Labarai

Buhari ya amince da ƙarin albashi wa ma’aikatan shari’a

Buhari ya amince da ƙarin albashi wa ma’aikatan shari’a

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya amince tare da ba da umarnin gaggawa game da aiwatar da ƙarin albashi ga ma'aikatan fannin shari'a. Buhari ya bayyana haka ne sa'ilin da yake jawabi a wajen bikin buɗe wani sashe na Makarantar Lauyoyi a Fatakwal. Hadimin Babban Lauyan Ƙasa kan sha'anin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Dakta Umar Gwandu, shi ne ya bayyana haka. Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, SAN, shi ne ya wakilci Buhari a wajen taron. A cewar jaridar Punch, Buhari ya buƙaci Hukumar Tara Kuɗin Shiga da Rabawa da kuma Ministan Shari'a da…
Read More
Tinubu ya warware rikicin shugabanci da ya dabaibaye ‘yan Arewa mazauna Legas

Tinubu ya warware rikicin shugabanci da ya dabaibaye ‘yan Arewa mazauna Legas

Daga WAKILINMU Ɗan takarar Jam'iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas, Sanata Ahmed Bola Tinubu, ya warware matsalar shugabanci da ta kunno kai kuma ta dabaibaye al'ummar Arewa mazauna Birnin Ikko, wato Legas. Asiwaju Bola Tinubu ya kawo ƙarshen rikicin ne a ranar Juma'a, 18 ga Nuwamba, 2022, bayan da ya amince da rahoton kwamitin da ya kafa ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da Alhaji Lawal Abbas Garba a matsayin Sakataren Kwamitin. A yanzu an amince da Alhaji Aminu Dogara Yaro a matsayin Sarkin Hausawan Jihar Legas, yayin da Dr. Mohammad Banbado zai cigaba da kasancewa…
Read More
2023: Duk jihar da rikicin siyasa ya tashi laifin gwamnoni ne – Mathew Kukah

2023: Duk jihar da rikicin siyasa ya tashi laifin gwamnoni ne – Mathew Kukah

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Limamin Ɗariƙar Cocin Katolika na Sakkwato, Mathew Kukah, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya cewa su ɗora laifin ɓarkewar rikice-rikicen siyasa a kan gwamnonin jihohi. Ya ce akasari duk rikicin siyasar da ya tashi da wanda zai tashi kafin nan da zaɓen 2023, duk gwamnonin jihohi ne musabbabinsu. Kukah ya yi wannan tsokaci a cikin wata hira da gidan talabijin na Arise TV ya yi da shi a ranar Talata. Ya ce wasu gwamnonin jihohi ƙiri-ƙiri su na hana jam’iyyun siyasa yin amfani wuraren taruka mallakar jihohi, lamarin da faston ya ce hakan…
Read More
Gwamna Buni ya tallafa wa marayu 200 da Naira 50,000 kowanne

Gwamna Buni ya tallafa wa marayu 200 da Naira 50,000 kowanne

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya umurci Ma’aikatar Ƙirƙiro Hanyoyin Tattalin Arziki da Ayyuka ta bai wa zawarawa 400 tallafin dogaro da kai. Gwamnan ya bayar da wannan umarnin ne a ranar Asabar a lokacin da ya karɓi baƙuncin marayu 200 daga ƙananan hukumomi 17 dake faɗin jihar. Bugu da ƙari kuma, gwamnan ya tallafa wa kowane maraya ɗaya daga cikin adadin marayu 200 da kyautar Naira 50,000, sannan kuma shaidar da cewa sun cancanci kulawar gwamnati da sauran al’umma baki ɗaya. Ya ce ya zama dole a tallafa musu tare da bai wa…
Read More
Ya zama dole Gwamnatin Tarayya ta bunqasa kiwo a Nijeriya – Sanata Lawan

Ya zama dole Gwamnatin Tarayya ta bunqasa kiwo a Nijeriya – Sanata Lawan

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya sha alwashin cewa zauren majalisar dattawan Nijeriya zai yi ƙoƙarin tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa harkokin kiwon dabbobi a ƙasar nan a matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan ci gaban tattalin arzikin ƙasar nan. Sanata Lawan ya sanar da hakan a ƙarshen mako, a sa'ilin da yake ƙaddamar da allurar rigakafi ga dabbobi kyauta a qauyen Jajuwa da ke ƙaramar hukumar Jakusko a jihar Yobe; shirin da Gidauniyar SAIL Foundation a ƙarƙashin sa ke ɗaukar nauyin gudanar da shi tun shekarar 2018,…
Read More
Yawan al’ummar Nijeriya kadara ce ga ƙasa – Isa Kwarra

Yawan al’ummar Nijeriya kadara ce ga ƙasa – Isa Kwarra

Daga BASHIR ISAH Hukumar Kula da Yawan Al'umma ta Ƙasa (NPC), ta jaddada ƙudirinta na tattalin yawan jama'ar Nijeriya wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiyasin ya kai sama da mutum miliyan 216. Hukumar ta ce za a yi tattalin yawan al'ummar ne domin tabbatar da fannin tattalin arziki mai inganci da cigaba mai ɗorewa. Wannan na zuwa ne biyo bayan rahoton da Sashen Lura da Tattalin Arziki da Zamantakewa na MƊD ya fitar ranar Talata, inda ya ce yanzu yawan al'ummar duniya ya kai mutum biliyan takwas. Shugaban NPC, Malam Nasir lsa Kwarra ya ce, yawan al'umma da Nijeriya…
Read More
Ɗan Majalisa ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da yaƙin neman zaɓen Tinubu

Ɗan Majalisa ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da yaƙin neman zaɓen Tinubu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Legas mai wakiltar mazaɓar Mushin II, Sobur Olayiwola Olawale ya rasu. Olawale wanda aka fi sani da Omititi, na cikin ’yan siyasar da suka halarci taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen dan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu a Jos, babban birnin Jihar Filato. Rahotanni sun bayyana cewa, marigayin ya yanke jiki ya faɗi a wajen taron kuma daga bisani ya ce ga garinku nan.
Read More
Nijeriya ta zama ta shida a jerin ƙasashe mafi yawan al’umma – MƊD

Nijeriya ta zama ta shida a jerin ƙasashe mafi yawan al’umma – MƊD

*Yayin da yawan al'ummar duniya ya kai biliyan takwas Daga BASHIR ISAH A halin da ake ciki, Nijeriya ta zama ƙasa ta shida daga jerin ƙasashe mafi yawan al'umma a faɗin duniya. Wannan ya biyo bayan hasashen da Sashen Lura da Sha'anin Tattalin Arziki da Zamantakewa na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kan cewa, yawan al'ummar ƙasar ya kai miliyan 216. MƊD ta bayyana hakan ne ranar Talata albarkacin bikin Ranar Yawan Alumma ta Duniya na bana. A cewar MƊD kawo yanzu, a ƙiyasce yawan al'ummar duniya ya kai mutum biliyan takwas. Rahoton Majalisar ya nuna hasashen da aka yi…
Read More
Magidanci ya daɓa wa surukinsa kwalba

Magidanci ya daɓa wa surukinsa kwalba

An gurfanar da wani magidanci a gaban wata Kotun Majistare mai zamanta a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, kan zargin daɓa wa surukinsa kwalba a kai. Lauyan mai gabatar da ƙara, Sufeta Evelyn Motim, ta faɗa wa kotun cewa, mai kare kansa ya aikata laifin ne ranar 30 ga watan Oktoba a yankin Abule Ijaye da ke jihar. Ta ce, wanda ake zargin ya daɓa wa mahaifin matarsa wata fasasshiyar kwalba a kai. Ta ce, surukin ya gamu da iftila’in ne bayan da aka gayyato shi don ya zo ya sasanta matsalar aure, daga nan wanda ake zargi ya haɗa…
Read More
An cafke makaho ɗan Nijar da safarar miyagun ƙwayoyi

An cafke makaho ɗan Nijar da safarar miyagun ƙwayoyi

Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi a Nijeriya (NDLEA) ta sanar da kama wani mutum makaho da ɗansa yayin da suke ƙoƙarin safarar tabar wiwi da miyagun ƙwayoyi. Cikin wani saƙo da NDLEA ta wallafa a shafinta na Facebook ɗauke da sa hannun Darektan yaɗa labaranta, Femi Babafemi ta ce, an kama mutanen biyu ne a hanyar Malumfashi-Zaria a Jihar Katsina. NDLEA ta ce, an mahaifin wanda shi ne makahon mai shekaru 52 da ɗansa mai shekaru 30, ɗauke da kilo 20.5 na tabar wiwi da kuma gram 10 na exol-5. NDLEA ta bayyana cewa asalin mutanen…
Read More