Labarai

Alhaji Abu Ɗanmalam Karofi ya rasu a Katsina

Alhaji Abu Ɗanmalam Karofi ya rasu a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Tsohon babban sakatare kuma raya karkaran Katsina, Alhaji Abu Ɗanmalam Karofi ya rasu bayan yayi fama da doguwar rashin lafiya a Katsina. Ɗanmalam Karofi wanda aka fi sani da ADK shi ke kula da ƙananan hukumomin jihar a lokacin Marigayi Umaru Musa Yar'adua na gwamnan jihar. Marigayi ADK za a riƙa tunawa da shi wajen jajircewa na ganin shugabannin ƙananan hukumomi dole su gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da mulkin ƙananan hukumomin jihar. Haka kuma an bayyana Karofi a matsayin mai gaskiya da jajircewa wajen ganin shugabannin ƙananan hukumomi sun sarrafa kason kuɗaɗen su…
Read More

2027: INEC ta ƙara wa’adin ɗora sunayen ‘yan takarar gwamna da majalisun dokokin jihohi a shafinta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta ƙara wa'adi ga jam'iyyun siyasa na su ɗora sunayen 'yan takararsu na kujerun gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi daga ranar 8 zuwa 11 ga watan Agusta, 2026 yayin cigaba da shirye-shiryen zaɓen 2027. INEC ta sanar da haka ne a wata takarda da ta fitar a ranar Lahadi ta hannun Shugabanta na Kwamitin 'Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe, Mohammed Haruna. A cewarta, matakin ya biyo bayan magiya da ta samu daga ɓangaren jam'iyyun na a ƙara wa'adin domin su samu damar kammala ayyukan ɗora…
Read More

Isra’ila ta ƙi amince wa matakan Trump 15 na janye sojojinta a Gaza

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi watsi da shirin saɗurra 15 ga Gaza da Shugaba Donald Trump na Amurka ya goya wa baya a matsayin sharuɗɗan zaman lafiya, yana mai cewa sojojin Isra'ila ba za su janye daga yankin Falasɗinun ba har zai Hamas ta tabbatar da ajiye makamanta. Netanyahu ya sanar da wannan matsaya ne a ranar Lahadi, yayin zama da manyan jami'an gwamnatinsa a wani yanayi da ka iya haifar da tsaiko ga yunƙurin zaman lafiya da ake shirin samarwa a yankin na Gabas ta Tsakiya. Netanyahu ya ce wajibi ne Hamas…
Read More
Gwamnan Zamfara na cikin tawagar da za ta wakilci Nijeriya a taron zuba jari na Kanada-Afirka

Gwamnan Zamfara na cikin tawagar da za ta wakilci Nijeriya a taron zuba jari na Kanada-Afirka

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, tare da wasu gwamnoni da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa za su wakilci Nijeriya a taron ƙoli na Kanada-Afirka kan hanyoyin zamani na tattalin arziki da za a gudanar a Toronto kamar yadda sanarwar ta fito daga mai magana da yawun gwaman Sulaiman Bala Idris. Taron zuba jari na farko na irin sa zai gudana ne daga ranar 10 zuwa 15 ga Agusta, 2026, a birnin Toronto na ƙasar Kanada. A cikin wasiƙar gayyatar da fadar shugaban ƙasa ta aika wa gwamna Lawal, an bayyana cewa kasancewarsa cikin manyan mahalarta taron zai taimaka wajen ƙarfafa…
Read More
Mustapha Inuwa ya fice daga jam’iyar ADC zuwa APC a Katsina

Mustapha Inuwa ya fice daga jam’iyar ADC zuwa APC a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Madugun adawa a Katsina Dr. Mustapha Muhammad Inuwa da dubban magoya bayansa sun fice daga ADC sun koma APC. Mustapha Inuwa wanda tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina dama can ɗan jam'iyar APC amma tun da jam'iyar ta gudanar da zaɓen fidda ɗan takara gwamna, da Dikko Raɗɗa ya kada shi ya bar jam'iyar. Bayan wani lokaci sai madugun adawar ya koma jam'iyar PDP nan ma ya fice bayan ya sami saɓani da Sanata Yakubu Lado Danmarke. Daga nan ya koma ADC inda ya zama jagorar jam'iyar a Jihar kafin shigar shi APC. Sauyin ya jawo…
Read More

Cika shekaru 58: Juriya da dagewar Yilwatda sun ƙarfafa matsayin APC, inji Iliyasu Kwankwaso

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Juriya, haƙuri da jagoranci na haɗa kowa da kowa na Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ne ginshiƙin da jam’iyyar ta dogara da su wajen ƙarfafa matsayinta na jam’iyya mafi yawan jama’a a Nijeriya. Darakta na Kuɗi na Hadejia Jama’are River Basin, Dr. Musa Illiyasu Kwankwaso ne ya bayyana haka yayin da yake taya Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Goshen Yilwatda, murna a ranar cika shekaru 58 da haihuwa. Dr. Musa Illiyasu Kwankwaso ya yaba da jajircewar Farfesa Yilwatda wajen ciyar da Shirin Sabon Bege na Shugaba Bola Ahmed Tinubu…
Read More
An yi kira ga ‘yan siyasa a Katsina su guji cin mutuncin juna a yaƙin neman zaɓe

An yi kira ga ‘yan siyasa a Katsina su guji cin mutuncin juna a yaƙin neman zaɓe

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An yi kira ga 'yan siyasa a Jihar Katsina da su guji cin mutuncin junan su gabanin fara yaƙin neman zaɓe na 2027. Shugaban ƙungiyar cigaban Funtua,Kwamred Mannir Suleiman ya yi wannan kira a Katsina a wata hira da manema labarai. Kwamred Suleiman ya nuna damuwarsa a yadda kwanaki kaɗan masu zuwa za a fara fita yaƙin neman zabe amma har an fara fitowa kafafen sadarwa ana musayar yawu wanda haka ka iya kawo rigingimu a tsakin su. Yakamata 'yan siyasa su san cewa duk wannan yunƙuri da suke yi kan neman kujerar mulki, domin…
Read More

Neja: Ambaliya ta lanƙwame gidaje da wasu kadarori a rukunin gidajen Minna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kadarorin miliyoyin naira sun lalace sakamakon aukuwar wata ambaliya a yankin sanannen rukunin gidajen nan na Janar M.I. Wushishi (Mohammed Inuwa Wushishi) da ke garin Minna a Jihar Neja. Haka kuma, ambaliyar ta haɗe wasu gidaje da ke rukunin gidajen, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin ɗebe kayayyakinsu daga cikin gidajen nasu. Don haka waɗanda al'amarin ya shafa suka yi magiya ga gwamnati da ta kai musu ɗauki tare da warware matsalolin da ke haddasa ambaliya a yankin nasu. Ɗaya daga waɗanda abin ya shafa mai suna Waziri Ahmed ya shaida wa manema…
Read More

Mutane 16 sun jikkata yayin da aka ceto 13 bayan ruftawar gini a Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Aƙalla mutane 13 ne aka ceto bayan wani gida ya rushe a yankin Ɗan Dishe da ke Kwanar Yashi a Ƙaramar Hukumar Fagge ta jihar Kano, a safiyar ranar Asabar. Haka kuma, wasu mutane 16 sun samu raunuka sakamakon faruwar al'amarin. Hukumar Kashe Gobara ta jihar ta ce sashenta na bayar da agajin gaggawa ya samu kiran gaggawa kan iftila'in da misalin ƙarfe 4:32, wanda ya sa cikin hanzari ta tura jami'ai daga hedikwatarta zuwa wajen domin kai ɗauki. Jami'inta na hulɗa da jama'a, Saminu Abdullahi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da…
Read More
Ya jefa ’ya’yansa biyu daga bene mai hawa uku a Aba

Ya jefa ’ya’yansa biyu daga bene mai hawa uku a Aba

Wasu yara biyu sun jikkata bayan da mahaifinsu ya jefa su daga saman wani bene mai hawa uku a unguwar Umuobe da ke kusa da Babban Garin Aba, a Jihar Abia. Rahotanni sun ce mutumin, mai kimanin shekara 40 a duniya, ya aikata hakan ne saboda wani dalili da har yanzu ba a bayyana ba. Bayan jefa yaran, shi ma ya yi tsalle daga saman wannan bene, bayan da ake zargin ya yi barazanar cutar da matarsa. Ko da yake yaran sun tsallake rijiya da baya, sun samu raunuka daban-daban sakamakon faɗuwar. Mazauna yankin, da suka fito bayan jin kukan…
Read More