Labarai

EFCC na farautar ɗan takarar sanatan Kano a APC, A.A Zaura kan badaƙalar miliyan N576.6

EFCC na farautar ɗan takarar sanatan Kano a APC, A.A Zaura kan badaƙalar miliyan N576.6

Daga WAKILINMU Hukumar EFCC ta ce za ta cafke ɗan takarar sanata na Kano ta tsakiya na Jam'iyyar APC, AbdulKareem AbdulSalam Zaura. EFCC na neman Zaura ta kama ne bisa zargin almundahanar Dalar Amurka miliyan 1.3, kwatankwacin miliyan N576.6. Lauyan EFCC, Ahmad Rogha ne ya bayyana haka ranar Litinin yayin da aka dawo ci gaba da sauraron shari'ar a Babbar Kotun da ke zamanta a Kano. Sai dai zaman shari'ar na wannan rana bai yiwu ba sakamakon Alƙalin kotun ya halarci wanibtaron ƙasa a wajen Kano. Lauyan hukumar ya ce, kamata ya yi ɗan takarar ya kai kansa ga hukumar…
Read More
NAF ta kashe ’yan ta’addan da ake nema ruwa-a-jallo a ƙauyukan Kaduna

NAF ta kashe ’yan ta’addan da ake nema ruwa-a-jallo a ƙauyukan Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jiragen yaƙin Rundunar Sojin Saman Nijeriya sun kawar da wasu jiga-jigan ’yan ta’addan Zamfara guda bakwai da ake nema ruwa-a-jallo. An kawar da ’yan ta’addan ne da suka yi ƙaurin suna a Jihar Kaduna sakamakon harin da jiragen yaƙin sojojin saman Nijeriya biyu suka kai musu. An tattaro cewa, waɗanda aka kashe sun haɗa da Jibrin Gurgu, Isah Jauro da Tambowal daga jihar Zamfara. Sauran da aka kawar sun haɗa da Noti, Bala, Yunusa da Burti wanda ya kasance sanannen abokin wani ɗan ta’adda da ake nema ruwa-a-jallo, Haladu Buharin Yadi. Wani jami’in leƙen asiri na…
Read More
Bayan tsaikon wata takwas, jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya fara aiki

Bayan tsaikon wata takwas, jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya fara aiki

Daga BASHIR ISAH Bayan shafe watanni takwas ba ya aiki, jirgin saƙan Abuja-Kaduna ya fara aiki a ranar Litinin. Jirgin ya dakatar da aiki ne tun wata takwas da suka gabata sakamakon harin 'yan bindiga. Manhaja ta kalato cewa, an ga fasinjoji na shiga jirgin a tashar Idu cikin tsattsauran tsro a safiyar Litinin. Sai dai ba a samu tururuwar fasinja ba kamar yadda aka saba gani a baya a lokacin da jirgin ke loadin safe a tashar ta Idu. Manhaja ta gano an ɗauki matakan tsaro da dama, ciki har da kafa kyamarorin CCTV a sassa daban-daban domin sanya…
Read More
Ɓatagari sun sake ƙona ofishin INEC a Imo

Ɓatagari sun sake ƙona ofishin INEC a Imo

*Sau bakwai ana kai wa ofishin INEC hari a cikin wata huɗi - Kwamishina Daga WAKILINMU Ɓatagari sun sake ƙona wani ofishin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ke yankin Ƙaramar Hukumar Oru ta Yamma a Jihar Imo. Bayanin faruwar hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da hukumar ta fitar ranar Lahadi ta hannun kwamishinanta, Festus Okoye. A cewar Okoye, Kwamishinan INEC na Jihar Imo, Farfesa Sylvia Uchenna Agu, ya kai rahoton harin da aka kai ofishin da misalin ƙarfe 4.00 asuba ran Lahadi. Ya ce, ɓarnar da ta auku sakamakon harin ta taƙaita ne a zauren…
Read More
‘Yan bindiga sun harbi liman, sun sace mutum da dama a masallacin Katsina

‘Yan bindiga sun harbi liman, sun sace mutum da dama a masallacin Katsina

Daga WAKILINMU Rundunar 'Yan Sanda ta Jihar Katsina ta ce, ta ceto wasu mutum shida waɗanda 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su ranar Asabar a yankin Karamar Hukumar Funtua a jihar. Ta ce waɗanda aka ceton suna daga cikin mutum 19 da aka yi garkuwa da su a lokacin da suke tsaka da sallar Issha a Masallcin ƙauyen Maigamji. Bayanan da Manhaja ta samu sun ce, kafin yin awon gaba da waɗanda suka kwashe sai da ɓarayin suka ji wa limamin masallacin da wani mutum guda rauni da harbin bindiga. Binciken Manhaja ya gano an sako biyu daga cikin…
Read More
Buhari ya kori manajan NIRSAL saboda zargin sa da almundahana

Buhari ya kori manajan NIRSAL saboda zargin sa da almundahana

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya sauke Manajan Daraktan Hukumar ba da Agajin Ibtila'i da Tallafin Noma (NIRSAL), Aliyu Abdulhameed, a kan zargin yin almundahana. Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaban qasar ya kori Abdulhameed daga aiki a yammacin ranar Alhamis 2, ga watan Disamba 2022, inda aka fatattake shi daga ofishin nasa jim kaɗan bayan nan. Abdulhameed dai ana zarginsa da laifin karkatar da wasu kuɗaɗen hukumar tun daga lokacin da aka naɗa shi muƙamin a shekarar 2015 zuwa yau. Haka zalika, rahotanni sun sake bayyana cewa, a halin yanzu tuni gwamnatin ta baza komar neman madadinsa.…
Read More
Ɗalibi Aminu ya kawo ƙarshen faɗansa da Aisha Buhari bayan ganawarsa da Shugaban Ƙasa

Ɗalibi Aminu ya kawo ƙarshen faɗansa da Aisha Buhari bayan ganawarsa da Shugaban Ƙasa

Daga BASHIR ISAH Yanzu dai ya tabbata fadan da ke tsakanin matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, da ɗalibin nan Aminu Mohammed Adamu, ya ƙare. Hakan ya biyo bayan ganawar da Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi da Aminu ɗin ne bayan da aka sako shi daga gidan maza. Aminu, wanda ɗalibi ne a Jami'ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa, ya gamu da fushin Aisha ne bayan da ya caccake ta a shafinsa na Tiwita inda ya ce ta ci kuɗin talakawa ta yi ɓul-ɓul. Lamarin da ya sanya jami'an tsaro na DSS suka bi sawun ɗalibin har makarantarsu suka…
Read More
An tallafa wa wanda lakarsa ta tsinke da miliyan N1 a Jigawa

An tallafa wa wanda lakarsa ta tsinke da miliyan N1 a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Ƙaramar Hukumar Buji a Jihar Jigawa, ta ba da tallafin Naira miliyan ɗaya ga wani matashi da ya samu matsala a lakarsa sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi kwanan baya. Tallafin ɓangare ne na ƙoƙarin da ƙaramar hukumar ke yi wajen ganin ta inganta rayuwar nakasassu da marasa lafiya a yankin. Matashin, Ahmad Karanjau, ya haɗu da tsautsayin ne a kan hanyar Abuja zuwa Benin. Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Abdullahi Sulaiman Yayari, ya tabbatar da cewa Hukumar Buji za ta ci gaba da tallafa wa Ahmad wanda a halin yanzu yake kwance…
Read More
‘Yan bindiga sun buɗe wuta cikin wani masallaci a Katsina

‘Yan bindiga sun buɗe wuta cikin wani masallaci a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina 'Yan bindiga sun yi dirar mikiya a wani masallaci dake garin Maigamji a Ƙaramar Hukumar Funtua a dai-dai lokacin da ake gabatar da Sallar Issha'i. Wani mazaunin garin ya shaida wa majiyar Manhaja cewa, da zuwan ɓarayin ana tsaka da Sallah sai suka buɗe wuta inda nan take suka harbi mutane biyu ciki har da wanda rahotanni suka ce shi ne limamin dake jan Sallar. Wanda yanzu haka suna karɓar magani a babban asibitin garin funtua. Rahotannin dai sun bayyana cewar, maharan sun yi awon gaba da mutane da dama. Harin na zuwa ne bayan…
Read More
An cafke matar da ta jefa jaririnta cikin masai a Jigawa

An cafke matar da ta jefa jaririnta cikin masai a Jigawa

Daga ABUBAKAR M TAHEER Rundunar 'Yan Sanda ta Jihar Jigawa ta sanar da kama wata mata mai suna Balaraba Shehu bayan Jefa jaririn da ta haifa a masai da niyyar binne shi. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tsurma da ke Ƙaramar Hukumar Kiyawa, Jihar Jigawa, inda aka gano jaririn aka garzaya da shi Asibitin Dutse inda a nan aka tabbatar da mutuwarsa. Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Shiisu Lawan Adam, shi ne ya sanar da hakan ga manema labarai. Ya ce, "Mun samu labarin jefar da jariri a masai inda jami'anmu suka garzaya domin bincike da kuma kama matar.…
Read More