Labarai

Za mu ɓullo da sabon tsarin karɓar haraji – Gwamnatin Tarayya

Za mu ɓullo da sabon tsarin karɓar haraji – Gwamnatin Tarayya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Nijeriya na shirin rage yawan harajin da gwamnatin tarayya da na jihohi ke karɓa daga sama da 60 zuwa ƙasa da 10, shugaban kwamitin sake fasalin harajin ne ya bayyana hakan a ranar Talata. Za a ɓullo da sabon tsarin a wani ɓangare na sauye-sauyen da za a samu wajen gudanar da harkokin kasuwanci cikin sauƙi da kuma ƙara samun kuɗaɗen shiga. Nijeriya, ƙasar da ta fi kowacce ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, tana da kaso 10.8 cikin 100 na haraji da GDP, wanda ɗaya ne daga cikin ƙasashe mafiya ƙarancin wannan adadin…
Read More
Cibiyar horas da kuratan sojoji ta DEPOT ta yaye mutum 6,315 a Zariya

Cibiyar horas da kuratan sojoji ta DEPOT ta yaye mutum 6,315 a Zariya

Daga ISAH GIDAN BAKKO a Zariya A ranar Asabar da ta gabata, cibiyar horas da kuratan sojoji da aka fi sani da' Depot Nigerian Army'' da ke Zariya ta ƙyanƙyashe kuratan sojoji har 6,315 karo na 85. A jawabinsa wajen bikin kammala horas da sojojin, babban kwamandan sojojin Nijeriya Laftana Janar Taoureed Lagbaja ya ja kunnuwan kuratan da aka yaye da su zama sojoji nagari a duk inda aka tura su aiki a ciki da wajen Nijeriya. Laftana Janar Lagbaja ya kuma ce rundunar sonojin Nijeriya da ya ke yin shugabanci za ta ƙara tashi tsaye na ganin ta qara…
Read More
Jega ya ƙalubalanci INEC kan ƙin loda sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa a manhajar IReV

Jega ya ƙalubalanci INEC kan ƙin loda sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa a manhajar IReV

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya ce tilas ne Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta binciki musabbabin rashin shigar da sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa zuwa manhajar duba sakamakon zaɓen INEC (IReV). A wata hira da ya yi da gidan talabijin na ARISE, tsohon Shugaban hukumar ta INEC ya ce zai iya danganta da yawa daga cikin ƙalubalen da aka fuskanta a lokacin babban zaɓen amma ya kamata a duba batun shigar da sakamakon zaɓe. “Kuma idan kun kasance kuna da ƙwarin gwiwa kan tsarin sai kuma a…
Read More
Yadda cire tallafi ke ƙara haifar da gagarumar matsalar fetur a Nijeriya

Yadda cire tallafi ke ƙara haifar da gagarumar matsalar fetur a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Watanni biyar kenan bayan Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin fetur, yayin da ‘yan Nijeriya suka afka cikin matsananciyar tsadar rayuwa, yanzu kuma wasu gaggan matsalolin da ke sake dabaibaye hada-hadar shigo da tataccen fetur cikin Nijeriya daga daga waje, sai bijirowa suke yi su na kwankwatsar ‘yan Nijeriya, ta hanyar zaizaye masu ɗan abin da suke samu na yau da kullum. Bayan cire tallafin fetur da lamarin ya kai ga har lita 1 ta kai N617, Gwamnatin Tarayya ta ce za ta tsame kan ta daga shigo da fetur, domin bai wa ‘yan…
Read More
WHO da UNICEF za su yi wa ‘yan mata miliyan 7.7 rigakafin cutar kansar mahaifa a Nijeriya

WHO da UNICEF za su yi wa ‘yan mata miliyan 7.7 rigakafin cutar kansar mahaifa a Nijeriya

Nijeriya a hukumance ta shigar da allurar rigakafin cutar HPV a cikin tsarin rigakafinta na yau da kullum, da nufin kai wa yara mata miliyan 7.7 agaji cikin zagaye guda na allurar rigakafin cutar, wanda ya kasance mafi girman irinsa a yankin Afirka. Ministan Lafiya da Walwalar Jama'a, Muhammad Ali Pate, ya bayyana matukar damuwarsa kan cutar ta kansar mahaifa, yana mai cewa, "Asarar mata kusan 8,000 a duk shekara daga cutar da ake iya rigakafinta ba abu ne da za a amince da shi ba.“ Pate ya jaddada cewa ceton rayuka da tabbatar da ingantaccen kiwon lafiya su ne…
Read More
Gwamnatin Tinubu za ta ba da fifiko wajen amfani da na’urorin zamani a gidajen rediyo da talabijin – Minista

Gwamnatin Tinubu za ta ba da fifiko wajen amfani da na’urorin zamani a gidajen rediyo da talabijin – Minista

Daga WAKILINMU Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa amfani da kayan aiki na zamani a gidajen rediyo da talbijin na da muhimmanci ga gwamnatin Bola Tinubu. Haka kuma ya jaddada alwashin gwamnati na bai wa harkokin bunƙasa kayan aikin rediyo, talbijin da shirya finafinai goyon baya saboda muhimmancin su ga bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Ya ce su na a sahun gaba wajen samun nasarar inganta tattalin arziki a ƙarƙashin ajandar Farfaɗo da Martabar Nijeriya ta 'Hope Agenda' da gwamnatin Tinubu ta himmatu a kai. Da ya ke jawabi wurin taron AFRICAST na 13…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar Atiku ta neman gabatar da sabuwar hujja a kan Tinubu

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar Atiku ta neman gabatar da sabuwar hujja a kan Tinubu

Daga BASHIR ISAH Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gabatar wa kotun ta neman kotu ta ba shi damar gabatar mata da sabuwar hujja a kan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu. Atiku ya buƙaci kotun da ta ba shi damar gabatar da bayanan da ya ce ya samo game da karatun da Tinubu ya ce ya yi a Jami'ar Jihar Chicago ta ƙasar Amurka. Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar na ra'ayin cewa bayanan bogi ne Tinubu ya miƙa wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a…
Read More
UNESCO ta yi bikin ‘Ranar Amfani Da Kafofin Watsa Labarai Da Yaɗa Bayanai Ta Duniya’ a Abuja

UNESCO ta yi bikin ‘Ranar Amfani Da Kafofin Watsa Labarai Da Yaɗa Bayanai Ta Duniya’ a Abuja

Darakta Janar na Hukumar Bunƙasa Ilimi da Al’adu ta Duniya (UNESCO), Ms. Audrey Azoulay, ta ce a shekarar 2023, kashi 60% na al'ummar duniya mai jimlar mutane biliyan 4.75, sun rungumi amfani da shafukan sada zumunta wajen bayyana abubuwan da suka shafe su da neman amsoshin tambayoyi da sauran mu’amala. Ms. Audrey, wanda Darakta na Hukumar UNESCO ta Nijeriya, Mista Diallo Abdourahamane, ya wakilta, ta bayyana hakan a yayin bikin Ranar Amfani da Kafofin Yada Labarai da Yaɗa Bayanai ta bana, ranar Laraba, a Abuja. Ta yi bayani a kan alfanun hanyoyin sadarwa na zamani da kuma ƙalubalen da suke…
Read More
Kotun Ƙoli: Gobe su Atiku za su san matsayinsu

Kotun Ƙoli: Gobe su Atiku za su san matsayinsu

Daga BASHIR ISAH A ranar Alhamis ta wannan makon Kotun Ƙoli za ta yanke hukunci kan ƙarar da 'yan takarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam'iyyun PDP da LP, Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar inda suke ƙalubalantar nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu wadda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar masa da ita. Daraktan Yaɗa Labarai na Kotun Ƙoli, Dr Awemeri Festus Akande, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba. Ya ce an ɗauki matakan tsaron da suka kamata domin tabbatar da lumana a ciki da wajen kotun. Baya ga rashin gamsuwa da nasarar Tinubu, Atiku yana kuma neman…
Read More