Labarai

Jami’an tsaro sun ceto mutum 16 da aka sace a Jihar Kogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani atisayen jami'an tsaro na haɗaka da rundunar sojoji ta jagoranta ya yi sanadiyyar sako baki ɗaya mutane 16 da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Ofu ta Jihar Kogi. A ranar Lahadi, 9 ga Agusta 2026 ne aka sace mutanen bayan 'yan bindigar sun farmaki mutanen da ke zirga-zirga a yankin titinan Ojuwo zuwa Ajengo zuwa Memarebo da Ojiwo zuwa Itobe. Bayan samun wani bayanin sirri da ke nuna cewa an garzaya da mutanen ta yankin ƙauyen Adumu a Ƙaramar Hukumar Dekina, dakarun Bataliya ta 21 da haɗin-gwiwar…
Read More

DSS ta sako kafinta bayan gano ba shi da hannu a sace ‘yan makarantar Oyo, ta biya diyyar miliyan N3

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta saki wani kafinta mai suna Mustapha Marwana, wanda aka kama bisa zargin sa da hannu a garkuwa da halaka ɗalibai da malaman wasu makarantu a yankin Oriire da ke Jihar Oyo. Darakta Janar na hukumar, Tosin Ajayi ne ya bayar da umarnin sakin nasa bayan masu bincike sun wanke shi daga dukkan wani abin da yake alaƙanta shi da harin. Wata majiyar tsaro da ke da kusanci da batun ta ce kwamitin binciken DSS ya gudanar da bincike mai zurfi akan zargin Marwana da hannu al'amarin kana…
Read More

Sojoji sun ƙwato makamai bayan daƙile harin ISWAP a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro na Atisayen Haɗin Kai a Arewa maso Gabashin Nijeriya, sun yi nasarar halaka wasu 'yan ta'adda a lokacin da suka daƙile wani hari da mayaƙan ISWAP suka yi yunƙurin ƙaddamarwa a sansanin sojoji da ke yankin Gajiram a Ƙaramar Hukumar Nganzai ta Jihar Borno. Jami'in Hulɗa da jama'a na rundunar na riƙo, Kyaftin Mohammed Goni, wanda ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin, ya ce wani adadi mai yawa na 'yan ta'adda ya ƙaddamar da mummunan farmaki a sansanin dakarun na sansanin FOB a Gajiram da…
Read More

An yi jana’izar ‘yan ƙauyen Benuwai 15 da aka halaka yayin da manoma ke biyan ‘yan bindiga tara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Asabar aka gudanar da jana'izar mutane goma sha biyar da aka halaka a ranar 28 ga watan Yuli, 2026 a yankin Ƙaramar Hukumar Otukpo da ke Jihar Benuwai. A cewar wani rahoto da AIT ya fitar, mazauna ƙauyen Efeyi-Utikpi ne suka jagoranci jana'izar, makonni bayan irin harin ya auku a ƙaramar hukumar. Rahoton ya ce, harin ya yi sanadiyyar lalata gidaje da jefa al'ummar yankin cikin ƙunci da firgici, inda jagororin jama'a suke kira ga gwamnatocin tarayya da jiha su daina taƙaice matakinsu akan yin alla-wadai tare da ɗaukar matakan samar da…
Read More

EU ta musanta yin watsi da gayyatar INEC ta neman ta sanya ido a zaɓen 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin Jakadan Majalisar Tarayyar Turai (EU) ga Nijeriya da ECOWAS, Gautier Mignot a wata sanarwa, ya bayyana cewa, rahotannin da ke yawo cewa EU ta yi watsi da gayyatar da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi mata na neman ta sanya ido a babban zaɓen 2027 da ke tafe a Nijeriya ba gaskiya ba ne kuma jita-jita ce mara asali. Mista Mignot ya tabbatar da cewa, majalisar ta sami saƙon gayyatar daga hukumar zaɓen Nijeriyar tun a watan Afrilu kuma ta bayar da amsa a kai, inda ta ce za ta…
Read More
Mutum 1,932 aka kashe cikin wata uku a Arewa maso Gabas – Majalisar Dinkin Duniya

Mutum 1,932 aka kashe cikin wata uku a Arewa maso Gabas – Majalisar Dinkin Duniya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da Daidaita Ayyukan Agaji (OCHA) ta bayyana cewa aƙalla mutum 1,932 ne suka rasa rayukansu a jihohin Borno, Adamawa da Yobe tsakanin watan Afrilu zuwa Yunin 2026, sakamakon matsalolin tsaro da suka addabi yankin. Rahoton, wanda ya fito a ƙarƙashin Binciken Hanyar Isar da Agaji na Farkon Shekarar 2026, ya nuna cewa rashin tsaro, hare-hare kan ma'aikatan agaji da kayayyakinsu, cikas na hukumomi da kuma matsanancin yanayin muhalli ne suka fi kawo tsaiko ga ayyukan jinƙai a yankin. Rahoton ya samo bayanansa ne daga ƙungiyar Aiki Kan Hanyar Isar da…
Read More
Lakurawa sun kashe soja da ‘yan sa kai biyu a Kebbi

Lakurawa sun kashe soja da ‘yan sa kai biyu a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Rahotanni daga ƙaramar hukumar Dandi sun bayyana cewa wani soja da 'yan sa kai biyu sun rasa ran su a wani artabu tsakanin su da lakurawa jiya a ƙauyen Tashar Jiba da ke kan hanyar Kamba zuwa Kangiwa. Wani mazauni garin Kamba Malam Aliyu Ibrahim ya bayyana cewa bayan samun labarin lakurawa sun kai hari a ƙauyen ne sai sojojin da 'yan sa kai da ke aiki a wannan yankin suka isa inda suka fafata da su wanda a nan ne aka ce an yi wa jami'an kwanton ɓauna aka harbe su. Ya ce duk…
Read More

Gwamnatin Kaduna ta fara raba takin zamani kyauta ga manoma 150,000

Gwamnatin Jihar Kaduna ta fara rabon takin zamani kyauta ga ƙananan manoma guda 150,000 a faɗin jihar, a wani mataki da ta ce zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona, inganta rayuwar manoma da kuma karfafa samar da isasshen abinci. An gudanar da taron rabon takin ne ta cibiyoyin karɓar taki guda 69 da aka kafa a faɗin ƙananan hukumomi 23 na jihar, inda kowace ƙaramar hukuma ke da cibiyoyi uku. Da yake duba yadda ake rabon takin a Cibiyar Karɓar Taki ta Gadan Gayan da ke Ƙaramar Hukumar Igabi, Kwamishinan Aikin Gona na jihar, Malam Murtala Dabo, ya ce…
Read More

Sojoji sun yi wa ‘yan bindiga 240 luguden wuta a hanyar zuwa Kebbi daga Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro na Bataliya ta 3 ƙarƙashin Sashe na 8 na Rundunar Sojin Nijeriya da haɗin-gwiwar jami'an Atisayen FANSAN YAMMA sun yi musayar wuta da wani dandazon 'yan bindiga a yankin iyakar jihohin Zamfara da Kebbi. Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan bindigar, waɗanda aka ƙiyasta adadinsu zai kai guda 240, sun ɗauko hanya ne daga yankin Sangeko Gap da ke Jihar Zamfara kana suka nufi birnin Makuku a Jihar Kebbi. A cewar majiyoyin tsaro, 'yan bindigar sun rabu ne kashi uku a lokacin suka tunkari yankin a wani yanayi na salon kai farmaki. Wannan…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta ƙaddamar da shirin horas da malamai 250 a Gusau

Gwamnatin Zamfara ta ƙaddamar da shirin horas da malamai 250 a Gusau

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara a yau Litinin ta ƙaddamar da shirin juyin juya hali na malamai na matsayin duniya (GSTTP), wani babban shiri na gina ƙarfi da za a horas da malamai 250, jami’an tabbatar da ingancin, da kuma masu gudanar da harkokin ilimi a faɗin jihar. Kwamishinan ma’aikatar ilimi, kimiyya da fasaha, Hon. Abdulmalik Gajam, wanda Babbar sakatariyar ma’aikatar, Hajiya Maryam Yahaya Shantali, ta wakilta ta ƙaddamar da horon a kwalejin fasaha da kimiyya ta Zamfara, ZACAS, da ke Gusau. Ta bayyana horon a matsayin mataki mai muhimmanci a tafiyar haɗin gwiwa wajen sauya ilimi…
Read More