11
Aug
Rikicin shugabanci acikin ƙungiyar ISWAP na ƙara tsananta biyo bayan wani sabon rahoton sirri da ke nuna cewa an kashe mambobi huɗu na Majalisar Shura ta ƙungiyar. A cewar wani rahoton sirri daga Zagazola Makama, mambobin guda huɗu, waɗanda aka garkame su a makon da ya gabata ta hannun dakarun ISWAP, an ce wani babban jami’in ISWAP mai suna Ba Shuwa ne ya kashe su a maɓoyarsu ta Kwatan Dila a ranar Laraba, 6 ga Agusta. Wannan sabon al'amari ana kyautata zaton zai ƙara bayyana ƙaruwar rashin jituwa a tsakanin 'ya'yan ƙungiyar da kuma samun rarrabuwar kawuna a cikinta wanda…
