Labarai

Akwai masu zuga ni na binciki Gwamna Abba – Muhuyi Magaji

Akwai masu zuga ni na binciki Gwamna Abba – Muhuyi Magaji

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Malam Muhuyi Magaji, ya ce wasu mutane na bincikensa domin ƙoƙarin tunzura shi ya binciki Gwamna Abba Kabir. Magaji ya bayyana haka ne yayin da ya halarci shirin Sunrise Daily na gidan talabijin Channels ranar Talata, 16 ga watan Afrilu, 2024. Jami'in ya ce, ya fara binciken shugaban jam’iyyar APC na qasa, Dr. Abdullahi Ganduje, a lokacin da yake kan kujerar gwamnan Jihar Kano. Shugaban hukumar yaƙi da rashawar, wanda ya jaddada cewa ya zama tilas jami'an gwamnati su kiyaye bin doka da oda,…
Read More
Dalilin da ya sa na daina saka baki a siyasar Nijeriya – Rotimi Amaechi

Dalilin da ya sa na daina saka baki a siyasar Nijeriya – Rotimi Amaechi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Ministan Sufuri a Nijeriya Rotimi Amaechi ya ce an daina jin ɗuriyarsa ne a fagen siyasar Nijeriya saboda "babu wani sabon abu" da zai faɗa. Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya riƙe muƙamin minista a gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2022, bayan ya mulki jihar tasa a Kudancin Nijeriya tsawon shekara takwas. "Babu wani sabon abu kwatakwata," inji ɗan siyasar wanda ya nemi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC mai mulki cikin hira ta musamman da BBC. "Abubuwan da ake so na yi magana a kan su suna nan…
Read More
An tsinci gawar jami’in ɗan sanda a gidansa a Maiduguri

An tsinci gawar jami’in ɗan sanda a gidansa a Maiduguri

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Al'ummar Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, sun samu kansu a cikin wani yanayi yayin da aka tsinci gawar wani sifeton ’yan sandan a gidansa. Marigayi jami’in (da aka sakaya sunansa) da ke aiki a sashin Gwange na rundunar ’yan sandan jihar Borno an gansa ne kwanaki uku da suka wuce kafin a gano gawarsa a gidansa da safiyar Asabar. Maqwabtansa a Layin Bayan, unguwar Wulari Jerusalem a Maiduguri, sun ɗaga murya wajen kiransa a lokacin da suka lura ya kulle ƙofarsa ta baya, amma wani ɗoyi na fitowa daga gidan. Nan take aka kai rahoton lamarin…
Read More
Ƙaramar Sallah: Sarkin Fataskum, Umar Bubaram, ya hori masu hali kan taimako

Ƙaramar Sallah: Sarkin Fataskum, Umar Bubaram, ya hori masu hali kan taimako

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai Martaba Sarkin Fataskum, Alhaji Umar Bubaram ya hori masu hali da su ci gaba da taimakon mabuƙata duba da halin da ake ciki na tsadar rayuwa a ƙasar. Sarkin ya bayyana haka ne cikin makon da ya gabata a lokacin da yake miƙa saƙon barka da Sallah ga al'ummar Fataskum da Musulmin duniya bakiɗaya. Alhaji Umar Bubaram ya ce a halin da ake ciki yanzu na taɓarɓarewar tattalin arziki, akwai buƙatar attajirai su dinga taimakon na ƙasa "domin ɗorewar zumunci da ƙaunar juna". Haka kuma mai martaba Sarkin Alhaji Umar Bubaram Ibn Wuriwa…
Read More
Atiku da Wike sun halarci babban taron jam’iyyar PDP a Abuja

Atiku da Wike sun halarci babban taron jam’iyyar PDP a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Laraba ne ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar da ministan babban birnin tarayya, Nyesome Wike, suka halarci taron jam’iyyar PDP na ƙasa a Abuja gabanin kwamitin zartarwa na jam’iyyar na ƙasa. Wannan dai shi ne karon farko da tsohon gwamnan jihar Ribas zai halarci taron jam'iyyar PDP tun bayan zaɓen shugaban ƙasa a bara. Wike dai ya samu saɓani da shugabannin jam’iyyar PDP kuma bai goyi bayan zaɓen Abubakar da jam’iyyar ta yi ba a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaven bara. Baya ga…
Read More
Ɗan gidan El-Rufai na yi wa ‘yan Majalisar Dokokin Kaduna barazana kan binciken da ake yi wa mahaifinsa

Ɗan gidan El-Rufai na yi wa ‘yan Majalisar Dokokin Kaduna barazana kan binciken da ake yi wa mahaifinsa

Daga BASHIR ISAH Kakakin Majalisar Jihar Kaduna, Yusuf Liman, ya zargi ɗan gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Bello El-Rufai, kan tura masa rubutaccen saƙo yana yi masa baraza kan batun binciken tsohuwar gwamnatin mahaifinsa. MANHAJA ta kalato a ranar Talatar da ta bagabata Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin na musamman domin bincikar hada-hadar ƙuɗaɗe da kwangiloli da sauransu, wanda tsohuwar gwamnatin Nasir El-Rufai ta yi daga 2015 zuwa 2023. Kakain Majalisar ya gargaɗi Bello kan ya daina yi wa majalisar barazana kan batun bibciken. Liman ya ƙara da cewa, Bello ya aike masa da saƙon zagi da barazana ta…
Read More
Ƙarancin kayan aiki ya addabi makarantun Jihar Jigawa

Ƙarancin kayan aiki ya addabi makarantun Jihar Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Ƙaran cin kayan koyarwa ya addabi makarantu da malamai a Jihar Jigawa, lamarin da ya sa wasu daga cikin malaman makarantun Jihar gabatar da ƙorafin su ga manema labarai. Kaɗan daga cikin ƙorafin ya haɗa da ƙarancin alli da rijistar ɗalibai da tsarin karantawar, wato scheme of work da kuma ƙarancin littatafan karatu. A hannu guda malaman sun yi ƙorafin rashin kulawa a kansu wajan ƙarin girma da gazawar gwamnati wajen biyansu haƙƙinsu na ƙarin girma a kan lokaci. Masu ƙorafin waɗanda suka buƙaci a sakaya sunansu, sun ce ce da yawa daga cikinsu…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe basarake a Taraba

‘Yan bindiga sun kashe basarake a Taraba

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga a Jihar Taraba sun kai hari tare da kashe sarkin masarautar Sansani, Alhaji Abdulmutalib Jankada, da ke cikin Ƙaramar Hukumar Gassol a jihar. Majiyoyi sun ce maharan sun shiga ƙauyen Sensani ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 9 na dare inda suka tafi kai tsaye zuwa fadar masarautar ƙauyen sannan suka kashe Nuhu a gidansa da ke kusa da Ibbi. Majiyarmu ta ce za a yi jana'izar marigayin bayan an sauka daga Sallar Juma'a daidai da karantarwar Musulunci. Ya zuwa haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga ɓangaren hukuma kan batun.
Read More
Gwamnatin Nijeriya na biyan tallafin mai a yanzu fiye da a baya – El Rufa’i

Gwamnatin Nijeriya na biyan tallafin mai a yanzu fiye da a baya – El Rufa’i

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin Nijeriya na ci gaba da biyan tallafin mai wani abu da ya ce an Nijeriya da dama ba su sani ba. Da yake amsa tambayoyin manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, El Rufai ya ce a yanzu gwamnati na biyan fiye da abin da take biya a matsayin tallafin mai a baya. Ya bayyana cewa matakai da dama da aka tanada na rage raɗaɗin janye tallafin mai ba sa tasiri abin da a cewarsa ya sa aka maido da…
Read More
Ɗalibai 1,680 aka sace a shekaru 10 a Nijeriya — UNICEF

Ɗalibai 1,680 aka sace a shekaru 10 a Nijeriya — UNICEF

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya ce hare-hare da sace-sacen da ake kai wa 'yan makaranta a Nijeriya ya karu tun bayan sace ‘yan matan makarantar Chibok a jihar Borno shekaru 10 da suka gabata. UNICEF, a cikin wani rahoto da ta fitar a jiya Litinin, ta ce kashi 37 na makarantu a jihohi 10 ne kawai ke da tsarin gargaɗin farko na gano barazanar irin waɗannan hare-hare. Rahoton ya yi la’akari da alƙaluma masu ban tsoro na tashe-tashen hankula da suka shafi yara. A cikin shekaru 10 da…
Read More