Labarai

‘Yan barandan siyasa sun lakaɗa wa shugaban ‘yan jarida duka a Zamfara

‘Yan barandan siyasa sun lakaɗa wa shugaban ‘yan jarida duka a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau A ranar Alhamis wasu ‘yan bangar siyasa suka lakaɗa wa Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Zamfara, Kwamred Ibrahim Musa Maizare, dukan tsiya tare da yin barazana ga rayuwar ‘yan jarida a jihar. ’Yan barandan sun daki Maizare ne bayan da ya buƙaci su dakatar da aikin gyaran wani shago daga rukunin shaguna mallakar NUJ da ke sakatariyar ƙungiyar wanda suke amfani da shi a matsayin ofishin yaƙin neman zaɓe. A nan aka ce ma'aikatan suna bijire wa hanin da Maizare yi musu saboda a cewarsu, wani ɗan siyas ne ya ba…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Buhari ya tsige shugaban hukumar NDDC

Da Ɗumi-ɗumi: Buhari ya tsige shugaban hukumar NDDC

Daga BASHIR ISAH A ranar Alhamis Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tsige shugaban Hukumar Bunƙasa Yankin Neja Delta (NDDC), Effiong Akwa. Sanarwar da ta fito daga hannun mai magana da yawun Ma'aikatar Kula da Harkokin Yankin Neja Delta, Patricia Deworitshe, ta ce, tsige Akwa da Buhari ya yi ya soma aiki ne daga ranar 20 ga Oktoba. Sanarwar ta kara da cewa, an nada Mr Akwa shugaban NDDC ne na wucin-gadi na wa'adin lokacin da za a kammala binciken harkokin hukumar, don haka kammala binciken na nuni riƙon da aka bai Akwa ya zo ƙarshe kenan. A cewar sanarwar, “Shugaba…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Shugaban Majalisar Ekiti, Hon. Funminiyi Afuye ya kwanta dama

Da Ɗumi-ɗumi: Shugaban Majalisar Ekiti, Hon. Funminiyi Afuye ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH Wata majiya mai tushe daga Jam'iyyar APC na Jihar Ekiti ya shaida wa jaridar New Telegraph cewa: “Mun rasa Shugaban Majalisar Jihar Ekiti sakamakon bugun zuciya.” Haka nan, Gwamnatin Jihar Ekiti ta ba da sanarwar rasuwar Shugaban Majalisar cikin sanarwar da ta fitar ta hannun Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamnan Jihar, Mr. Yinka Oyebode. Sanarwar ta ce Afuye ya rasu ne da yammacin Laraba a Asibitin Koyarwa na Jihar (EKSUTH),  da ke Ado-Ekiti babban birnin jihar sakamakon fama da bugun zuciya. Marigayin ya bar duniya yana da shekara 66. Kafin rsuwarsa, tsohon Kwamishina ne a Ma'aikatar Yaɗa…
Read More
Boko Haram, ISWAP sun mamaye Zamfara – Dr Shinkafi

Boko Haram, ISWAP sun mamaye Zamfara – Dr Shinkafi

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da cewa, umarnin da gwamnatin jihar ta bayar na dakatar da duk wasu harkokin siyasa a jihar, ta yi ne sakamakon bayanan sirrin da ta samu wanda ya nuna wasu 'yan ƙungiyar Boko Haram da ISWAP na lardin yammacin Afrika, sun mamaye wasu sassan jihar. Shugaban kwamitin zartar da hukunci a kan ayyukan ta'addanci a jihar, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Gusau ran Talata. Shinkafi wanda shi ne tsohon sakataren Jam’iyyar APGA na ƙasa, ya bayyana cewa matakan da gwamnan jihar…
Read More
Kotu ta raba auren shekara ɗaya saboda rashin soyayya

Kotu ta raba auren shekara ɗaya saboda rashin soyayya

Wata Kotun Shari’ar Musulinci da ke Ilorin, Jihar Kwara ta raba wasu ma’aurata da aka ɗaura aurensu watanni 12 da suka gabata. Alƙalin kotun, Abdulƙadir Umar, ya ce, matar mai suna Roimat Qodir ta roƙi kotun ta kashe aurenta da mijinta Abdulƙadir AbdulRazak, saboda ba ta sonsa. Bayan alaalin ya tambaye ta ko tana da juna biyu, ta musanta hakan. Shi ma dai mijin ya bayyana wa alƙalin cewa ya amince da buƙatar matar, kuma ko a lokacin ta so za ta iya tafiya. A ƙarshe dai kotun ta raba auren, tare da bai wa matar umarnin yin iddar watanni…
Read More
Ya harbe ƙaninsa yayin gwada maganin bindiga

Ya harbe ƙaninsa yayin gwada maganin bindiga

Wani matashi ya harbe ƙaninsa mai shekaru 12 yayin gwada maganin bindiga a Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara. Wanda lamarin ya shafa dai ƙanin wani mafarauci ne da suka mallaki wani sabon maganin bindiga kuma suka yi yunƙurin tabbatar da ingancinsa. Lamarin a cewar rahotanni ya faru ne a makon da ya gabata, inda wanda ya yi aika-aikar tuni ya arce ya bazama cikin daji bayan lamarin ya afku. Da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Litinin, Jami’in Hulɗa da Al’umma na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce, Kwamishina ’Yan sanda Paul Odama ya ba…
Read More
Matawalle ya ba da haƙuri kan rufe kafofin yaɗa labarai

Matawalle ya ba da haƙuri kan rufe kafofin yaɗa labarai

Daga WAKILINMU Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ba da hakuri tare neman afuwa kan matakin rufe wasu kafafen yada labarai a jihar. Kafofin yada labaran da lamarin ya shafa sun hada da tashar NTA da gidan Pride FM da ke Gusau, baki dayansu mallakar mallakin Gwamnatin Tarayya. Sauran su ne tashar Gamji TV da Gamji FM da Al-umma TV wadanda suke masu zaman kansu. Sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya fitar, ta nuna kafofin da aka rufen sun saɓa wa dokar jihar da ma ta aikin jarida, shi ya sa aka ɗauki matakin rufe su.…
Read More
Ba mu da kuɗin motar koma wa jami’o’inmu, inji Malaman jami’a

Ba mu da kuɗin motar koma wa jami’o’inmu, inji Malaman jami’a

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU), ta nuna damuwarta kan rashin biyan mambobinta albashinsu na tsawon wata takwas, wanda a cewarta hakan ya sa malaman rasa kuɗin motar da za su koma bakin aiki bayan janye yajin aikin da suka yi. Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugaban ASUU na Ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, a lokacin da yake jawabi dangane da batun janye yakin aikin da suka yi a tashar Talabijin ɗin Channels ranar Lahadi. Idan dai za a iya tunawa, Manhaja ta rawaito batun janye yajin aikin da ASUU ta yi a Juma'ar da ta gabata bayan…
Read More
Rufe kafofin yaɗa labarai: Ka hanzarta gyara kuskuren da ka aikata, kiran NUJ ga Matawalle

Rufe kafofin yaɗa labarai: Ka hanzarta gyara kuskuren da ka aikata, kiran NUJ ga Matawalle

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), ta yi kira ga Majalisar Tsaron Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Bello Muhammad Matawalle, da ta janye matakin da ta ɗauka na rufe wasu kafofin yaɗa labarai a jihar. Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi, ƙungiyar ta ce an jiyo Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, lbrahim Dosara na cewa, kafafen da lamarin ya shafa su ne; Tashar NTA da Gamji TV da Umma TV da kuma Pride FM. A cewarsa, an ɗauki matakin da aka ɗauka a kan kafafen ne saboda saɓa dokar aiki da suka yi, inda…
Read More
Garƙame kafofin yaɗa labarai: BON ta yi tir da matakin Matawalle

Garƙame kafofin yaɗa labarai: BON ta yi tir da matakin Matawalle

Daga BASHIR ISAH Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta Nijeriya (BON), ta nuna kaɗuwarta da kuma Allah wadai da matakin da Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ɗauka na garƙame wasu kafofin yaɗa labarai huɗu mallakar gwamnati da masu zaman kansu a jihar. Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi mai ɗauke da sa hannun Sakatarenta, Dr. Yemisi Bamgbose, kuma a matsayin martani ga matakin na Matawallen ya ɗauka, BON ta ce a dokance Gwamnan ba shi da ikon da zai ba da umarnin rufe kafafen, kuma hakan da ya yi tamkar cin mutunci ne da kuma yin…
Read More