Labarai

Ƙudirina shi ne inganta Hukumar Kula da Ilimin Kimiyya da Fasaha a Kano – Farfesa Ɗahiru Saleh

Ƙudirina shi ne inganta Hukumar Kula da Ilimin Kimiyya da Fasaha a Kano – Farfesa Ɗahiru Saleh

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, Farfesa Ɗahiru Saleh Muhammad, ya bayyana cewa babban burinsa shi ne inganta ayyukan hukumar kimiyya da fasaha ta Jihar Kano a mastayinsa na masani akan harkar ilimin kimiyya da fasaha. Don haka ya ce ƙudirinsa shi ne ɗaukaka darajar hukumar da kuma yin aiki bisa ƙa'idar koyar da ilimin kimiyya da fasaha domin kwalliya ta biya kuɗin sabulu wato kowacce ƙwarya a ajiyeta a gurbinta, kamar yadda ƙudirin gwamnan Kano ya ke Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ke na bunƙasa ilimin kimiyya da fasaha…
Read More
Yadda ‘yan bindiga suka banka wa gidaje, asibiti da ofishin ‘yan sanda wuta a Katsina

Yadda ‘yan bindiga suka banka wa gidaje, asibiti da ofishin ‘yan sanda wuta a Katsina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ranar Litinin ce bayan sallar magriba, gungun ‘yan bindiga akan babura suka afka cikin garin Wurma, a Ƙaramar Hukumar Kurfi. Maharan sun banka wa ofishin ‘yan sanda da wani sabon asibitin kula da marasa lafiya wuta. Haka kuma sun banka wa gidajen mazauna garin wuta da dama. ‘Yan bindigar sun kuma ƙone motoci duk a cikin daren. Mazauna garin sun tabbatar wa wakilin mu cewa sun arce da mutum 12. Wata majiya ta shaida wa wakilin mu cewa maharan sun afka wa garin Wurma da ke yamma da Birchi su na kan babura, ƙoƙarin…
Read More
Teku ta ci matashi a Legas

Teku ta ci matashi a Legas

Daga BASHIR ISAH Rahotannai daga Jihar Legas sun ce, teku ya yi gaba da wani matashi ɗan shekara 13, mai suna Kelvin Onyengba, a lokacin da suka je shaƙatawa tare da abokansa a bakin teku a yankin Ajah da ke Legas. Majiyarmu ta ce lamarin ya auku ne ranar Talata da rana. Bayanai sun ce igiyar ruwa ce ta ja matashin zuwa cikin teku a daidai lokacin da suke wanka tare da wasu abokansa su biyar. Majiya ta ce, "Mahaifiyar yaron ta ce igiyar ruwa ce ta ja ɗanta. Sun tafi shaƙatawa ne a bakin teku tare da wasu abokansa…
Read More
Mazauna Chikun sun yi zanga-zanga kan harin ta’addanci a yankinsu

Mazauna Chikun sun yi zanga-zanga kan harin ta’addanci a yankinsu

Daga BASHIR ISAH Mazauna yankin Chikun cikin Ƙaramar Hukumar Goningora da ke Jihar Kaduna sun tare babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a yankinsu sakamakon zanga-zangar da suka gudanar a ranar Alhamis. Jaridar Intelrigeon ta rawaito cewar, mazauna yankin sun shirya zanga-zangar ne domin nuna rashin jin daɗinsu da harin ta'addancin da 'yan bindiga suka kai yankin. Zanga-zangar ta yi sanadiyar hana abubuwan hawa zirga-zirga a hanyar kamar yadda aka saba. A cewar tashar Channels TV, mazauna yankin da dama ne aka yi awon gaba da su yayin da wasu sun jikkata sakamakon harin 'yan bindiga a yankin a ranar Laraba.…
Read More
Lawal ya ƙaddamar da raba kayayyakin karatu ga makarantu 250 a Zamfara

Lawal ya ƙaddamar da raba kayayyakin karatu ga makarantu 250 a Zamfara

Daga BASHIR ISAH Gwanna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jaddada cewa fannin ilimi shi ne kan gaba a jerin ɓabgarorin da zai bai wa fifiko wajen gina jihar Zamfara. Lawal ya bayyana haka ne a wajen bikin ƙaddamar da raba kayayyakin koyo da koyarwa ga makarantu wanda ya gudana ranar Laraba a Gusau, babban birnin jihar. Rabon kayayyakin ya shafi makarantun gwamnati 250 ne da suka haɗa firamare da ƙananan sakandare a jihar. Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris ya ce, Hukumar Ilimin Bai-ɗaya (UBEC) da ke Abuja da kuma UNICEF su ne suka samar da kayayyakin.…
Read More
Za a yi taron wayar da kan ‘yan Kannywood kan sabbin dokokin Hukumar NCC – KSCB

Za a yi taron wayar da kan ‘yan Kannywood kan sabbin dokokin Hukumar NCC – KSCB

Hukumar kare haƙƙin masu mallaka tare da yaki da satar fasaha ta kasa (NCC), ta nemi haɗa hannu da Hukumar tace Fina-finai da Ɗab'i ta Jihar Kano domin wayar da kan abokan hulɗarsu kan sabbin dokokin hukumar da waɗanda aka yi wa gyara. Da yake jawabi a yayin ganawar sa da manema labarai, Alh Sani Ahmad wanda shi ne mai kula da jihohin Kano, Katsina da Jigawa na Hukumar kula da haƙƙin masu mallaka tare da satar fasaha ta kasa ya ce, ya ziyarci Hukumar ta tace Fina-finan ne a domin neman goyan bayan su ta yadda za su haɗa…
Read More
NLC ta janye ci gaba da zanga-zangar gama-gari

NLC ta janye ci gaba da zanga-zangar gama-gari

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta dakatar da ci gaba da zanga-zangar gama-gari na yini biyun da ta shirya. Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a cikin sanarwar bayan taron da ta fitar bayan taron Majalisar Zartarwar ƙungiyar, tana mai cewa zanga-zangar ranar farko ta haifar da cigaba mai ma'ana. Don haka ta je ta janye ci gaba da zanga-zangar a rana ta biyu biyo bayan nasarar davta samu a ranar farko ta zanga-zangar. Da fari NLC ta ƙeƙashe ƙasa inda ta ce babu gudu babu ja da baya game da zanga-zangar yini biyun da ta shirya…
Read More
Lawal zai gina garejin manyan motoci a sassan Zamfara

Lawal zai gina garejin manyan motoci a sassan Zamfara

Daga BASHIR ISAH Gwamna Jihar Zamfara Dauda Lawal, ya bayyana cewa zai gina wuraren hada-hadar motocin kasuwa a Zamfara a matsayin ɓangaren ƙudirinsa na raya birane a jihar. Lawal ya furta hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙungiyar masu motocin haya ta NARTO da ta direbobin tankokin dakon fetur, PTD. Cikin sanarwar da Kakakinsa Sulaiman Bala Idris ya fitar, Gwamna Lawal ya ce, “Na ba da umarnin a gina garejin manyan motoci guda biyu, ɗaya a hanyar Funtua zuwa Gusau gudan kuma a hanyar Sokoto zuwa Gusau. "Ni na gayyato NARTO da PTD kan su zo su…
Read More
‘Za mu ci gaba da zanga-zanga’ — cewar NLC

‘Za mu ci gaba da zanga-zanga’ — cewar NLC

*Ganawarsu da gwamnati ba ta haifar da ɗa mai ido ba Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta ce za ta ci gaba da zanga-zangarta tun da ba a cimma maslaha ba a taron da suka yi da Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin. Ɓangarorin biyu sun gana ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja da zummar lalubo bakin zare dangane da zanga-zangar da NLC ke kan gudanarwar domin nuna rashin jin daɗinta da halin tsadar rayuwar da 'yan ƙasa ke fuskanta. Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero, ya ce "Za a ci gaba da zanga-zangar, kuma haƙƙi…
Read More
Tsadar Rayuwa: NLC na zanga-zanga a sassan ƙasa

Tsadar Rayuwa: NLC na zanga-zanga a sassan ƙasa

Daga BASHIR A halin da ake ciki, haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta shirya zanaga-zangar lumana a sassan ƙasa domin nuna rashin jin daɗinta game da ƙuncin rayuwar da 'yan ƙasa ke fuskanta. Bayanan da MANHAJA ta kalato a ranar Talata sun nuna an hangi masu zanga-zangar a yankin Ikeja, Jihar Legas. Inda aka ga da damansu ɗauke da kwalaye masu ɗauke da saƙonni daban-daban kamar "A kawo ƙarshen yunwa da talauci yanzu" da dai sauransu. A Jos babban birnin Filato ma haka lamarin yake, a nan ma an ga ɗaruruwan masu zanga-zangar sun mamaye wasu manyan hanyoyin birnin.…
Read More