01
Oct
Yau Lahadi ake sa ran Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi wa 'yan ƙasa jawabi bayan dawowa daga taron da ya halarta a Amurka. Taron shi ne karo na 78 da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya wanda ya gudana a birnin New York. Bayan kammala taron ne Shugaba Tinubu ya ziyarci Paris da Faransa don taƙaitaccen hutu, in ji wata majiya. Tinubu ya iso gida ne sa'o'i kafin Ranar Samun 'Yancin Kan Nijeriya karo na 63, sannan kawana huɗu gabanin tsunduma yajin aikin da Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya da takwarorinta suka shirya. Da misalin ƙarfe 7:00am na wannan safiya…
