ake zargin handama, harƙalla da karkatar da kuɗaɗen Ma’aikatar Ayyukan Jinqai da Inganta Rayuwar Marasa Galihu ba. EFCC ta kara da cewa, “har yanzu dai ana ci gaba da bincike, kuma sai ƙarin haske ake samu. Saboda haka muna kira ga jama’a su yi watsi da duk wasu surutai da ba su ji daga bakin EFCC ɗin ba.” Haka sanarwar ta ƙunsa, wadda aka fitar da ita a ranar Asabar, mai ɗauke da sa hannun Kakakin EFCC, Dele Oyewale…
