Labarai

Sama da yara miliyan ɗaya za a yi wa allurar rigakafi a Zamfara

Sama da yara miliyan ɗaya za a yi wa allurar rigakafi a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Aqalla ƙananan yara 1,123, 143 miliyan ne ake sa ran za a yi wa allurar rigakafin da za a yi nan gaba a faɗin Jihar Zamfara. Mataimakin gwamnan jihar Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana haka a wani taron kwamitin yaƙi da cuttuttaka da aka gudanar a ofishin sa ranar Talata. Mataimakin gwamnan wanda shi ne shugaban kwamitin da ke kula da harkokin rigakafi a jihar ya ce, aikin rigakafin zai mayar da hankali ne kan cutar Ƙyanda, rigakafin cutar Sanƙarau, ƙarin bitamin A, takardar shaidar haihuwa da aikin rigakafin COVID-19. Ya bayyana cewa za…
Read More
Canja takardun kuɗi: EFCC za ta sa zare da masu ɓoye Naira

Canja takardun kuɗi: EFCC za ta sa zare da masu ɓoye Naira

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar hana cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati  (EFCC), ta lashi takobin sanya ƙafar wando guda da dukkan masu ɓoye Naira, a yayin da CBN ta samu sahalewar shugaban ƙasa Buhari a kan canza fasalin wasu daga cikin takardun Nairorin Nijeriya.   Idan za a iya tunawa, Babban Banki Nijeriya (CBN) bayan samun sahalewar Buhari ya bayyana cewa, nan da 15 ga watan Disamba za ta fitar Da sabbin takardun Nairori waɗanda aka canza wa fasali. Takardun kuɗin da za a sauya wa fasalin sun haɗa da, takardun Naira 200, Naira 500,…
Read More
Masana sun ɗora laifin ambaliya kan al’umma da kuma watsi da gargaɗin NiMeT

Masana sun ɗora laifin ambaliya kan al’umma da kuma watsi da gargaɗin NiMeT

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu ƙwararru masu fafutukar kare muhalli sun ɗora matsalar ambaliya kan halayyar wasu 'yan ƙasa da ke toshe magudanan ruwa da bola, gami da gini a kan hanyoyin ruwa, lamarin da ke haifar da ta’azzara ambaliya a cikin al’umma da garuruwa. Ƙwararru a wani bincike da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya gudanar a yankin Kudu maso Kudu sun kuma ɗora laifin a kan rashin kula da shawarar gwamnati a kan lamarin. Sun yi zargin cewa gwamnati ta yi watsi da hasashen ambaliyar ruwa da Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya, NiMeT, da Hukumar…
Read More
Kotu ta sake ƙwace wasu manyan gidaje na Diezani a Abuja

Kotu ta sake ƙwace wasu manyan gidaje na Diezani a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta bayar da umarnin kammala ƙwace maka-makan gidaje na biliyoyin nairori, waɗanda tsohuwar Ministar Harkokin Fetur, Diezani Allison-Madueke ta mallaka a Abuja. Gidajen waɗanda kotun Babban Mai Shari’a Mobolaji Olajuwon ta ƙwace, sun haɗa da katafaren gida mai Lamba 1854, kan Titin Mohammed Mahashir, da ke Aso Drive. An ƙiyasta gidan zai kai Dala miliyan 2,674,418. Sai kuma gida mai Lamba 6 da ke Aso Drive a Asokoro, wanda tafkeken gidan alfarma ne na gani na faɗa, wanda Hukumar EFCC ta…
Read More
2023: Zaɓen Nijeriya zai iya shafar Afrika ta Yamma – ECOWAS

2023: Zaɓen Nijeriya zai iya shafar Afrika ta Yamma – ECOWAS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar ECOWAS ta bayyana cewa zaɓen da Nijeriya za ta gudanar cikin 2023 zai iya shafar Afrika ta Yamma. Tawagar Gani Da Ido ta ECOWAS wadda ta zo Nijeriya domin ganin irin ci gaban da ake samu dangane da shirye-shiryen zaɓen 2023 ce ta bayyana cewa yanayin sakamakon zaɓen zai iya shafar Afrika ta Yamma. Sun bayyana haka a lokacin da su ka kai wa Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ziyara, ranar Litinin, a Abuja. Tawagar na ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Hukumar Zaven Ghana, Kwadwo Afadi-Gyan. Mai magana a madadin tawagar, kuma Daraktan Harkokin…
Read More
Ya hallaka mahaifinsa kan amfanin gona

Ya hallaka mahaifinsa kan amfanin gona

Wani matashi ɗan ƙasa da shekaru 20 ya hallaka mahaifinsa kan saɓani da suka samu a tsakaninsu a gona. Yaron ya yi wa tsohon kisan gilla ne saboda dattijojin ya yi masa tambaya a gonar a ranar Juma’a da yamma a kauyen Issele-Uku da ke Karamar Hukumar Aniocha, Jihar Delta. Wani ganau a kauyen ya ce, “Matashin ya kashe mahaifinsa ne bayan dattijon ya bi shi gona yana tambayar dalilin da ya girbe masa amfanin gona ba da izininsa ba. “Tambayar da tsohon ya yi masa a gonar kan dalilin girbe masa amfanin gona ba da izini ba ne ya…
Read More
Budurwa ta kashe saurayinta a Nasarawa

Budurwa ta kashe saurayinta a Nasarawa

An damƙe wata mata mai shekara 30 kan zargin yin amfani da wuƙa ta kashe saurayinta a yankin Maraba da ke Jihar Nasarawa. Kakakin ’Yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce, matar ta kashe saurayin nata ne bayan faɗa ya kaure a tsakaninsu. Ya ce, yanzu, “tana hannu kuma an kwace wuƙar da ta yi amfani da ita wajen aikata kisan, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, Adesina Soyemi. A cewarsa, sun damƙe matar ne bayan ta yi ɗanyen aiki a Ungwan Gwari, Karamar Hukumar Karu ta jihar. “An miƙa ta ga Babban Sashen Binciken Manyan Laifuka da…
Read More
Matawalle ya halasta tarurrukan siyasa, ya sake buɗe ƙananan hukumomi uku

Matawalle ya halasta tarurrukan siyasa, ya sake buɗe ƙananan hukumomi uku

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara ta ɗage dokar haramta tarurrukan siyas da ta kafa a jihar. Haka nan, ta janye dokar hana zirga-zirgar da ta kafa a yankunan ƙananan hukumomin Gummi da Anka da kuma Bukkuyum a jihar. Bayanin hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa labarai na Jihar, Ibrahim Dosara, ya fitar a Gusau ranar Litinin. A cewar Dosara, gwamnati ta janye dokokin ne bayan gansuwar da ta yi da rahoton tsaron jihar da ta samu. Daga nan, sanarwar ta buƙaci alummar jihar su ci gaba da gudanar da harkokinsu ta hanyar kiyaye doka…
Read More
ICPC ta rufe jami’o’i 68 na bogi a Nijeriya

ICPC ta rufe jami’o’i 68 na bogi a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar da ke yaƙi da almundahana da sauran lafukan da suka shafi cin hanci ta ICPC a Nijeriya, ta ce, ta rufe jami'o'i da kwalejin kimiyya da fasaha da ke bayar da shaidar digiri na bogi 62 a faɗin ƙasar. Hukumar ta ce, wannan abu ne da ke neman zama ruwan dare a Nijeriya, domin kuwa babu wata jiha a faɗin ƙasar da ba a samu irin wannan makarantu ba a cikinta. Cikin shekaru da ICPC ta kwashe tana gudanar da wani bincike a ɓoye, ta kai ga gano adadin makarantu da suka haɗa da jami'o'i…
Read More
Barazanar hari: DSS ta buƙaci a kwantar da hankali

Barazanar hari: DSS ta buƙaci a kwantar da hankali

Daga BASHIR ISAH Biyo bayan sanarwar barazanar harin da Ofishin Jakadancin Amurka a Abuja ya fitar, hukumar tsaro ta DSS ta bukaci jama'a kowa ya kwantar da hankalinsa. Cikin sanarwar da mai magana da yawun DSS ya fitar a ranar Lahadi, Dr. Peter Afunanya, ya ce an tuntube su daga sassa da dama dangane da sanarwar barazanar tsaron da Ofishin Jakadancin Amurka ya fitar. A ranar Lahdi Ofishin Jakadancin Amurka da takwaransa na Birtaniya da ke Abuja, suka fitar da sanarwar falkarwa kan yiwuwar kai hare-hare a Abuja, babban birnin ƙasar. Lamarin da ya sanya ofisoshin biyu suka yanke shawarar…
Read More