Babban Labari

Faransa za ta maido wa Nijeriya $150m wadda Abacha ya wawushe

Faransa za ta maido wa Nijeriya $150m wadda Abacha ya wawushe

Daga BASHIR ISAH Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana a ranar Juma'ar da ta gabata cewa, ƙasar Faransa za ta maido wa Nijeriya kuɗi har Dala miliyan 150 wanda tsohon Shgugaban Ƙasa marigayi Janar Sani Abacha ya wawushe a halin rayuwarsa. Cikin sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa Faransa da matakin maido da kuɗin da ta ɗauka. Da yake karɓar baƙuncin Ministar Harkokin Wajen Faransa, Catherine Colonna, Shugaba Tinubu ya yaba da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da Faransa, yana mai cewa, fahimtar juna da ke…
Read More
Ƙaramin kasafin kuɗi: Sojojin ruwa sun shafa wa Tinubu kashin kaji

Ƙaramin kasafin kuɗi: Sojojin ruwa sun shafa wa Tinubu kashin kaji

*Ban buƙaci yin ta-more ba, inji Shugaban Ƙasa*Majalisa ta fizgo wa ɗalibai biliyan N5 daga Fadar Shugaban Ƙasa Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Daga dukkan alamu wani ɓangare na ƙaramin kasafin kuɗin da Rundunar Sojojin Ruwan Nijeriya ta nemi a ba ta cikin ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi na 2023, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa Majalisar Dokoki, domin neman amincewarta, ya nemi ya shafa shugaban kashin kaji a wajen akasarin masu sharhi da lura da al’amuran yau da kullum a faɗin ƙasar, saboda yadda cece-kuce ya ɓarke akan batun har ma Fadar Shugaban Ƙasa ta magantu kan lamarin. Wannan…
Read More
Duniya mai yayi: Mawakan Kannywood sun yi wa Rarara taron dangi akan Buhari

Duniya mai yayi: Mawakan Kannywood sun yi wa Rarara taron dangi akan Buhari

Daga WAKILINMU Wasu fitattun mawaqan masana’antar Kannywood a ƙarƙashin ƙungiyar mawaƙa ta Murya Ɗaya sun caccakin fitaccen mawaƙin siyasar nan, Dauda Abdullahi Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, bisa sukar da ya yi wa tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari. Babban abin mamakin shine, yawancin mawaƙan da suka taso su na caccakar Rarara ɗin ba su tare da tsohon shugaban ƙasar a lokacin da ya ke gadon mulki, yayin shi kuma Rarara ɗin yana tare da Buhari har zuwa lokacin da ya sauka daga kan karagar mulki. Rarara ya janyo waccan magana ne a makon jiya, inda ya kira taron…
Read More
Shari’ar zaɓen 2023: Yadda Tinubu ya yi zarra a Kotun Ƙoli

Shari’ar zaɓen 2023: Yadda Tinubu ya yi zarra a Kotun Ƙoli

•Kotun ta yi fatali da shaidar takardun Chicago•Ta raraki Peter Obi•Tinubu ye nemi haɗin kai don gina Nijeriya•Atiku da Obi su jira zuwa 2031, cewar Ganduje•PDP da LP sun maida martani•Buhari ya yi maraba da hukuncin Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotun Ƙolin Nijeriya ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasar na 2023. Hukuncin na alƙalai bakwai ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Inyang Okoro ya ce, “a ƙarshe, bayan warware duk wasu lamurra game da ɗaukaka ƙarar, zan iya cewa babu hujjoji masu ƙwari game da ɗaukaka ƙarar, saboda haka an yi watsi…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar Atiku ta neman gabatar da sabuwar hujja a kan Tinubu

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar Atiku ta neman gabatar da sabuwar hujja a kan Tinubu

Daga BASHIR ISAH Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gabatar wa kotun ta neman kotu ta ba shi damar gabatar mata da sabuwar hujja a kan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu. Atiku ya buƙaci kotun da ta ba shi damar gabatar da bayanan da ya ce ya samo game da karatun da Tinubu ya ce ya yi a Jami'ar Jihar Chicago ta ƙasar Amurka. Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar na ra'ayin cewa bayanan bogi ne Tinubu ya miƙa wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a…
Read More
Zamfara: Dauda ya ƙara yi wa Matawalle fallasa

Zamfara: Dauda ya ƙara yi wa Matawalle fallasa

*Gwamna ya zargi ministan da wawure biliyoyin kuɗi na aikin filin jirgi*Za a gurfanar da masu hannu ciki a gaban kuliya Daga MAHDI M. MUHAMMAD Daga dukkan alamu zazzafar adawar siyasar dake tsakanin Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da wanda ya gaje shi kuma Ƙaramin Ministan Tsaro, Muhammad Bello Matawalle, na ƙara yin tsamari a tsakaninsu, inda a baya-bayan nan gwamnan ya zargi ministan da wawure biliyoyin Dala na aikin gina filin jiragen sama na jihar ta Zamfara. Lawal ya ce, gwamnatin da ta shuɗe ta Bello Matawalle ta wawure biliyoyin Naira a filin jirgin sama na Zamfara, wanda daga…
Read More
Ana zargin almundahana a rabon kayan tallafin Kebbi 

Ana zargin almundahana a rabon kayan tallafin Kebbi 

*An dakatar da rabon tallafin Argungu Daga JAMIL GULMA a Kebbi  A ranar Juma'ar da ta gabata ne Gwamnan Jihar Kebbi, Malam Nasir Idris wanda shine Ƙauran Gwandu, ya ƙaddamar da rabon kayan tallafi a Ƙaramar Hukumar Maiyama, don rage raɗaɗin matsin tattalin arziki ga al'ummar jihar, inda kuma daga nan ya umarci kowacce ƙaramar hukumar mulki ta je ta raba a yankinta. Sai dai ba a nan gizo ke saƙa ba, saboda rabon kayan ya samu tarnaƙi yayin da a ke zargin tafka almundahana a waɗansu ƙananan hukumomi. Wata mata da ba ta so a bayyana sunanta ba ta…
Read More
Chicago: Zan dangana idan Kotun Ƙoli ta tsarkake Tinubu – Atiku

Chicago: Zan dangana idan Kotun Ƙoli ta tsarkake Tinubu – Atiku

*Ɗan takarar PDP ya ce ba don kansa yake wa Tinubu tone-tone ba*Siyasarka ta zo ƙarshe – APC ga Atiku*Ba na tsoro domin Buhari ya gama kassara kasuwancina a Nijeriya, inji Atiku Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Ɗan takarar babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi iƙirarin cewa, idan har Kotun Ƙolin Nijeriya ta yanke hukuncin cewa, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu tsarkakke ne shi, duk da satifiket ɗin da shi Atikun ya amso daga Jami’ar Chicago dake Birnin Ilinious, don ƙalubalantar sahihancin zaɓensa a 2023, to zai dangana ya haƙura…
Read More
Ranar Samun ‘Yancin Kan Ƙasa: Tinubu ya yi wa ma’aikata ƙarin albashi na wucin-gadi

Ranar Samun ‘Yancin Kan Ƙasa: Tinubu ya yi wa ma’aikata ƙarin albashi na wucin-gadi

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana ƙarin albashi ga ma'aikatan gwamnati don rage musu raɗaɗin cire tallafin mai. Ya sanar da hakan ne a jawabinsa da ya yi wa 'yan ƙasa da safiyar Lahadi albarkacin Ranar Samun 'Yancin Kan Ƙasa, 1 ga Oktoba, 2023. Game da ƙarin, Tinubu ya ce ƙaramin ma'aikaci zai samu ƙarin N25,000 a albashinsa har na tsawon wata shida. Wannan na nufin ma'aikacin gwamnatin tarayya da ke karɓar albashi N30,000, yanzu N55,000 zai riƙa karɓa har na tsawon wata shida. Da alama dai ƙarin albashin na wucin gadi ne, kuma Shugaban bai yi ƙarin haske…
Read More
Ruɗani ya mamaye hukuncin kotun zaɓen Gwamnan Kaduna

Ruɗani ya mamaye hukuncin kotun zaɓen Gwamnan Kaduna

*Shugaban Kotun ya kori ƙarar*Alqalai biyu sun nemi yin tutsu?*Gwamna Sani ya yaba wa Ashiru Kudan*PDP ta kasa gamsuwa Daga MAHDI M. MUHAMMAD Daga dukkan alamu hukuncin da kotun sauraron ƙarar zaɓen kujerar Gwamnan Jihar Kaduna ta yanke ya jefa mutane da dama cikin ruɗani, inda da fari aka bayar da rahotannin da ke nuni da cewa, kotun ta ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba (wato inconclusive), to amma jim kaɗan bayan hakan sai kuma sababbin rahotanni suka nuna cewa, hukuncin yana magana ne akan tabbatar da Gwamna Uba Sani na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe…
Read More