30
Jul
*An kasa samun matsaya kan ministocin Kano, Zamfara da Kebbi Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ƙarshe dai Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunayen mutane 28 da ya zaɓa a matsayin ministoci, domin naɗa su a matsayin mabobin Majalizar Zartarwar Tarayyar Nijeriya. Bayan an daɗe ana jiran jerin sunayen ne a jiya Alhamis Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya zo zauren majalisar da ƙarfe 12:05 na rana, inda bayan an yi addu’ar buɗe zaman zauren sai kuma ya bayyana cewa, majalisar za ta shiga wani zama na musamman. Bayan zaman ne ya fito ya bayyana jerin sunayen…
