Labarai

Ma’aikata ne matsalar hanyar Bachaka zuwa Dankirya a Kebbi – Alh. Umar Dankirya

Ma’aikata ne matsalar hanyar Bachaka zuwa Dankirya a Kebbi – Alh. Umar Dankirya

Daga JAMIL GULA a Kebbi 'Yan kasuwa da ke hada-hada kan hanyar garin Bachaka da ke kan iyakokin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar a ɓangaren Jihar Kebbi sun koka bisa yadda jami'an tsaro suka mayar da su waɗansu shanun tatsa. Alhaji Umar Ɗankirya ɗaya daga cikin shugabannin 'yan kasuwa da ke sayar da abinci ne ya bayyana haka a wata zantawa da wakilinmu a garin Bachaka ƙarshen makon da ya gabata. Alhaji Umar ya ce jami'an tsaro da suka haɗa da 'yan sanda da masu hana fasakwabri da jami'an shige da fice da na farin kaya da ke aiki kan wannan…
Read More
Na biya wa mutum shida Umara saboda murnar zagayowar Mauludin Manzon Rahama – Sharif Sidi Abdulkaqadir

Na biya wa mutum shida Umara saboda murnar zagayowar Mauludin Manzon Rahama – Sharif Sidi Abdulkaqadir

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Alhaji Sharif Sidi Abdulqadir Sarkin Baƙi, Fitaccen sharifin nan wanda ke kashe miliyoyin nairori wajen tallafa wa maqota sama da 400 a abinci a duk wata da kuma yin hidima ta maqudan kuɗaɗe a wajen shirya katafaren Mauludi da kuma raba kuɗaɗe da kayayyaki da kujerun Makkah duk shekara. Ya ce wannan karon ya biya wa muta ne biyar waɗanda suka samu cin gasa da yake shiryawa a duk Maulidi na waɗanda suka sa wani suna ko dai sunan da ya dace da sunayen iyalan gidan Manzon Allah ko kuma sunayen da ya dace da…
Read More
Ribar dimukraɗiyya sai hamdala a Zariya, amma a ƙara duba mata – Hajiya Salamatu

Ribar dimukraɗiyya sai hamdala a Zariya, amma a ƙara duba mata – Hajiya Salamatu

Daga ISAH GIDAN BAKKO a Zariya Wata fitacciyar 'yar siyasa a Jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar birnin Zariya, Hajiya Salamatu ta bayyana yadda wasu zaɓaɓɓu ke rabon ribar dimukuraɗiyya a gundumomi goma sha uku a ko ƙaramar hukumar Zariya sai dai ta koka na yadda mata ba a yayyafa masu kamar yadda ake yayyafa wa maza ba a cewarta. Hajiya Salamatu ta ci gaba da cewa duk wani ɗan siyasa da kuma waɗanda ba ma siyasar suke yi ba, ya san jam'iyyar APC ta yi sa'ar samun wakilai guda biyu da suka san yadda al'umma suka yi amfani da damar…
Read More
Ɗaura aure ba bisa ƙaida ba: Kotu ta aike da ango da amarya da waliyyansu zuwa gidan gyaran hali

Ɗaura aure ba bisa ƙaida ba: Kotu ta aike da ango da amarya da waliyyansu zuwa gidan gyaran hali

Daga WAKILINMU Kotun Shari’ar Musulunci dake zama a ƙofar fada a Haɗejia ƙarƙashin mai shari’a Aliyu Muhammad Kwalam ta soke wani aure da aka yi ba bisa ƙa’ida ba, inda ake zargin wani saurayi da budurwa sun ɗaura wa kan su. Waɗanda ake tuhumar su 5 sun haɗa da Angon da Amarya da Waliyyansu da kuma mai masaukin baƙi. A cewar ɗan sanda mai gabatar da ƙara sufeta Ya'u Ismail ana tuhumar aikata laifuka 3 da suka haɗa haɗin baki da tada hankalin jama’a laifin da ya saɓa wa sashen doka na 122. Da kuma laifin karya dokar musulunci ta…
Read More
Ku yi wa duk wanda aka kawo ɗauke da raunin bindiga magani kafin neman rahoton ‘yan sanda, umarnin IGP ga ma’aikatan lafiya

Ku yi wa duk wanda aka kawo ɗauke da raunin bindiga magani kafin neman rahoton ‘yan sanda, umarnin IGP ga ma’aikatan lafiya

Daga BASHIR ISAH Muƙƙadashin Babban Sufeton 'Yan Sanda, IGP Olukayode Egbetokun, ya bai wa ma'aikatan kula da lafiya a faɗin ƙasa umarni a kan su riƙa yi wa duk wani da aka kawo asibiti ɗauke da raunin bindiga magani ba tare da neman rahoton 'yan sanda ba. Egbetokun ya ba da wannan unarnin ne tare kuma da kiran ma'aikatan kiwon lafiya da su wayar da kan 'yan kan wannan batu. IGP ya ba da umarnin ne bisa la'akari da Dokar wajabta kula da masu ɗauke da raunin bindiga ta 2017. Umarnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwar cikin gida mai…
Read More
An naɗa sabon Magajin Garin Zazzau

An naɗa sabon Magajin Garin Zazzau

Daga BASHIR ISAH Masarautar Zazzau ta naɗa Alhaji Mu'azu Nuhu Bamalli a matsayin sabon Magajin Garin Zazzau. Bayanin naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar da masarautar ta fitar a ranar Juma'a mai ɗauke da sa hannun Jami'in Yaɗa Labarai, Abdullahi Aliyu Kwarbai. Alhaji Mu'azu yayan tsohon Magajin Garin Zazzau, Ambasada Mansur Nuhu Bamalli ne wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Juma'a ta makon jiya. Kafin sabon naɗin nasa, Alhaji Mu'azu Nuhu Bamalli shi ne Baraden Zazzau. Sabon Magajin Garin na Zazzau Darakta ne a Babban Bankin Nijeriya kuma ƙani ga Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR A…
Read More
Emefiele ya faɗa komar EFCC jim kaɗan bayan kuɓuta daga hannun DSS

Emefiele ya faɗa komar EFCC jim kaɗan bayan kuɓuta daga hannun DSS

Daga BASHIR ISAH A halin da ake ciki, tsohon Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, na tsare a hannun Hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC don amsa tabayoyi da fuskantar bincike. Majiyarmu ta ce ta samu tabbacin Emefiele na can babban ofishin EFCC da ke Jabi, Abuja, bayan da jami'anta suka ɗauke shi cikin dare a ranar Alhamis jim kaɗan bayan da hukumar DSS ta sako shi. Majiya mai tushe ta ce EFCC ta damƙe Emefiele ne bisa zargin aikata ba daidai ba a lokacin da yake shugabancin CBN. “Tabbas, yanzu haka Emefiele na tsare a hannunmu (EFCC), a…
Read More
Gobarar tanka ta jikkata sama da mutum 20 a Kaduna

Gobarar tanka ta jikkata sama da mutum 20 a Kaduna

Daga BASHIR ISAH Aƙalla mutum 20, ciki har da jami'an kwana-kwana da 'yan banga suka jikkata sakamakon gobarar tankar mai da ta auku ranar Juma'a a Jihar Kaduna. MANHAJA ta kalato cewar, gobarar ta auku ne a daidai lokacin da ake sauke mai daga tankar a wani gidan mai da ke Rigasa cikin yankin Ƙaramar Hukumar Igabi a jihar. Da yake tabbatar da aukuwar iftila'in, Daraktan Hukumar Kwana-kwana na Jihar, Paul Aboi, ya ce gobarar ta ji wa wasu jami'ansu su biyar da wasu 'yan bangan jihar haɗi da wasu masu wucewa da dama raunuka. Jami'in ya ɗora alhakin faruwar…
Read More
Irin ta’asar da Yahudawa ke yi mana a Palastinu – Jakada Shawesh

Irin ta’asar da Yahudawa ke yi mana a Palastinu – Jakada Shawesh

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Jakadan Ƙasar Palastinu a Nijeriya, Abdullah Shawesh, ya bayyana irin ta’asar da ya ce Ƙasar Isra’ila (wato Yahudawa) suke yi wa al’ummar Palastinu na kisan gilla da kisan kiyashi kan waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, kamar ƙananan yara da mata, inda kawo yanzu aka kashe kimanin Palastinawa fiye da mutum 6,000, waɗanda fiye sa rabinsu yara ne ƙanana. Shawesh ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai, ciki har da Blueprint Mahhaja, a ofishin jakadancin Palastinu da ke Abuja ranar Laraba. Idan za a iya tunawa, a ranar 7…
Read More
Shan fetur ya ragu zuwa lita miliyan  44.3 kowacce rana a Nijeriya

Shan fetur ya ragu zuwa lita miliyan  44.3 kowacce rana a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI Amfani da man fetur na cikin gida na ƙasar Nijeriya ya ragu sosai daga litoci miliyan 66.7 da ake sha a kullum a faɗin ƙasar zuwa litoci miliyan 44.3 a kowacce rana.  Shugaban zartarwa na hukumar kula da man fetur ta NMDPRA, Farouk Ahmed Ahmed shi ya bayyana haka a jawabinsa na buxe taro a taron 'Oil Trading and Logistics' (OTL) na makon Afirka na bana, shekarar 2023, da aka gudanar ranar Litinin a jihar Legas. A cewarsa, an samu raguwar kaso 33.58 a kan yawan man da ake sha a kullum.  A jawabin nasa, shugaban…
Read More