26
Feb
Daga BASHIR ISAH Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce yau Lahadi za a fara tattara sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan Majaisar Tarayya a hukumance. Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar sa'ilin da yake bayani game da sha'anin zaɓe a Abuja. Yabuku ya ce na'urar BVAS ta yi aiki sosai a galibin wurare a sassan ƙasa, yayin da an fuskanci ƙalubale a wasu ɓangarori. A cewarsa, ƙalubalen da aka fuskanta shi ne na jinkirin da aka samu wajen buɗe wasu rumfunan zaɓe a kan lokacin da aka tsayar, wato ƙarfe 8:30 na safe.
