Labarai

Barazanar hari: Amurka ta gargaɗi ‘ya’yanta mazauna Abuja

Barazanar hari: Amurka ta gargaɗi ‘ya’yanta mazauna Abuja

Daga BASHIR ISAH Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja, ya gargaɗi 'yan Amurka mazauna birnin kan yiwuwar kai hare-hare a sassa daban-daban. Gargaɗin na ƙunshe ne cikin saƙon da ofishin ya aika wa Amurkawa mazauna Najeriya mai ɗauke da kwanan wata 23 ga Oktoba wanda jaridar Neptune Prime ta samu gani. Saƙon ya nuna hare-haren ka iya shafar wurare da dama, don haka ofishin ya ce zai taƙaita harkokinsa har sai abin da Allah Ya yi. Daga nan, ofishin ya bai wa Amurkawa mazauna Najeriya shawarar kare kansu ta hanyar taƙaita tafiye-tafiye, guje wa shiga cinkison jama'a, tabbatar da cajin…
Read More
Ranar Litinin za a koma karatu a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya

Ranar Litinin za a koma karatu a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya

Daga MOH'D BELLO HABIB a Zariya Mahukantar Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya sun sanar da komawa harkokin karatu a jami'ar ranar Litinin mai zuwa, wato 24 ga watan nan da muke ciki sakamakon janye yaji aikin da Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Ƙasa ta tsunduma a ciki har na tsawon watanni takwas. Wannan na ƙunshe ne cikin wani ɗab'i na musamman da sashin al'amuran jama'a ta wallafa kuma aka raba wa manema labarai shekaranjiya. Sanarwar ta ce mahukantar jami'ar sun cimma matsaya ne sakamakon taron gaggawa na Majalisar Ƙolin Jami'ar ta yi ranar Laraba 19 ga wannnan watan. Sanarwa ta ci…
Read More
Matashi ya bada kwangilar kashe mahaifinsa a Yobe

Matashi ya bada kwangilar kashe mahaifinsa a Yobe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar 'yan sandan Jihar Yobe a yau Laraba ta tabbatar da cafke wani matashi mai suna Yahaya Sai’du, ɗan shekaru 20 da haihuwa, wanda ake zargi da bada kwangilar kashe mahaifinsa, Saidu Oroh. Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, ya shaida wa manema labarai a Damaturu cewa an kama wanda ake zargin ne a Gujba, a ranar Litinin. Ya ce wanda ake zargin ya ɗauki hayar wasu mahara uku da suka harbe Oroh har lahira a gidansa da ke ƙauyen Pompom, a ranar 20 ga watan Agusta. “Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya…
Read More
EndSars: An gudanar da zanga-zangar tunawa da kisan Lekki a Legas

EndSars: An gudanar da zanga-zangar tunawa da kisan Lekki a Legas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A jiya Alhamis ne wasu ɗaruruwan mutane suka gudanar da zanga-zangar jimamin tunawa da kashe 'yan uwansu da suke zargin jam'ian tsaro sun yi a Ƙofar Lekki shekaru biyu da suka gabata a zanga-zangar ƙin jinin 'yan sandan SARS. Sai dai jami’an rundunar 'yan sandan jihar ta Legas sun ta harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar da nufin daƙile shirinsu. Masu zanga-zangar dai sun yi tattaki ne a kan ƙofar a wani ɓangare na bukukuwan tunawa da zagayowar ranar, an ce sun yi arangama da 'yan sandan da ke ɗauke da makamai da aka…
Read More
Kotu ta bada umarnin bincikar shugabannin hukumomin tsara birane da na kadarorin Gwamnatin Kano

Kotu ta bada umarnin bincikar shugabannin hukumomin tsara birane da na kadarorin Gwamnatin Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Wata babbar kotu a Jihar Kano ta bai wa kwamishinan 'yan sandan jihar umurnin su binciki Shugaban Hukumar Tsara Birane, Abdulwahab da na Kula da Kadarorin Gwamnati na Jihar Jibrilla Muhammad bisa zargin da ake musu na ruguje wa 'yan kasuwar Bampai shagunansu da yin awon gaba da kayayyakinsu ba tare da sahalewar doka ba. Lauyan 'yan kasuwar Barista Abba Hikima Fagge ya bayyana hakan yayin da yake ƙarin haske ga manema labarai, inda ya ce wannan ya biyo bayan ƙunshin tuhuma da suka kai wa kotun. Ya ce kotun ta baiwa kwamishinan 'yan sanda…
Read More
Makarantar Almumtaz ta yi bikin yaye ɗaliban ta karo na biyar

Makarantar Almumtaz ta yi bikin yaye ɗaliban ta karo na biyar

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Makarantar Al’mumtaz dake kusa da masallacin Idi dake kan tsohuwar hanyar Nasarawa a garin Keffi, Jihar Nasarawa, ta yi bikin yaye ɗalibanta da suka kammala karatun Alƙur’ani da na zamani karo na 5 tare da karrama su da ba su kyaututtuka da sauransu.  Bikin wanda aka gudanar a harabar makarantar ya samu halarcin iyayen ɗaliban da ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya da sauran shugabanni a duka matakai.  A jawabin shugaban makarantar kuma Darakta Dr. Musa Ahmad Isa ya faro ne da bayyana taƙaitaccen tarihin makarantar ta Al’mumtaz wanda a cewarsa aka kafa ne da…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin sakin Nnamdi Kanu

Gwamnatin Tarayya ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin sakin Nnamdi Kanu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Biyo bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, wacce ta saki jagoran ƙungiyar ’yan ta'addan Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, Gwamnatin Tarayya ta ɗaukaka ƙara a gaban Kotun Ƙoli. A ɗaukaka ƙarar da aka shigar a ranar 19 ga Oktoba, 2022, a gaban Kotun Ƙoli ta ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya (AGF), Gwamnatin Tarayya ta buƙaci Kotun Ƙoli ta dakatar da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a ranar 13 ga Oktoba, 2022, wanda ya saki shugaban na ƙungiyar 'yan awaren Biyafara. Gwamnatin Tarayya a cikin shaɗarar ɗaukaka ƙara ta bakwai, ta yi Allah-wadai da matakin da ƙaramar…
Read More
Nijeriya na da kyakkyawar makoma a hannunmu – Buhari

Nijeriya na da kyakkyawar makoma a hannunmu – Buhari

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, duk da ƙalubalan tattalin arziki da duniya ke fuskanta da faɗuwar farashin mai wanda hakan ya haifar wa ƙasa ƙarancin kuɗin shiga, gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin ɗora Nijeriya kan turbar cigaba. Buhari ya ce duba da irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu ƙarƙashin Jam'iyyar APC, jami'yyar na da dukkan dalilan da za su ta yin alfahari da hakan. Shugaban ya bayyana haka ne a Juma'ar da ta gabata, sa'ilin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe Shugaban Ƙasa (PCC) da sauran tsare-tsaren yaƙin neman zeɓe na…
Read More
Hukumar NDLEA ta cafke mace mai goyo, mai juna-biyu, da wasu 26 da muggan ƙwayoyi

Hukumar NDLEA ta cafke mace mai goyo, mai juna-biyu, da wasu 26 da muggan ƙwayoyi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Hukumar yaƙi da sha, da fatauci da miyagun ƙwayoyi ta NDLEA ta bayyana cewar, ta yi nasarar cafke mutane 28, cikin su har da mace mai juna biyu, da wata mai goyo, haɗi da wani ɗalibin jami’a ɗan aji biyu a makaranta da buhunan tabar wiwi waɗanda aka ƙiyasta nauyin su akan kilogiram dubu tara da ɗari huɗu da talatin da bakwai, da ɗigo shida haɗi da ƙwayoyi opioids guda 138, 053, da ma wasu ƙwayoyin daban-daban. A cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Lahdi da ta gabata, mai magana da yawun hukumar,…
Read More
Likitocin asibitin ATBU sun duba lafiyar direbobi 180 a Yankari Express

Likitocin asibitin ATBU sun duba lafiyar direbobi 180 a Yankari Express

Daga MU'AZU HARDAWA a Bauchi A ƙoƙarin su na tallafa wa direbobi da ma'aikatan kamfanin sufuri na Yankari Express, da ke Bauchi, ƙwararrun likitoci kan harkar ido sun duba mutane 180 a ƙarƙashin shirin bikin ranar gani ta duniya wato World Sight Day na Majalisar Ɗinkin Duniya wanda ke kasancewa a ranar kowace Alhamis ta biyu a cikin watan Oktoba, inda a bana ya kasance ranar 13 ga Oktoba. Likitoci daga Asibitin Koyarwa na Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi sun duba lafiyar idon direbobin kamfanin sufara na Yankari Express inda suka ba mutane 90 tabarau da magani wa…
Read More