Labarai

Gwamnatin Katsina ta ɗauki matakin bunƙasa noman mangwaro a faɗin jihar

Gwamnatin Katsina ta ɗauki matakin bunƙasa noman mangwaro a faɗin jihar

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Aminu Bello Masari, ta ɗauki matakin bunƙasa ayyukan noman mangwaro a faɗin Jihar Katsina. Shugaban ƙungiyar masu noma da sarrafa mangwaro, ya ce an shirya horon ne domin a ƙarfafa guiwa tsakanin manoman mangwaro don inganta samar da kuɗaɗen shiga a jihar Katsina. Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir M.D na hukumar KATARDA, wanda ya samu wakilcin Alhaji Abubakar Dabo, ya bayyana cewa, taron zai taimaka matuqa ga mahalartan domin su samu ilimi na yadda ake dasa gami da rainon itatuwan mangwaro ya zuwa girmansu a zamanance. Ya ce hakan zai taimaka…
Read More
Ka yi kaɗan ka rushe sabbin masarautun Jihar Kano – Ganduje ga Abba Gida-Gida

Ka yi kaɗan ka rushe sabbin masarautun Jihar Kano – Ganduje ga Abba Gida-Gida

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Talata ne gwamnatin jihar Kano ta shaida wa jam’iyyar adawa ta New Nigeria People’s Party, NNPP cewa shirinta na mayar da tsohon birnin ga tsohon masarautu tare da kakkave sabbin masarautu ba zai tava yiwuwa ba. Gwamnatin ta ce sabunta sheqar da ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya yi na sallamar sabbin masarautu idan aka zaɓe shi, hakan na nufin ba zai yi aiki da dokar kafa sabuwar masarautu da kuma shawarar da jama’a suka yanke. Gwamna Ganduje ta bakin Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na…
Read More
Direbobin tanka sun toshe hanyar Zariya-Kano bayan kashe abokin aikinsu

Direbobin tanka sun toshe hanyar Zariya-Kano bayan kashe abokin aikinsu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Direbobin tanka sun toshe babbar hanyar Zariya zuwa Kano a ranar Laraba don nuna tsantsan vacin ransu kan kashe ɗaya daga cikinsu da wani soja ya yi. Lamarin ya faru ne wajen misalin ƙarfe 3:30 na yamma, lokacin da direbobin suka haddasa mummunan cunkoson ababen hawa sakamakon rufe hanyar na tsawon sa’o’i. Ba a gano asalin abin da ya kai har sojan, wanda ke aiki tare da wani kamfanin gine-gine, ya kashe direban ba. Sai dai bayanai sun nuna lamarin ya faru ne a kusa da garin Tashar Yari da ke Ƙaramar Hukumar Makarfi ta Jihar…
Read More
Abduljabbar ya ƙalubalanci hukuncin kisa da kotu ta yanke masa

Abduljabbar ya ƙalubalanci hukuncin kisa da kotu ta yanke masa

Daga Ibrahim Hamisu, Kano Malam Abduljabbar Nasir Kabara wanda Kotu ta zartar wa da hukuncin kisa ta hanyar rataya ya ce bai gamsu da hukuncin da aka yi masa ba gaba ɗaya. Wannan na ƙunshe ne cikin wata takarda da lauyansa ya miƙa wa Babbar Kotun Jihar Kano. Cikin takardar, ya ce "Ni Abduljabbar ban gamsu da hukuncin da Kotun Shari’ar Musulunci ta Ƙofar Kudu ta yanke a kaina ba, a shari’a mai lamba CR/01/2021 da aka zartar ranar 15th Disamba, 2022, ƙarƙashin Alƙali Ibrahim Sarki Yola." Abduljabbar ya ɗaukaka ƙara zuwa Babbar Kotun jihar Kano bisa dalilin da ya…
Read More
‘Yan sandan sun cafke ‘yan bindiga 2, sun ƙwace tarin alburusai a Zamfara

‘Yan sandan sun cafke ‘yan bindiga 2, sun ƙwace tarin alburusai a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta kama wasu da ake zargin masu yi 'yan bindiga safarar makamai ne a jihar. Kakakin rundunar, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau ranar Talata. A cewarsa, abubuwan da aka ƙwato daga wajensu sun haɗa da harsashi guda 325 da kuma bindigar Ak47 guda ɗaya. “A ranar 8 ga Janairu, 2023 ne jami’an ‘yan sanda suka kama wasu ‘yan bindiga biyu, Emmanuel Emmanuel da takwararsa Nana Ibrahim a kan hanyar Gusau, Wanke zuwa Dansadau, da harsasai 325 da…
Read More
Ɗan uwan ɗan sanda ya kashe shi ya sace bindigarsa

Ɗan uwan ɗan sanda ya kashe shi ya sace bindigarsa

Wani ɗan uwan wani ɗan sanda ya harbe shi har lahira sannan ya tsare da bindigarsa ta aiki. Ɗan sandan da ke gadin wani banki ya gamu da ajalinsa a hannun ɗan uwan nasa ne a yayin da suke shirin cin abincin rana a harabar bankin da ɗan sandan yake gadi. Majiyarmu ta ce, “abin ya faru da ɗan sandan mai muƙamin kofur ne a ranar Laraba lokacin da ɗan sandan ke wanke cokulan da za su ci abinci, bayan ya bar bindigarsa a bisa benci. “Sai makashin nasa ya ɗauki bindigar ya matsa kunamar sosai inda ya ɗirka masa…
Read More
Rashe-rashen da aka yi a masana’antun finafinan Nijeriya cikin 2022 (1)

Rashe-rashen da aka yi a masana’antun finafinan Nijeriya cikin 2022 (1)

Daga AISHA ASAS Masu karatu barkanmu da haɗuwar farko a sabuwar shekara cikin wannan shafi na Nishaɗi. Barka da ganin sabuwar shekara. Muna taya masoyan Manhaja murnar ganin shekarar 2023, Allah Ya linka mana alkhairan da muka samu a baya, Ya zaunar da mu lafiya a ƙasarmu, Ya azurta mu, Ya bamu cikar burikanmu. Masu iya magana dai na cewa, waiwaye adon tafiya. Wannan ne ya sa muka yi sha'awar waiwayawa shekarar da muka take, don share fage wurin kawo maku ƙayatattun labarai da tattaunawa tsakanin Manhaja da masu ruwa da tsaki a harkar finafinai har ma da su kansu…
Read More
Rundunar soji ta yi wa manyan jami’anta sauyin wurin aiki

Rundunar soji ta yi wa manyan jami’anta sauyin wurin aiki

Daga BASHIR ISAH A ƙoƙarin da take yi na inganta sha'anin aiki da magance matsalar tsaro, Rundunar Sojin Nijeriya (NA) ta yi wa manyan jami'anta sauyin wajen aiki. Sanarwar da rundunar ta fitar ta hannun Daraktan Hulɗa da Jama'a, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu a ƙarshen mako, ta nuna Shugaban rundunar, Laftanar-Janar Faruk Yahaya ya amince da sauya wa jami'an wurin aiki. Su Manjo-Janar da Birgediya-Janar, kwamadoji da sauransu na daga cikin waɗada sauyin ya shafa. Fitattu daga ciki akwai Manjo-Janar IS Ali daga Hedikwata wanda yanzu shi ne Kwamandan Operation Haɗin Kai da dai sauransu. Sannan sabbin kwamandojin da aka naɗa…
Read More
Matar shugaban DSS ta ba da umarnin tsare Abba Gida-gida a Kano,

Matar shugaban DSS ta ba da umarnin tsare Abba Gida-gida a Kano,

Ta ba da odar kashe hadiminsa Daga WAKILINMU Mai ɗakin Shugaban hukumar tsaro na DSS na ƙasa, Aisha Bichi, ta ba da odar a tsare ɗan takarar gwamna na Jam'iyyar NNPP a Kano, Abba Yusuf, tare da hana shi shiga jirgi daga Kano zuwa Abuja a ranar Lahadi da daddare. Jaridar Daily Nigerian ta rawaito rikicin ya soma ne bayan da tawagar ɗan siyasar ta haifar da cinkoson abubuwan hawan da haifar wa Aisa tsaiko da jinkirin isa inda ya kamata a Babban Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano. Majiyoyi sun ce lamarin bai yi wa Aisha daɗi ba wanda…
Read More
An sako mamallakin tashar AIT, Dokpesi

An sako mamallakin tashar AIT, Dokpesi

Daga WAKILINMU Hukumomi a ƙasar London sun sako mu'assasin kamfanin sadarwar nan na DAAR Communications Plc, wato Cif Raymond Dokpesi, bayan tsare shi da aka yi ranar Lahadi a filin jirgin saman ƙasar. Da take tabbatar da sakin nasa cikin sanarwar da ta fitar da safiyar Litinin, hukumar kamfanin DAAR ta ce an tsare Dokpesi ɗin ne saboda wani al'amari da ya taso. “An riƙe Dokpesi na wasu sa'o'i kafin daga bisani jami'an hukumar shige da fice na Birtaniya su buga wa fasfo ɗinsa kan-sarki na shiga ƙasar. “Cif Dokpesi na godiya dangane da ƙauna da addu'o'in da aka yi…
Read More