Labarai

Matashi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa a Kano

Matashi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa a Kano

Daga WAKILINMU Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta tsare wani matashi ɗan shekara 20 mai suna Ghadaffi Sagir, bayan da ya yi iƙirarin kashe kishiyar mahaifiyarsa. Bayanan 'yan sanda sun nuna matashin ya aikata ɗanyen aikin ne ta hanyar amfani da makami mai tsini da kuma maƙare 'yarta. Jaridar News Point Nigeria ta rawaito lamarin ya faru ne ranar Asabar da daddare da misalin ƙarfe 11:00 a Rijiyar Zaki kusa da Layin Dorawanyan Kifi cikin Ƙaramar Hukumar Ungogo a jihar. Da yake tabbatar da cafke matashin a ranar Lahadi, Shugaban Ƙaramar Hukumar Ungogo, Injiniya Abdullahi Garba Ramat, ya ce wanda…
Read More
Dalilin tuɓe wa tsohon Wazirin Bauchi, Bello Kirfi rawani

Dalilin tuɓe wa tsohon Wazirin Bauchi, Bello Kirfi rawani

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce tsige tsohon minista, Alhaji Muhammadu Bello Kirfi da aka yi a matsayin Wazirin Bauchi hakan ba shi da nasaba da alaƙarsa da ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar. Gwamnatin Bauchi ta bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu, Hon AbdulRazak Nuhu Zaki, a wata hira da BBC Hausa ta yi da shi ranar Asabar. A cewar Kwamishinan, sau da dama tsohon Wazirin ya janyo wa Masarautar Bauchi ɓacin suna, kuma bayan gargaɗin da aka yi masa Majalisar Masarautar ta ga dacewar ɗaukar matakin ladabtarwa…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: NRC ta rufe tashar jirgin ƙasa a Edo

Da Ɗumi-ɗumi: NRC ta rufe tashar jirgin ƙasa a Edo

Daga BASHIR ISAH Hukumar Sufurin Jirgin Ƙasa ta Nijeriya (NRC), ta rufe tashar jirgi da ke Ekehen a Jihar Edo har sai 'baba ta gani'. Hukumar ta ba da sanarwar rufe tashar ne a zaurenta na WhatsApp inda takan yi mu'amala da fasinjoji. Sanarwar ta ce, "Ana sanar da ɗaukacin jama'a musamman fasinjojinmu cewa, mun rufe tashar Ekehen na wucin-gadi saboda matsalar tsaro." Kazalika, wata sanarwa ta ce, “Saboda halin da tashar Ekehen ta faɗa ranar Asabar, jirgi mai lamba WITS 01/ 02 ba zai sake tsayawa ba a Tashar Ekehen."
Read More
Ƙananan hukumomin Borno 2 na hannun Boko Haram – Zulum

Ƙananan hukumomin Borno 2 na hannun Boko Haram – Zulum

Daga WAKILINMU Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya tabbatar cewa a halin da ake ciki Boko Haram na riƙe da wasu ƙananan hukumomi biyu a jihar. Ya ce ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa su ne; Guzamala da Kukawa da ke yankin Borno ta Arewa. Zulum ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja ranar Juma'a. Yayin ziyarar tasa, Zulum ya shaida wa manema labarai cewa hakan ba zai hana shi gudanar da zaɓe a yankunan da lamarin ya shafa ba. “Insha Allah, ba mu da kowace matsala a…
Read More
Mulkin soji ya fi na Buhari kyautawa – ASUU

Mulkin soji ya fi na Buhari kyautawa – ASUU

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Malaman Jami'o'in Nijeriya ASUU, ta ce mulkin soji ya fi na gwamnatin farar hula, musamman wajen kyautata jin daɗin malamai a Nijeriya. Shugaban ASUU na Ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke shi ne ya bayyana hakan ranar Talata 5 ga Janairu, 2023, a wajen wani taron ƙaddamar da wasu littafan karatu guda 50 na manyan makarantu da marubutan Nijeriya suka wallafa ƙarƙashin tallafawar Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu na Nijeriya (TETfund), a Abuja. Idan dai za a iya tunawa, a ranar Juma'a ne 16 ga Oktoba, 2022 ASUU ta janye yajin aikin watanni takwas da…
Read More
NANS ta nemi agajin Buhari don hana ƙarin kuɗin makaranta

NANS ta nemi agajin Buhari don hana ƙarin kuɗin makaranta

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya (NANS) ta nuna rashin yardarta kan take-taken Gwamnati na neman ƙara kuɗin makaranta na jami'o'in tarayya da kashi 200 daga wannan shekara. Wannan ya sa ƙungiyar ta ce tana kira da babbar murya ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya taimaka ya gaggauta sa baki don taka wa shirin burki kafin hakan ya ta da ƙura a ƙasa. Ƙungiyar ta bayyana rashin jin daɗinta ne cikin wasiƙar da ta aike wa Shugaba Buhari mai ɗauke da kwanan wata 4 ga Janairu, 2023. Wasiƙar ta samu sa hannun Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Usman Umar Barambu da…
Read More
Buhari zai wadata Burundi da fetur duk da ƙarancinsa a Nijeriya

Buhari zai wadata Burundi da fetur duk da ƙarancinsa a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Nijeriya za ta wadata ƙasar Burundi da man fetur, inda ya yi alƙawarin cewa Kamfanin Man Fetur na Nijeriya zai duba buƙatar ƙasar na tallafin makamashi. A cewar wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina ya fitar, Buhari ya bayyana hakan ne a fadar shugaban ƙasa ranar Talata yayin da yake karɓar baƙoncin Shugaba Ƙasar Burundi, Evariste Ndayishimiye, wanda yazo da buƙatar. “A kan neman taimako a fannin samar da makamashi musamman man fetur da shugaban ƙasar Burundi ya yi, shugaba Buhari ya ce,…
Read More
‘Yan sanda sun cafke matashin da ya yi garkuwa da mahaifinsa a Kwara

‘Yan sanda sun cafke matashin da ya yi garkuwa da mahaifinsa a Kwara

Daga WAKILINMU Ana zargin wani matashi da yin garkuwa da mahaifinsa a Jihar Kwara inda ya buƙaci a biya fansar miliyan N2.5. A sanarwar manema labarai da ya fitar a Ilorin Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, ya ce jami'an rundunar yaki da masu garkuwa da mutane a jihar sun cafke yaron. “Yayin bincike wanda ake zargin ya yi ikirarin yin garkuwa da mahaifin nasa bayan haɗa baki da wasu mutum biyu. "Lamarin ya auku ne a yankin Igboho/Igbeti Oyo inda suka karɓi kuɗin fansa N2.5m ransom,” in ji shi. Jami'in ya ce suna ci gaba da…
Read More
Sarkin Kano, Aminu Bayero ya angonce

Sarkin Kano, Aminu Bayero ya angonce

Daga WAKILINMU A ranar Juma'a aka ɗaura auren Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da amaryarsa Hauwa'u Adamu Abdullahi Dikko. An ɗaura Auren ne a gidan marigayi Jarman Kano, Farfesa Isah Hashim da ke unguwar Nassarawa a birnin Kano. Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani Cigari, shi ne ya kasance wakilin Mai Martaba Sarkin Kano, yayin da Alhaji Shehu Hashim ya yi waliccin amarya. Majiyarmu ta ce tun a shekarar da ta gabata aka yi baikon basaraken da amaryarsa inda sai a wannan lokaci aka ɗaura auren. An ce amaryar zuri'ar marigayi Malam Jamo ne wanda ɗan uwa yake ga…
Read More
Birgediya-Janar Chukwu ya kwanta dama

Birgediya-Janar Chukwu ya kwanta dama

Bayanan da Manhaja ta samu na nuni da Birgediya-Janar JTE Chukwu (mai murabus), ya kwanta dama. Sashen Hulɗa da Jama'a na Rundunar Sojoji (DAPR) ne ya sanar da hakan, inda ya ce marigayin ya rasu ne ranar Alhamis. Sanarwar ta ce marigayin tsohon Darakta ne na DAPR, kuma ya rasu ne a gidansa da ke Abuja.
Read More