Labarai

Sojojin Nijeriya sun fitar da jerin sunayen ’yan ta’addan da su ke nema ruwa-a-jallo

Sojojin Nijeriya sun fitar da jerin sunayen ’yan ta’addan da su ke nema ruwa-a-jallo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar Tsaron Nijeriya ta fitar da sunayen mutum 19 waɗanda ta ce ’yan ta’adda ne a ƙasar kuma tana neman su ruwa-a-jallo. A sanarwar da ta fitar ranar Litinin, rundunar ta ce, mutanen sun daɗe suna tafka ɓarna a Arewa maso Gabas, da arewa maso yamma da kuma arewa maso tsakiyar ƙasar ta Nijeriya. Ta kuma ce, duk wanda ya bayar da bayanin da ya taimaka wajen kama kowanne daga cikin mutanen za a ba shi tukwicin naira miliyan 5. Sunayen mutanen, kamar yadda daraktan yaɗa labaru na cibiyar tsaron na Nijeriya Manjo Janar Jimmy Akpor…
Read More
Shugabannin Sin da Amurka sun gana yau a Bali

Shugabannin Sin da Amurka sun gana yau a Bali

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Amurka Joe Biden, sun gana a yau Litinin, gabanin taron ƙolin ƙungiyar G20 da zai gudana a tsibirin Bali na ƙasar Indonesia. A cewar Xi Jinping, ya kamata ƙasashen biyu su waiwayi tarihi, kuma ya zama alƙiblar da za su bi a nan gaba. Ya ce yanayin da ake ciki yanzu game da dangantakar Sin da Amurka, bai dace da moriyar ƙasashen biyu da al’ummominsu ba, haka kuma bai dace da fatan al’ummar ƙasa da ƙasa ba. Kuma a matsayinsu na shugabannin manyan ƙasashe biyu, ya kamata su lalubo…
Read More
Cutar shan-inna: Zamfara za ta yi wa yara 667,623 riga-kafi

Cutar shan-inna: Zamfara za ta yi wa yara 667,623 riga-kafi

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau A matsayin wani mataki na ci gaba da bai ƙananan yara kariya daga cutar shan-ina, gwamnatin Jihar Zamfara ta ce za ta yi wa yara aƙalla 667,623 ‘yan ƙasa da shekara ɗaya da kuma shekara biyar allurar riga-kafin cutar. Shirin ba yin allurar in ji gwamnatin, zai gudana ne a tsakanin wasu ƙananan hukumomi guda bakwai. Ta kuma bayyana cewa, 125,964 daga cikin jimillar yaran'yan shekara ɗaya ne, sannan 542,669 'yan shekara biyar su za a yi wa riga-kafin. Daraktan kula da riga-kafin cututtuka na hukumar lafiya a matakin farko na jihar Zamfara, Malam Lawali…
Read More
ASUU na shirin zanga-zanga kan ƙin biyan mambobinta cikakken albashi

ASUU na shirin zanga-zanga kan ƙin biyan mambobinta cikakken albashi

Daga BASHIR ISAH Akwai yiwuwar ɗaliban jami'oin Nijeriya su sake fuskantar rashin malamai a cikin aji sakamakon shirin da Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) na hana malamai shiga aji na yi ɗaya a matsayin zanga-zangar nuna rashin jin daɗi kan matakin da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka na "babu aiki, babu albashi" a kan malaman. Rahotanni sun ce, ASUU za ta shirya zanga-zangar ne a rassanta da ke jami'o'in gwamnati a faɗin ƙasa. An ce mambobin ASUU za su yi zanga-zangar ne ta hanyar ƙin shiga azuzuwa balle kuma su karantar da ɗalibai. Ɗaya daga cikin shugannin ASUU na ƙasa ne ya…
Read More
Ɗaya daga cikin ɗaliban Yawuri da aka sace ta haihu a hannun ‘yan bindiga

Ɗaya daga cikin ɗaliban Yawuri da aka sace ta haihu a hannun ‘yan bindiga

Daga SANI AHMAD GIWA Ɗaya daga cikin ‘yan matan Kwalejin Tarayya da ke Birnin Yawuri a Jihar Kebbi da ‘yan bindiga suka sace ta haifi yaro namiji a sansanin da 'yan bindigar ke tsare da su kamar yadda jaridar PRNigeria ta ruwaito. Ɗalibar mai shekaru 16 wacce har yanzu ba a bayyana sunanta ba, ta kwashe sama da shekara ɗaya a hannun ‘yan bindigan da suka sace su a watan Yunin 2021. Iyayen ‘yan matan dai sun koka kan yadda ‘yan bindigan suka kalmashe kuɗin fansa tare da aurar da ‘ya’yansu bayan garkuwa da suka yi da su. Idan za…
Read More
‘Yan bindiga sun nemi diyyar miliyan N10 a kan gawa

‘Yan bindiga sun nemi diyyar miliyan N10 a kan gawa

Daga BASHIR ISAH 'Yan bindiga sun nemi a biya su Naira miliyan 10 kafin su miƙa gawar Obadiah Ibrahim wanda suka yi garkuwa da shi makonnin baya a Jihar Kaduna. A cewar majiya ta kusa da marigayin, tun farko sai da 'yan fashin dajin suka karɓi Naira miliyan N3 daga wajen 'yan uwa ba tare da sun sake shi ba. Wani ɗan uwan marigayin, Kefas Obadiah, ya ce tun ranar Litinin da ta gabata Allah Ya yi wa ɗan uwan nasa cikawa amma sai a ranar Alhamis aka sanar da su. Ya ce ɓarayin sun ƙi sakar musu gawar ɗan…
Read More
2023: Tinubu ya yarda gwamnatin APC ta gaza, ya roƙi ‘yan Nijeriya su sake ba su wata dama

2023: Tinubu ya yarda gwamnatin APC ta gaza, ya roƙi ‘yan Nijeriya su sake ba su wata dama

Daga BASHIR ISAH Ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin Jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya yarda cewa gwamnatin APC ta gaza, amma ya roƙi 'yan Nijeriya da kada su yi ƙasa a gwiwa dangane da gwamnatin ta APC. Tinubu ya yi wannan roƙo ne yayin da yake jawabi a wajen taron jana'izar mahaifiyar Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, Grace Akeredolu, ranar Lahadi a Majami'ar Cathedral da ke Imola a yankin Owo. Taron wanda ya samu halarcin jiga-jigan 'yan siyasa da manyan jami'an gwamnati da suka haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, gwamnoni da sauransu. A jawabinsa, Tinubu ya gode wa Allah kasancewar…
Read More
Atiku Abubakar ya ba da tallafin miliyan N50 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Hadejia

Atiku Abubakar ya ba da tallafin miliyan N50 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Hadejia

Daga ABUBAKAR M. TAHEER Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar GCON, ya bada tallafin Naira miliyan 50 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a fadar Mai Martaba Sarkin Hadejia. Cikin jawabinsa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa sun zo jajantawa masarautar Hadeja ne ganin irin asarar dukiyoyi da rayuka da aka samu sanadiyar ambaliya. Atiku ya ƙara da cewa, ya bada tallafin Naira miliyan 50 domin a raba wa waɗanda iftila'in ya shafa. Da yake jawabi, Sarkin Hadejia, Alhaji Adamu Abubakar Maje CON, ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara ta Atiku, kana ya yi kira…
Read More
Gwamnati ta shigar da sabuwar ƙara a kotu kan Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu

Gwamnati ta shigar da sabuwar ƙara a kotu kan Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ƙarkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta sake shigar da ƙarar jagoran masu fafutukar ƙasar Biyafara (IPOB) Nnamdi Kanu, kan wasu tuhume-tuhume guda bakwai da ta yi wa gyaran fuska. Rahotanni sun nuna cewa ƙarar mai lamba: FHC/ABJ/CR/383/2015 da aka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, na ƙunshe da dukkan tuhume-tuhumen da aka yi wa Kanu a baya wanda kotu ta riga ta wanke shi a kansu. Gwamnati ta sake maka Kanu a kotun ne kimanin wata ɗaya bayan da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta wanke shi daga zarge-zargen da gwamnati ta yi masa a baya.…
Read More
An sa lokacin gudanar da ƙidayar jama’a a Nijeriya

An sa lokacin gudanar da ƙidayar jama’a a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A hirar da Kwamishinan Ƙidayar Jama'a da Gidaje na Tarayya da ke Jihar Katsina, Injiniya Bala Almu Banye, ya tabbatar da cewa za a gudanar da ƙidayar jama'a a cikin watan Afrilu na shekarar 2023. Injiniya Bala Almu, wanda shi ne Zarman Katsina, ya yaba da yadda hukumar ta samu nasarar shirin na gwajin ƙidayar mutane da gidaje a shiyyar Daura. Zarman na Katsina ya kuma ce za a gudanar da shirin ƙidayar jama'a da gidaje a ko'ina a cikin Nijeriya a watan Afrilu na shekarar 2023. Ya kuma gode wa Shugaban Nijeriya, Muhammadu…
Read More