Labarai

Gwamnan Zamfara ya yi wa fursunoni 46 afuwa

Gwamnan Zamfara ya yi wa fursunoni 46 afuwa

Daga MUHAMMAD SANUSI, a Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya yi wa fursunoni 46 a jihar. Fursunonin da afuwar ta shafa waɗanda kotunan shari’a na jihar suka yanke musu hukunci ne tare da tsare su a gidan yari a Gusau. Babban Lauyan jihar kuma Kwamishinan Shari'a, Barista Junaidu Aminu Kaura ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar gidan gyaran hali ta jihar da ke Gusau a ranar Juma’a. A cewarsa, waɗanda aka yi wa afuwar sun haɗa da fursunoni 30 da aka yanke wa hukunci daban-daban na ɗaurin shekaru 20 zuwa…
Read More
Buhari ya nuna alhininsa game da mutuwar Pele

Buhari ya nuna alhininsa game da mutuwar Pele

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya nuna alhininsa dangane da mutuwar gwarzon ɗan wasan ƙallon ƙafar nan na ƙasar Brazil, Edson Arantes do Nascimento, wanda aka fi sani da Pele. Pele ya rasu ne a ranar Alhamis bayan fama da cutar kansa. Cikin saƙon ta'aziyyar da ya aika a madadin 'yan Nijeriya, Buhari ya yi fatan mutuwa ta zama hutu ga marigayin. Ya kuma bayyana shi a matsayin wanda ya ba da gudunmawa mara misaltuwa a duniyar ƙwallon ƙafa da ma fannin wasannin motsa jiki baki ɗaya. Ya ƙara da cewa, marigayin ya taka rawa wajen samar da…
Read More
Gidauniyar Sadiq Maira da haɗin kan hukumomi mu ke yaƙi da cin zarafin yara – Sayyada Umaira

Gidauniyar Sadiq Maira da haɗin kan hukumomi mu ke yaƙi da cin zarafin yara – Sayyada Umaira

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Shugabar Gidauniyar Sadiq Maira, Ambasada Sayyada Umaira Sadiq, Tauraruwar Hausawan Afirka ta ce gidauniyar su ta Sadiq Maira Foundation for the Less Privileged, tana yaƙi da cin zarafin 'ya'ya mata da kuma taimaka wa marasa galihu. Ambasada Sayyada Umaira, ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da wakilin mu, a Gombe, inda ta ce suna haɗa kai da jami'an tsaro da alƙalan kotuna har ma da hukumomi wajen ƙwato wa duk wata yarinya da aka yi wa fyaɗe ko aka ci zarafin ta 'yanci. Ta ce idan suka samu rahoton cin zarafi…
Read More
‘Yan siyasa ke maguɗin zaɓe ba mu ba, inji INEC

‘Yan siyasa ke maguɗin zaɓe ba mu ba, inji INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta bayyana cewa ba za ta bari a yi maguɗin zaɓe a babban zaɓe mai zuwa na 2023 ba, domin daman ba halinta ba ne. Sabuwar Kwamishinar Zaɓe ta Jihar Ebonyi, Onyeka Ugochi ce ta bayyana haka yayin wani taron tattaunawa da ‘yan jarida da ƙungiyoyin fararen hula, CSOs. A cewarta, maguɗin zaɓe zai yi matuqar wahala domin hukumar ta shirya tsaf domin tabbatar da sahihin zae. Misis Ugochi ta ce: “INEC ba za ta taɓa yin maguɗin zaɓe ba. 'Yan siyasa ne ke tafka maguɗin…
Read More
Malamai a Bauchi sun ƙalubalanci hukuncin kisa a kan Abduljabbar

Malamai a Bauchi sun ƙalubalanci hukuncin kisa a kan Abduljabbar

• Sun ce za su ɗaukaka ƙara Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Wasu Jiga-jigan malaman addinin Musulunci dake ƙarƙashin tutar ‘As’habul Kahfi Warraqeen’ mazauna garin Bauchi sun yi kakkausar suka da fatali da abinda suka kira saɓanin addinin Islama, da hukunci kisa na jeka-na-yika da Alƙali Ibrahim Sarki Yola ya zartar a kan Shehin Malami Abduljabbar Nasiru Kabara bisa zargin yin ɓatanci ga Shugaban Halitta Muhammadu, (SAW) Aminci Allah ya tabbata a gare shi. “Wannan banbaraqwai da Islama, jeka-na-yi-kan hukunci da Ibrahim Sarki Yola ya zargi ɗumgurugum ɗinsa ba daidai ba ne kuma baya cikin Islama, saboda haka mun yi…
Read More
Sojojin Nijeriya sun kashe wasu kwamandojin Boko Haram a Borno

Sojojin Nijeriya sun kashe wasu kwamandojin Boko Haram a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu hare-hare ta sama da dakarun sojin Nijeriya suka kai ranar 20 ga watan Disamba a ƙauyen Mantari an yankin Gezuwa da ke cikin ƙaramar hukumar Bama a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Nijeriya ya yiisanadin kashe wasu manyan kwamandojin ƙungiyar Boko Haram. A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin sama na ƙasar Air Commodore Edward Gabkwet ya sanya wa hannu ya ce harin ya yi sanadin mutuwar manyan kwamandojin qungiyar da suka haɗar da Khaids Abbah Tukur da Maimusari da kuma Bakura Jega, tare da wasu 'yan ƙungiyar da dama. Labarin…
Read More
“Masu garkuwa da mutane ke iko da wani yanki na Jihar Zamfara”

“Masu garkuwa da mutane ke iko da wani yanki na Jihar Zamfara”

Daga SUNUSI MUHAMMAD a Gusau A Jihar Zamfara mutum huɗu sun mutu wasu goma sun samu raunuka a garin Ruwan Baure da ke cikin Ƙaramar Hukamar Gusau bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai a yammacin Litinin. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu garkuwa da mutanen suka sako wasu mutane sama da 200, sai dai sun kashe wasu mutum 28 a lokacin da suka yi garkuwar da su a garin Randa da ke cikin Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar ta Zamfara. Wannan mutumin da BBC ta sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, ya shaida harin da…
Read More
Fashewa mai ƙarfi ta yi ajalin mutun huɗu a Kogi

Fashewa mai ƙarfi ta yi ajalin mutun huɗu a Kogi

Daga BASHIR ISAH An samu aukuwar fashewa mai ƙarfi da safiyar Alhamis a yankin Okene cikin Jihar Kogi, lamarin da ya yi ajalin aƙalla mutum huɗu kamar yadda rahoton 'yan sanda ya nuna. Majiyarmu ta ce, fashewar ta auku ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe na wannan rana. An ce fashewar ta auku ne a kusa da fadar Sarkin Ibira da ke hanyar Kuroko a Okene. Haka nan, fashewar ta yi sanadiyar ƙonewar wasu abubuwan hawa a yankin. Wani ganau ya ce, fashewar ta auku ne a cikin wata mota da wasu babura, inda duka matuƙa baburan suka mutu…
Read More
Shugaban Ƙungiyar Ohanaeze, George Obiozor ya kwanta da dama

Shugaban Ƙungiyar Ohanaeze, George Obiozor ya kwanta da dama

Daga WAKILINMU Shugaban ƙungiyar nan ta ƙabilar Ibo Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor ya rasu. Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma ne ya sanar da mutuwar cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba da daddare. Ya ce, “A madadin gwamnati da al’umar Jihar Imo, ni, Sanata Hope Uzodimma, Gwamnan Jihar Imo na sanar da rasuwar Shugaban Ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor ga duniya. “Farfesa George Obiozor , fitaccen masani, dattijo kuma uban ƙasa ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya. “Rasuwar shahararren jagoran Igbon kuma tsohon jakadan Nijeriya a Amurka, babban rashi ne ga Jihar Imo, yankin Kudu…
Read More
Gobara ta ƙone gidaje a Legas

Gobara ta ƙone gidaje a Legas

Daga BASHIR ISAH Al'uma mazauna yankin Ebute Metta a Jihar Legas sun shiga hali na jimami da alhini sakamakon gobarar da ta auku a yankin ranar Talata da safe. Rahotanni sun ce, gobarar ta ƙone gidaje da dukiya mai mai yawa. An ce gobarar ta fara ne daga wani gida sannan ta faɗaɗa zuwa maƙwabta. Wani ganau ya ce, "Da misalin ƙarfe 9:05 na safe na kira Hukumar Kwana-kwana inda jami'ansu suka isa wurin bayan minti 40. "Cinkoson jama'a da ya haɗu a wurin ya haifar da jinkiri, domin sai da 'yan sanda suka taimaka kafin 'yan kwana-kwanan suka samu…
Read More