Labarai

An naɗa Uba Kari Wazirin Bauchi bayan badaƙalar tuɓe Muhammadu Kirfi

An naɗa Uba Kari Wazirin Bauchi bayan badaƙalar tuɓe Muhammadu Kirfi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Masarautar Bauchi ta naɗa Alhaji Muhammad Uba Ahmed Kari a matsayin sabon Wazirinta kuma ɗan Majalisar Masarautar. A wata sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na Masarautar Bauchi, Babangida Hassan Jahun ya fitar a ranar Alhamis, ya sanar da cewa Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu ya naɗa Alhaji Muhammadu Uba Ahmad Kari a matsayin sabon Wazirin Bauchi.  Kan wannan matakin, Uba Ahmed Kari ya maye gurbin Muhammadu Bello Kirfi da aka samu da rashin biyayya wa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad. Wani yanki na sanarwa na cewa: "Majalisar Mai Martaba Sarkin Bauchi…
Read More
Bayyana kadara: Kotu ta haramta wa DSS tsare shugaban INEC

Bayyana kadara: Kotu ta haramta wa DSS tsare shugaban INEC

Daga WAKILINMU Babbar Kotun Tarayya a Abujata dakatar da karar da aka shigar gabanta na neman tsige Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, daga mukaminsa kan zargin ba da bayanan karya dangane da kadarorinsa. Alƙalin Kotun, M. A. Hassan, ya ce bayanan gaskiya Yakubu ya bayar dangane da kadarorin da ya mallaka kuma daidai da doka, don haka ya ƙi amincewa da ƙarar da aka shigar kan shugaban na INEC. A zaman kotun na ranar Laraba, alƙalin ya hana hukumar DSS da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da Hukumar Da'ar Ma'aikata (CCB) kama Yakubun. Ya yanke hukuncin ne…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Uba Kari ya zama sabon Wazirin Bauchi

Da Ɗumi-ɗumi: Uba Kari ya zama sabon Wazirin Bauchi

Masarautar Bauchi ta naɗa Alhaji Muhammad Uba Ahmed Kari a matsayin sabon Wazirinta kuma ɗan Majalisar Masarautar. Bayanin naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar da Masarautar ta fitar ranar Alhamis ta hannun jami'in labaranta, Babangida Hassan Jahun. Sanarwar ta ce za a yi wa sabon Wazirin Bauchin naɗi ne a ranar Juma'a, 6 ga watan da ake ciki a Fadar Masarautar Bauchi. Wannan na zuwa ne bayan da masarautar ta tuɓe Muhammadu Bello Kirfi a matsayin wazirinta saboda rashin da’a ga Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.
Read More
Wanda ya ka harin bom yayin ziyarar Buhari Kogi ya fada a komar DSS

Wanda ya ka harin bom yayin ziyarar Buhari Kogi ya fada a komar DSS

Daga WAKILINMU Hukumar tsaro ta DSS ta sanar cewa ta cafke wanda ake zargi ya jagoranci dana bom din da ya tashi a yayin da Shugaba Buhari ke ziyarar aiki a Jihar Kogi.  A ranar 29 ga Disamba, 2022 ne bom ya tashi kusa da Fadar Sarki Ohinoyi na Kasar Ibira a Okene, Jihar Kogi yayin da Shugaba Buhari ke ziyarar aiki a masarautar. Mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, ya faɗa a ranar Laraba cewa, "Yayin bincikensu an gano wanda aka cafken babban kwamanda ne a ISWAP. "Ya jagoranci ko yana da hannu a hare-haren da aka kai…
Read More
Kwamishinar Bauchi ta ajiye aiki bayan tuɓe wa mahaifita rawani a masarauta

Kwamishinar Bauchi ta ajiye aiki bayan tuɓe wa mahaifita rawani a masarauta

Daga WAKILINMU Sakamakon tuɓe wa mahaifinta rawani a matsayin Wazirin Bauchi da Masarautar Bauchi ta yi, ya sa Kwamishinar Bunƙasa Ƙungiyoyi, Ƙananan da Matsakaitan Sana’o’i ta Jihar Bauchi, Sa’adatu Bello Kirifi, ta yi murabus daga muƙaminta. Sa’adatu Bello Kirifi ta yi murabus ne ƙasa da awa 24 bayan tuɓe wa mahaifin nata, Alhaji Muhammadu Bello Kirfi, rawaminsa na Wazirin Bauchi tare da sallamar sa daga Majalisar Masarauar a ranar Talata. A takardar ajiye aikin da ta aike wa Gwamna Bala Mohammed ranar Laraba, Honorabul Sa’adatu ta ce, “Ina miƙa takardata ta yin murabus daga Majalisar Zartarwa da kuma kujerar Kwamishinar…
Read More
Sarkin Bauchi ya tsige Wazirinsa saboda rashin ɗa’a ga Gwamnan jihar

Sarkin Bauchi ya tsige Wazirinsa saboda rashin ɗa’a ga Gwamnan jihar

Daga WAKILINMU Masarautar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Dokta Rilwanu Suleiman Adam ta tube wazirinta, Muhammadu Bello Kirfi, daga mukaminsa saboda rashin da’a ga Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed. Masarautar ta bayyana haka ne cikin wasiƙar da ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Janairu, 2023 da kuma sa hannun Sakataren masarautar, Shehu Mudi Muhammad. Majiya ta kusa da Kirfi ta ce tuɓaɓɓen Wazirin ba ya ƙasar sakamakon ya yi tafiya balle kuma a ji ta bakinsa. Ta ce idan Allah Ya yi dawowarsa, za su zauna su tattauna kan batun. Idan dai za a iya tunawa, a 2017…
Read More
An tsinci gawar yaron da aka kashe iyayensa a Ogun

An tsinci gawar yaron da aka kashe iyayensa a Ogun

Daga BASHIR ISAH An gano gawar wani yaro mai suna Oreoluwa Fatiniye ranar Talata a wani rafin Jihar Ogun. Rahotanni daga jihar sun ce, wasu masunta ne suka gano gawar a rafin da ke yankin Adigbe-Obada a jihar. Jaridar Premium Times ta ce, wannan na zuwa ne kwana uku da kashe iyayen yaron a ranar Sabuwar Shekara, wato Lahadin ta gabata, a Abeokuta babban birnin jihar. An yi wa Kehinde Fatinoye da matarsa, Bukunola, kisan gilla ne a gidansu da ke GRA ta hanyar banka wa gidan wuta wanda har yanzu ba a gano ko su wane ne suka aikata…
Read More
An kori ’yan sanda 7 daga aiki kan yi wa jama’a kwace

An kori ’yan sanda 7 daga aiki kan yi wa jama’a kwace

Wasu ’yan sanda da ke yawo da na’urar cirar kuɗi ta POS suna kwatar kuɗaɗe daga hannun mutane sun rasa aikinsu. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Imo, Mohammed Barde, ya ce jami’an da aka kora su bakwai sukan kama mutane su tafi da su a wata mota zuwa wasu wurare na musamman su kwace musu kuɗaɗe. Ya ce, dubun jami’an da aka kora ta cika ne bayan rundunar ta samu ƙorafi daga jama’ar gari kan abin da suke aikatawa. Ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis a Owerri, baban birnin jihar, cewa an gano jami’an sukan yi sintiri ɗauke da…
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Kanal Lawal Yandoto a Zamfara

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Kanal Lawal Yandoto a Zamfara

Daga MUHAMMAD SANUSI a Gusau 'Yan bindiga a Jihar Zamafara su ui garkuwa da Kanal Lawal Rabi’u Yandoto (mai ritaya) a kan hanyarsa daga Gusau zuwa mahaifarsa ‘Yandoto a Karamar Hukumar Tsafe a jihar. Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa Blueprint Manhaja ta waya cewar, da yammacin Lahadi ‘yan bindigar suka tare Kanal Yandoto inda suka yi garkuwa da shi tare da ‘ya’yansa biyu da wasu mutane biyu. Majiyarmu ta ce, “Mun ji ƙarar harbin bindiga a kusa da garinmu na Yandoto kuma kowa ya fara gudun tsira don samun mafaka". Ya ce nan take…
Read More
‘Yan sanda sun tsare basaraken da ya yi lalata da ɗan shekara 14 a Zariya

‘Yan sanda sun tsare basaraken da ya yi lalata da ɗan shekara 14 a Zariya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta kama wani basarake a Zariya da ya yi wa ɗan shekara 14 fyaɗe. Kakakin rundunar Muhammadu Jalige wanda shine ya sanar da haka ranar Laraba, ya ce rundunar za ta maka basaraken a kotu da zarar 'yan sanda sun kammala bincike akai. Da ya ke tattaunawa da Kamfanin Dillanci Labaran Nijeriya wani ɗan uwan wannan yaro, Hamza Zubairu ya ce basaraken ya yi lalata da ƙanensa ne ranar 9 ga Disamba a Unguwar Ƙwarbai. Zubairu ya ce basaraken makwabcin su ne kuma kowa a unguwan na yi masa…
Read More