Labarai

Kakakin Majalisar Jihar Zamfara na fuskantar barazanar tsigewa

Kakakin Majalisar Jihar Zamfara na fuskantar barazanar tsigewa

Daga BASHIR ISAH Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Bilyaminu Moriki, na fuskantar barazanar tsigewa daga mafiya rinjayen mambobin majalisar. Ya zuwa haɗa wannan rahoto, MANHAJA ta tattaro cewar galibin 'yan majalisar na gudanar da taro a harabar majalisar da yammacin ranar Alhamis kan yadda za su tsige kakakin majalisar. Kazalika, ziyarar da wakilinmu ya kai harabar majalisar ya gano yadda aka rufe harabar majalisar da kuma girke jami'an tsaro da suka haɗa da 'yan danda da sibul difens a cikinta. Bincike ya nuna hatta sandan majalisar bai tsira ba, don kuwa an samu wasu da suka yi awon gaba…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Sunday Igboho ya shigo Nijeriya

Da Ɗumi-ɗumi: Sunday Igboho ya shigo Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Mai fafutukar kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya dawo Nijeriya. Mai magana da yawun Igboho, Olayomi Koiki, shi ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis. Koiki ya ce Igboho ya dawo Nijeriya ne don halartar jana'izar mahaifiyarsa. Idan za a iya tunawa tun a 2021 Igboho ya bar Nijeriya inda aka ɗauke shi zuwa Jamhuriyar Benin bayan da hukumar DSS ta ayyana shi a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
Read More
Gwamnati na shirin farfaɗo da shirin bada tallafi na ‘Direct Cash Transfers’

Gwamnati na shirin farfaɗo da shirin bada tallafi na ‘Direct Cash Transfers’

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya za ta farfaɗo da shirin bada tallafin da aka fi sani da 'Direct Cash Transfers' wanda gwamnatin baya ta samar domin tallafa wa masu tsananin buƙata a faɗin ƙasa. Ministan Kuɗi, Wale Edun ne ya bayyana haka sa'ilin da yake jawabi a wajen wani taro da aka shirya ranar Laraba a Uyo, babban birnin Jihar Akwa-Ibom. A cewar Ministan, “Kwamitin shugaban ƙasa kan shirye-shiryen bada tallafi ya shirya ganin Shugaban Ƙasa inda zai gabatar masa da buƙatar sake farfaɗo da shirin bada tallafi ga masu tsananin buƙata. Ana yin dukkan mai yiwuwa domin rage wa…
Read More
Tsadar Rayuwa: Sanwo-Olu ya rage wa ma’aikata ranakun aiki a Legas

Tsadar Rayuwa: Sanwo-Olu ya rage wa ma’aikata ranakun aiki a Legas

Daga BASHIR ISAH Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas ya rage ranakun aiki wa ma'aikatan jihar zuwa uku maimakon biyar da aka saba. A sanarwar da ya bayar a ranar Alhamis, Sanwo-Olu ya ce daga yanzu ma'aikatan gwamnatin jihar da ke mataki na 1 zuwa 14 sau uku kacal za su riƙa tafiya aiki a mako. Ya ce ya gwamnatinsa ta ɗauki wannan mataki ne domin sauƙaƙe wa ma'aikatan jihar ƙuncin tattalin arzikin da ake fuskanta. Ya bayyana haka ne a jawabin kai-tsaye da ya yi wa 'yan jihar a ranar Alhamis domin sanyaya musu rai dangane da tsadar rayuwar…
Read More
NLC a Neja ta janye yajin aiki bayan cimma yarjejeniya da gwamnati

NLC a Neja ta janye yajin aiki bayan cimma yarjejeniya da gwamnati

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen Jihar Neja ta sanar da janye yajin aikin da ta fara a ranar Laraba a jihar. Ƙungiyar ta ce ta dakatar da yajin aikin ne biyo bayan yarjejeniyar da ta suka cimma da ɓangaren gwamnati da kuma don bada zarafin ci gaba da tattaunawa a tsakanin ɓangarorin biyu. Shugaban NLC a jihar, Abdulkareem Lafene, shi ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan tattaunawar da suka yi da ɓangaren gwamnati a ranar Laraba. Haka shi ma Gwamnan Jihar, Mohammed Umaru Bago, ya ce lallai sun cimma yarjejeniya kan gwamnatin jihar za ta…
Read More
Ban haramta samar da biredi a Zamfara ba – Dauda

Ban haramta samar da biredi a Zamfara ba – Dauda

*Ya ce an haramta kai wa 'yan ta'adda biredi a jihar Daga BASHIR ISAH Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya yi ƙarin haske inda ya ce bai haramta samar da biredi a sassan jihar ba. Sai dai, ya ce ya haramta duk wata hanya da ake amfani da ita wajen taimaka wa 'yan fashin daji da biredi a jihar. Dauda ya yi wannan ƙarin hasken ne biyo bayan dakatar da samar da biredi a jihar da Ƙungiyar Masu Gasa Biredi ta yi a sakamakon dakatar da harkar babura masu kai wa 'yan fashin daji biredi a jihar da gwamnati…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya kafa dokar haramta ɓoye kayan abinci a Katsina

Gwamna Raɗɗa ya kafa dokar haramta ɓoye kayan abinci a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya saka hannu kan dokar da za ta hana mutane ɓoye kayan abinci. Kafa wannan doka na nufin hana wasu 'yan kasuwa da ake zargi da ɓoye kayan abinci a rumbuna daban-daban don kayan abincin su yi tsada. Kazalika, Gwamnan ya kafa wani kwamiti na musamman da za a ɗora wa alhakin bi lungu da saƙo na jihar don zaƙulo mutanen da suke ɓoye kayan abinci. Dokar ta kuma haramta duk wani yunƙuri na ɓoye kayan abinci a duk faɗin jihar. Haka nan, dokar ta lissafta kayan abinci…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Sanatoci sun taka wa shirin cire tallafin lantarki burki

Da Ɗumi-ɗumi: Sanatoci sun taka wa shirin cire tallafin lantarki burki

Daga BASHIR ISAH Majalisar Dattawa ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya kan kadabta cire tallafin labtarki duba da ƙuncin rayuwar da ake fama da shi a ƙasa Majalisar ta ɗauki wannan mataki ne biyo bayan ƙudirin da aka gabatar mata yayin zamanta a ranar Laraba kan buƙatar ci gaba da bai wa 'yan ƙasa tallafin lantarkin. Sanata mai wakiltar shiyyar Adamawa ta tsakiya Aminu Iya Abbas (PDP), shi ne ya gabatar da ƙudirin. A makon da ya gabata Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta iya ci gaba da bada tallafin wutar lantarki ba. Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu ne ya…
Read More
Ma’aikata sun tsunduma yajin aiki a Neja

Ma’aikata sun tsunduma yajin aiki a Neja

Ma'aikata sun tsunduma yajin aiki a Neja Daga BASHIR ISAH Ma'aikatan gwamnati a Jihar Neja, sun fara yajin aikin sai-baba-ta-gani domin biyar haƙƙinsu a wajen gwamnati. Da safiyar Laraba ma'aikatan suka fara yajin aikin bisa umarnin Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) reahen jihar, lamarin da ya haifar da tsaiko a harkokin jihar. NLC reshen jihar ta ɗauki wannan mataki ne bayan da gwamnatin jihar ta kasa cimma buƙatun mambobinta a jihar. Shugaban NLC na jihar, Idrees Lafene da takwaransa na ƙungiyar 'yan kasuwa, Ibrahim Gana, su ne suka bai wa ma'aikatan jihar unarnin shiga yakin aikin bisa abin da suka kira gazawa…
Read More