02
Sep
•Ba za mu amince da halayyar sojoji ba, inji Shugaban Nijeriya*Shugabannin Kamaru da Rwanda sun sauke manyan hafsoshinsu*Ka daure ka koma Nijar – Tinubu ya roqi Sarkin Musulmi*Hamɓararren Shugaban Gabon ya nemi agaji Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Daga dukkan alamu hamvarar da gwamnatin Ƙasar Gabon ya ɗaga hankalin wasu shugabannin Afrika bisa la’akari da yadda suke ɗaukar matakai daban-daban wajen ganin sun daƙile afkuwar hakan a ƙasashensu, inda ake ganin lamarin a matsayin kaɗuwar hanta. A shekaranjiya Laraba, 30 ga Agusta, 2023, ne sojoji suka hamɓarar da gwamnatin Ƙasar Gabon, makonni bayan kiki-kakar da ake yi da sojojin…
